A gun taron shekara-shekara na dandalin tattaunawar Asiya na shekara ta 2009 da aka rufe kwanan baya a garin Bo'ao na lardin Hainan da ke kudancin kasar Sin, muhimman 'yan siyasa da 'yan kasuwa da masana na kasar Sin da na kasashen waje sun zura idanunsu kan makomar tattalin arzikin kasar Sin. Wasu kyawawan sauye-sauyen da kasar Sin ta samu a fannin tattalin arziki sun sanya a gano wata kyakkyawar makoma wajen fama da matsalar kudi ta duniya.
A cikin jawabin da firayin minista Wen Jiabao na kasar Sin ya yi a gun taron Bo'ao, ya bayyana cewa, halin da kasar Sin ke ciki a fannin tattalin arziki ya fi wanda aka yi hasashe kyau.
"Da farko dai, yawan kudaden da ake zubawa ya karu cikin sauri sosai. A waje daya, yawan kudaden da masu sayayye suka kashe shi ma ya karu sosai. Bukatun da ake nema a kasuwannin cikin gida sun yi ta karuwa. Bugu da kari kuma, masana'antu sun soma farfadowa yadda ya kamata a kai a kai. Aikin gona ma yana cikin yanayi mai kyau. Haka kuma, an samu ci gaba wajen daidaita sana'o'in masana'antu, kuma yankuna daban daban suna samun ci gaba cikin halin daidaito. Dadin dadawa, yawan mazauna garuruwa da suka samu aikin yi ya soma karuwa, yawan kudin shiga da mazauna suke samu ma ya karu. Daga karshe dai, ana tafiyar da bankunan kasar Sin kamar yadda ya kamata."
Tun daga karshen rabin shekara ta 2008, a sakamakon matsalar kudi ta duniya, yawan kayayyakin da kasar Sin ta kan fitar da su zuwa kasashen waje ya ragu, masana'antu da yawa sun shiga mawuyacin hali, kuma yawan mutanen da suka rasa guraban aikin yi ya karu, har ma yawan kasafin kudin da gwamnatin kasar Sin take samu ya ragu cikin sauri. A gaban wannan mawuyacin halin da take ciki, gwamnatin kasar Sin ta dauki matakan farfado da tattalin arziki daga dukkan fannoni cikin daidai lokaci. Alal misali, ta dauki matakan habaka bukatu a kasuwannin cikin gida da zuba makudan kasafin kudi da daidaita shirin farfado da sana'o'i goma da kara saurin kyautata fasahohin zamani da kuma daga matsayin ba da tabbaci ga zaman al'umma domin bunkasa tattalin arziki.
Ya zuwa yanzu an soma samun kyakkyawan sakamako bayan da aka aiwatar da wadannan manufofi da matakai. A cikin watanni 3 na farkon shekarar da ake ciki, saurin karuwar tattalin arzikin kasar Sin ya wuce kashi 6 cikin kashi dari. Ko da yake ya ragu da kashi 4.5 cikin kashi dari bisa na makamancin lokaci na shekarar bara, amma a lokacin da tattalin arzikin sauran kasashen duniya yake raguwa cikin sauri, ba abu ne mai sauki ba ga kasar Sin ta samu karuwar tattalin arziki cikin sauri kamar haka. Halin da ake ciki a fannin tattalin arzikin kasar Sin ya fi hasashen da aka yi kyau.
Masu tafiyar da masana'antu wadanda suka sha wahalhalu a lokacin da ake fama da matsalar kudi ta duniya sun kuma bayyana cewa, yanzu kasuwa tana samun farfadowa a kai a kai a kasar Sin. Mr. Ding Lei, babban direktan kamfanin kera motoci kirar General na Shanghai wanda ya halarci taron shekara-shekara na Bo'ao na daya daga cikinsu. Yana ganin cewa, sana'ar kera motoci na daya daga cikin sana'o'in da suka samu moriya a sakamakon shirin ingiza tattalin arziki da gwamnatin kasar Sin take aiwatarwa. Mr. Ding ya ce, "A karshen shekarar da ta gabata, mun dauka cewa, mai yiyuwa ne za mu shiga mawuyacin hali sosai a cikin watanni 3 na farkon shekarar bana, sai ga shi tun daga watanni uku na mataki na biyu ko watanni 3 na mataki na uku na shekarar da ake ciki, mai yiyuwa za a samu farfado da tattalin arziki a kai a kai. Amma a hakika dai, yawan motocin da aka sayar a cikin watanni 3 na farkon shekarar da ake ciki ya karu da kashi 5.6 cikin kashi dari bisa na makamancin lokacin shekarar bara. Daga cikinsu, yawan motoci masu daukar fasinja da aka sayar ya karu da kashi 7.4 cikin kashi dari. Wannan ya bayyana cewa, an soma samun karin bukatu a kasuwa."
