Babbar girgizar kasar da ta faru a ranar 12 ga watan Mayu na shekarar 2008, ta auku ne a wurin da aka fi samun mutanen kabilar Qiang, daya daga cikin kananan kabilun kasar Sin, inda girgizar kasa ta yi sanadiyyar wutuwar wasu masu cin gadon al'adun gargajiya na kabilar Qiang, da rushewar gidaje da yawa, sa'an nan halin ya sa aikin kiyaye al'adun gargajiya na kabilar Qiang ya shiga cikin mawuyacin hali. Yanzu shekara daya ta wuce tun da aka samu bala'in girgizar kasa, shin yaya aikin farfado da al'adun kabilar Qiang yake? To, cikin shirin yau zan ba ku amsa.
Macen da ke rera waka sunanta Wang Zhengfang, tana zama a kauyen Yu Zixi da ke lardin Sichuan. Ita wata 'yar kabilar Qiang ce, wadda ke da shekaru 44 a duniya. Fasahohinta ba su tsaya kan rera waka ba, har ma ta iya sassaka, da kera abubuwan da ake sanya a jiki, kamarsu kallabi da marufi, da dai makamantansu. Amma duk wadannan fasahohin gargajiya na kabilar qiang da Madam Wang take da su, ba ta koya daga wani malami ba, sai dai ta yi kokarin samu bisa karfin kanta. Shi ya sa bisa abin koyi da ta bayar, za a iya gani makoma mai kyau kan bunkasa al'adun gargajiya na kabilar Qiang.
"Ban taba shiga cikin makaranta domin koyon fasaha ba, sai dai a ko wace ranar Lahadi na kan koma gida in duba yadda manya suke kula da ayyukan. Da na yi musu tambaya, sa'an nan sun gaya mana abin da ake fara da shi, da sauki ne za a fara sanin fasahar."
Kabilar Qiang ita ce daya daga cikin kabilun kasar Sin wadanda suka fi dogon tarihi, ta riga ta kasance a kasar Sin har shekaru fiye da 3000. A da can, an fi samun mutanen kabilar Qiang a wurin da ke dab da iyakar kasar Sin ta arewa maso yamma, daga baya sannu a hankali, sun kaura zuwa lardin Sichuan da ke kudancin kasar Sin. Suna son zama a cikin dakunan da aka shimfida a tsakiyar duwatsu, abun ya sa ake kiransu 'kabilar da ke kan gajimare'. Fasahar musamman da suke amfani da ita wajen gina gidaje, ta sa kabilar ta yi suna a tarihin aikin gini a duniya.
Bayan babban girgizar kasa da aka samu a wurin da 'yan kabilar Qiang suke zama, hukumomin kiyaye da binciken kayayyakin gargajiya na kasar Sin sun fara aiki ba tare da bata lokaci ba, inda suka tura kungiyoyin aiki zuwa wuraren da bala'in ya ritsa da su, don binciken hasarar da aka samu kan rayukan mutane da kayayyakin gargajiya, ta yadda za a iya ba da shawara kan aikin kiyaye da farfado da al'adu. Sa'an nan wasu hukumomin gwamnatin kasar Sin sun hada karfi don kafa yankin gwaji na kare al'adun kabilar Qiang, inda suka sanya wasu wuraren da mutanen kabilar Qiang suke zama cikin yankin da ake sa lura, don kiyaye kayayyakin gargajiya, da mutanen da suke gadon al'adun musamman na kabilar. Haka kuma don aiwatar da aikin, gwamnatin kasar Sin za ta samar da tallafi daga asusunta.
Zhou Heping, mataimakin ministan al'adu na kasar Sin, ya ce, sabo da mutanen kabilar Qiang ba su da bakaken harshensu, suna yada al'adunsu daga zuriya zuwa zuriya ta baka, shi ya sa ya wajaba da a kara taimakawa wasu mutane, da gina wuraren yada al'adu, da kuma yin amfani da fasahar zamani don yada al'adu da kara tasirinsa.
"Ana yada al'adun kabilar Qiang ne bisa karfin mutum, shi ya sa kiyaye mutane zai zama abin da za mu fi dora muhimmanci cikin aikinmu na kiyaye al'adu. Za mu aiwatar da aikin don tabbatar da cewa wadannan mutane za su samu damar yada da kuma koyon al'adunsu, haka kuma za mu kare kayayyakin al'adu masu muhimmanci, da kara yin amfani da fasahar zamani don ajiye al'adun musamman na kabilar Qiang."
