Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-05-12 16:21:21    
Shirye-shiryen musamman na tunawa da ranar cika shekara daya da aukuwar bala'in girgizar kasa a gundumar Wenchuan a ranar 12 ga watan Mayu

cri

Ranar 12 ga watan Mayu, rana ce da ke da ma'anar musamman ga al'ummar Sinawa, a shekara daya da ta gabata, an yi girgizar kasa da karfinta ya kai digiri 8 bisa ma'aunin Richter a gundumar Wenchuan da ke lardin Sichuan a kudu maso yammacin kasar Sin, mutane 68712 sun mutu, tare da bacewar wasu 17921, kawo yanzu, shekara daya ke nan. A cikin shirinmu na yau na Sin da Afrika, muna son mu ce, yaya lardin Sichuan, yaya jama'ar wurin? To, masu sauraro, sai a kasance tare da mu, domin jin yadda Sichuan yake?

Kullum da safe, malam Dong Zhenji ya kan je yawo a kauyen Qipan da ke gundumar Xiang'E a birnin Du Jiangyan, sabo da ya yi zama a can. Manyan gidaje sun tashi kusa da tsaunuku, maziyarta za su iya cewa gidajen a kauyen can sun yi kama da unguwanni a manyan birane na kasar.

Mr. Dong Ya ce, "Ban taba tsammani zan iya zama a gidaje kaman haka ba, ko da yake, gidana na da, na da kyau, amma idan aka kwatanta shi da irin wanda nike zama yanzu, lalle wannan ya fi kyau kwarai. Ga ruwa da gas da wutar lantarki ga kuma dakunan da aka gina da tubali, dukkansu sun fi gidana na da."

A lokacin da, a kauyen Qipan, mutane sun yi zama a kan tsaunuka, amma, yayin da ake samun girgizar kasa, galiban gidaje sun ragargaje ciki har da gidaje na malam Dong, amma bayan watanni 7 ne kawai, a ranar 22 ga watan Janairu na shekarar bana, Mr. Dong ya yi kaura zuwa sabbin gidaje, dukkan jama'a, manyan da kanana sama da 1500 sun shiga cikin sabbin gidaje, gwamnatin wurin ta tsara fasalin unguwannin gidaje kuma ta rarraba dukkan gidaje ga jama'a, da kowannensu ya samu gidajen da fadinsu sun kai murabba'in mita 35. A iyalin Dong, akwai mutane 9, sun samu gidaje guda 2 ke nan.

A gun girgizar kasa, ba ma kawai an lalata kauyen Qipan ba, kana an lalata dukkan gundumar Xiang'e, kusan dukkan gidaje sun ragargaje, yanzu, gwamnatin birnin Chengdu na taimakawa gundumar Xiang'e wajen gina unguwanni kaman haka har guda 16, domin taimakawa jama'a da bala'in girgizar kasa ya ritsa da su, don su iya kaura zuwa sabbin gidaje kafin lokacin hunturu na wannan shekara.

Ba ma kawai, ana bukatar sake gina gidaje ba, har ma ana bukatar gina wata makarantar sakandare, da makarantun firamare guda 2, sabo da dukkansu sun lalace a sakamakon girgizar kasar, amma yanzu bisa taimakon daga birnin Shanghai, wata sabuwar makaranta ta riga ta tashi.

A wuraren da ake aikin gini, daruruwan ma'aikata na kokarin aiki, suna gina makarantar firamare na gundumar Xiang'e, kuma bayan da aka gina ta, za ta zama makaranta ta farko da aka gina da katako, kuma dukkan katakan da aka yi amfani da su, an sami su ne bisa akidar jin kai daga kasar Canada.

Jami'i mai kula da aikin sake ginawa na ma'aikatar ilmi ta birnin Du Jiangyan Zhang Pin ya bayyana cewa, Ana gudanar da aikin sake gina sabuwar makarantar firamare Xiang'e kamar yadda aka tsara, daga fasali zuwa labarin kasa har zuwa aikin sa ido kan ingancin gidaje.

Aikin sake gina gundumar Xiang'e shi ne daya daga cikin manyan ayyukan sake ginawa da aka yi a lardin Sichuan, gwamnatin tsakiya ta tsara larduna da birane 19 da suka fi karfin tattalin arziki wajen taimakawar wadannan wuraren da bala'in ya shafa. A karkashin kokarin da aka yi, a cikin shekara daya da ta gabata har zuwa yanzu, ana gudanar da aikin sake gina birane Shifang da Beichuan da Wenchuan da Mianzhu lafiya, kuma dukkan inda ka zo, ana iya ganin ko wane mutum na kokarin aiki.