Bisa kididdigar da aka yi, an ce, a cikin watanni 3 na farkon shekarar da ake ciki, lokacin da kasar Amurka take samun raguwar yawan motocin da ake sayarwa, yawan motocin da ake sayarwa a kasuwar kasar Sin yana ta karuwa. Yawan motocin da aka sayar a kasuwar kasar Sin a cikin watanni 3 na farkon shekarar da ake ciki ya kai miliyan 2 da dubu 680, wato ya karu da kashi 3.88 cikin kashi dari.
A cikin dogon lokacin da ya gabata, jarin da ake zubawa na daya daga cikin muhimman karfin ci gaban tattalin arzikin kasar Sin. Bisa kididdigar da babban bankin kasar Sin, wato bankin jama'ar kasar Sin ya bayar, an ce, a cikin watanni 3 na farkon shekarar da ake ciki, yawan karin rancen kudi da aka samar ya kai kudin Sin yuan biliyan 4580, wato ya wuce karin rancen kudaden da aka samar a duk shekarar da ta gabata. Sakamakon haka, wasu manazarta suna nuna damuwa kan cewa, ko wadannan irin rancen makudan kudi za su haddasa hadarurruka? A yayin taron shekara-shekara na Bo'ao, a bayyane Mr. Liu Mingkang, shugaban kwamitin sa ido kan bankunan kasar Sin ya bayyana cewa, za a iya sassauta hadarurrukan da irin wadannan irin rancen makudan kudi za su haddasa.
"Ana zuba sabbin rancen kudin da yawansu ya kai fiye da kudin Sin yuan biliyan dubu 4 kan muhimman ayyukan yau da kullum na kasar. A waje daya kuma, an zuba wasu daga cikinsu kan ayyukan da suke da nasaba da zaman rayuwar jama'a da ayyukan cinikayya, alal misali, kan dakunan ajiye kayayyaki da ayyukan sufurin kayayyaki. A hakika dai, yawan karin rancen kudin da aka zuba kan masana'antu ya yi kadan. Haka kuma, yawan rancen kudin da aka zuba kan ayyukan da suke amfani da dimbin makamashi da albarkatun halittu da kuma gurbata muhalli ya ragu. Ko shakka babu, za a haifar da wasu hadarurruka idan an samar da karin rancen kudi masu dimbin yawa cikin sauri, amma ina tsammani cewa, za mu iya sassauta irin wadannan hadarurruka."
Baki mahalarta taron shekara-shekara na Bo'ao na shekarar 2009 sun gano kyawawan sauye-sauyen da kasar Sin ta samu a fannin tattalin arzikinta. Sun kuma yaba wa matakan da kasar Sin ta dauka domin tinkarar matsalar kudi ta duniya. Kamfanin samar da kayayyakin yau da kullum na kasar Saudiyya kamfani ne da ke samar da takin zamani da kayayyakin leda da sauran kayayyakin sinadari. Kuma yana sayar da kusan rabin kayayyakinsa a kasuwannin kasashen Asiya. A yayin taron shekara-shekara na Bo'ao, Mr. Mohammed Almady, jami'in farko na wannan kamfani ya bayyana cewa, zai ci gaba da sa rai kan kasuwar kasar Sin, kuma kamfaninsa zai ci gaba da zuba jari a kasar Sin. Mr. Almady ya ce, "Mun riga mun gano wasu alamun da suke farfado da tattalin arzikin kasar Sin, kuma shirin ingiza tattalin arziki da kasar Sin ta dauka yana taka rawa. Ina kuma fatan irin wadannan jerin matakan da gwamnatin kasar Sin ta dauka za su zama matakin ciyar da tattalin arzikinta gaba cikin sauri. Halin da tattalin arzikin kasar Sin yake ciki zai yi tasiri sosai ga kamfaninmu."
Ko da yake an soma samun alamun farfado da tattalin arzikin kasar Sin, amma a lokacin da matsalar hada hadar kudi ta duniya take ci gaba da bazuwa a duk duniya, kuma har yanzu ba a samu sauyi a halin tabarbarewar tattalin arzikin duniya ba, kasar Sin tana fuskantar kalubale mai tsanani a fannin tattalin arziki. Sakamakon haka, Mr. Zhou Xiaochuan, shugaban babban bankin kasar Sin ya yi sharhi kan halin da kasar Sin ke ciki a fannin tattalin arziki da cewar, "Ko da yake kasar Sin ta samu wasu alamun farfado da tattalin arzikinta, amma har yanzu tana cikin matakin fama da matsalar kudi ta duniya da rikicin tattalin arziki daga dukkan fannoni."
Bugu da kari kuma, a matsayin rukunin tattalin arziki mafi girma a duniya da kuma rukunin da ke sheda ci gaban tattalin arziki mafi sauri, kasar Sin wata muhimmiyar jigo ce wajen ciyar da tattalin arzikin duniya gaba. Mr. Kenneth Morgan, shehun malamin jami'ar Australiya ta yamma ya bayyana cewa, "Ko da yake kasar Sin tana fuskantar kalubale iri iri har yanzu, amma idan wani ya yi tambaya cewa wace kasa take da wata makoma mai haske? Ko shakka babu kasar Sin tana daya daga cikinsu." (Sanusi Chen)
|