Beichuan ta kasance gunduma mai cin gashin kai daya tak ta mutanen kabilar Qiang, inda aka samu makarantun da ake koyar da ilimin kabilar Qiang da wakokin kabilar. An fara yin haka ne tun bayan girgizar kasa, don yada al'adun kabilar qiang. Xu, malama ta wata makarantar wurin, ta ce, (4)
"A halin yanzu mutanenmu na kokarin wallafa littattafai don yin bayani kan al'adun kabilar Qiang, da aka gama aikin, za mu yada ilimin zuwa ga dukkan dalibanmu."
A wannan zangon karatu, Li Chunhong, wata daliba ta aji na 2 na makarantar sakandare?ita ma ta saurari darasin da aka yi na yada al'adu, wanda ya sa ta samu ilimi sosai. A ganin ta, darasin na da amfani.
"Darasin nan zai sa mutanen waje su kara fahimtar al'adun kabilarmu, har ma zai sa a kara sanin abubuwa masu ban sha'awa."
A halin yanzu, yawan al'ummar kabilar Qiang ya kai fiye da dubu 300, kuma kashi 80% daga cikinsu na zama a wasu gundumomin da ke lardin Sichuan, inda aka fi samun mumunan tasiri na babbar girgizar kasa. Yawancin garuruwa da kauyuka na mutanen kabilar Qiang sun rushe a cikin girgizar kasar. Sa'an nan ana mai da hankali sosai kan nuna halin musamman na al'adun kabilar Qiang yayin da ake sake gina garuruwan. Xiao Youcai, wani jami'in wurin, ya ce, ana aiwatar da aikin sake ginawa lami lafiya.
"Bala'in girgizar kasa ya ritsa da wasu wuraren da mutanen kabilar Qiang suke zaune, shi ya sa yayin da ake sake gina wadannan wurare, ba mu manta da tara kayayyakin al'adu da gina gidaje masu halayen musamman na kabilar Qiang ba.Yanzu mun tabbatar da cewa za a gina wani gidan nuna kayan tarihi na kabilar Qiang, a hakika an riga an fara aikin ginawa."
Don kiyaye halin musamman na gidajen mutanen kabilar Qiang, hukuma mai kula da aikin ginawa ta lardin Sichuan ta sa kwararru su shirya gadaje masu kyaun fasali wadanda suka dace da bukatun jama'ar wurin. Bisa kokarin da suka yi ne, an shimfida wani sabon kauye mai sunan "Jina". Sabon kauyen nan an shimfida shi ne a wani wurin da aka sha wahalar bala'in girgizar kasa sosai, inda dukkan gidaje sun rushe, sa'an nan gonaki sun lalace sosai. Amma yanzu mutanen wurin sun samu jin dadi sabo da sabon kauyen da aka gina wanda cike yake da halin musamman na kabilar Qiang. Sa'an nan wani jami'in wurin mai kula da aikin gina kauyen yana da shirin ci gaba, domin a ganinsa, saukar da jama'a cikin sabbin gidaje matakin farko ne kawai, bayan hakan kuma ana bukatar samun guraben aiki. Sai dai jama'ar kabilar Qiang su yi zaman rayuwarsu lami lafiya, za a iya samun damar yada al'adun kabilar da kyau.
"Kafin girgizar kasa mutanen wurin sun dogara kan aikin gona da kiwon dabbobi, sai dai yanzu bayan da muka kafa wani sabon kauye, muna la'akari da raya aikin yawon shakatawa. Shirinmu na yanzu shi ne, an ba iyalai 71 na wurin aiki, wasu za su kula da aikin saukar da baki, yayin da wasunsu za su sayar da abinci. Ka san muna da wasu fasahohin al'adun musamman na kabilar Qiang kamarsu rawa da waka da sassaka, to, abubuwan za su ba mu damarraya aikin yawon shakatawa a wurin".
Madam Shi, wata mace da ke kauyen Jina, dama ta yi kokarin ciyar da iyali bisa aikin gona. Amma yanzu, tana zama cikin sabon gida, ta fara sayar da wasu kayan al'adun a wani filin da ke cikin kuayen. Ko da yake ba a samu baki masu yawon shakatawa da yawa ba tukuna, amma Madam Shi tana da imani kan samun makoma mai kyau a nan gaba. Ta ce,
'Idan an samu damar raya aikin yawon shakatawa sosai, to, sannu a hankali, za a fara aiwatar da aikin sayarwa lami lafiya. Shi ya sa ina fata za mu kara samun baki da ke zuwa wurinmu don yawon shakatawa.'
Sa'an nan aikin da ake yi na bunkasa sha'anin yawon shakatawa da na sayarwa ya samu goyon baya daga gwamnatin kasar Sin, domin ana tsamanin cewa ta hakan za a iya kyautata zaman rayuwar mutanen wurin, da kuma kara yada al'adun wurin. (Bello Wang)
|