Sakatariyar ofishin kula da aikin ginawa ta lardin Sichuan Tian Liya, ta bayyana cewa, game da wasu gidajen da suka lalace a gun girgizar kasar, gwamnatin ta sake yin gyaggyare gare su, amma game da gidaje miliyan 1 da suka ragargaje a gun girgizar, gwamnatin ta sake gina sabbin gidaje, don cika gurbinsu.

Domin tabbatar da ingancin gidaje da saurin aikin ginawa, masana da kimiyya sun tsara sabbin fasahohi wajen ginawa gidaje, kuma sun tsara fasalin gidaje 400 bisa bambancin labarin kasa da bambancin kabilu da bambancin bukatu wajen yaki da girgizar kasa.

Yauzu, a lardin Sichuan, mutane fiye da dubu 70 sun bar gidajen wucin gadi, kuma sun yi kaura zuwa sabbin gidaje, lardin Sichuan ta yi shirin kammala dukkan aikin sake gina kauyuka kafin karshen shekarar bana, kuma za a kammala dukkan aikin sake gina birane kafin watan Mayu na shekarar badi, ya zuwa wancan lokaci, duk wanda ya rasa gidajensu a sakamakon girgizar kasa, zai yi kaura zuwa sabbin gidajensu.

Mataimakin Direkta na kwamitin yin gyare-gyare na kasar Sin Mu Hong ya ce, yanzu ana gudanar da aikin sake gina makaratu a wuraren da bala'in ya abku cikin armashi. )

Yanzu, ana gundar da aikin sake ginawar makarantu cikin saurin. Yaran da yawansu ya kai kashi 70 cikin kashi 100 sun yi karatu a sabbin makarantu.

Kana, a cikin aikin sake ginawa da aka yi, ba ma kawai ana bukatar saurin kammala aiki ba, kana ana sa ido sosai a kan ingancin injiniyoyi.

A cibiyar jin dadin jama'a ta birnin Shifang, babban injiniya mai kula da aikin sake gina birnin Shifang Huang Wenwei ya gaya mana cewa, kungiyar injiniyoyi ta cibiyar kula da jin dadin jama'a ta kunshi ma'aikata sama da 200, kuma kimmanin rabinsu, sun taba yin aiki a gun gasar wasannin Olympic ta Beijing.

Mun kula da ingancin aiki sosai, da dukkan kayayyakin ginawa da muka yi amfani da su, suna da izni, kuma yayin da muka gina gidaje, muna sa ido sosai a kan aikinmu.

A hakika dai, ba ma kawai ana bukatar sake ginawa manyan ayyuka da suka lalace ba, kana ana bukatar taimakawa dubun dubantar mutane da suka rasa kwarin gwiwa kan zaman rayuwarsu.

Wannan yarinya na gabatar da kanta da Turanci, sunanta Qing Fangrui, ita daliba ce a makarantar Guangya da ke birnin Du Jiangyan na lardin Sichuan a kasar Sin, kuma kafin aw'o'i da aka yi girgizar kasa, iyayenta sun je makarantar kallonta, amma abin bakin ciki ne, sabo da a kan hanyar komawa gida, an yi girgizar kasa, manyanta sun bace.

Yara da suka zama marayu a sakamakon girgizar kasar sun yi yawa, sabo da iyayensu sun rasu, ba su so su yi magana, kullum sun yi shiru.

Wu Xiaoxia, malama ta Qing Fangrui ta gaya mana cewa, gwamnati ta ba da kudin taimako da yawansa ya kai 600 a ko wane wata, zaman rayuwar Fangrui ya kyautu.

Daga Lahadi zuwa Jumma'a, Fangrui ta kan yi zama tare da sauran dalibai, sun yi kamar 'yan uwa da abokai. A karshen mako, ta kan je wasa tare da sauran dalibai, kuma a ko wane wata, kawunta ya kan je ya dauke ta. Sabo da haka, ta sami sauki.

Bayan da girgizar kasa ta auku, Fangxu wani mutum da ke zama a birnin Du Jiangyan, a karkashin kokarin da aka yi, ya sami wani aiki mai kyau, ya zama ma'aikaci mai kula da aikin ginawa. Ya ce, Bayan da girgizar kasa ta auku, farashina ya hau, na iya samun kudi Yuan dubu 2 a ko wace wata, a da, sai Yuan dubu 1 ne kawai, gwamnatin ta ba mu gudummawa mai yawa.

Sakatare janar na gwamnatin lardin Sichuan Yu Wei ya bayyana cewa mutane kimanin milliyan 1.3 sun sake samun ayyukan yi.

Ana gudanar da sake ginawa a lardin Sichuan lafiya, jama'ar Sichuan na hawa wahalhalun da ke gabansu, sun tafi abinsu. (Bako)