Bala'in girgizar kasa da ya auku a ran 12 ga watan Mayu na shekarar bara ba zato ba tsammani a lardin Sichuan ya sanya mutanen wurin sun rasa gidajensu, yara ma sun rasa wuraren koyon ilmi baki daya. Bayan shekara daya da ta gabata, wakilanmu sun je yankunan da suke fama da bala'in girgizar kasa na lardin Sichuan sun gano cewa, yara sun sake samun damar yin karantu a wurare daban daban, kamar a kwarya-kwaryan dakunan karatu ko a cikin sabbin makarantun da aka gina. Murmushi ma ya koma fuskokin yara.
Makarantar midil ta Beichuan tana birnin Mianyang inda aka samu bala'in girgizar kasa mafi tsanani a duk lardin Sichuan. Bayan kwanaki 7 da aka yi girgizar kasa, an kwashe dukkan daliban makarantar midil ta Beichuan zuwa cibiyar horar da ma'aikata ta wani kamfanin da ke kusa da ita. Mr. Li Xueyan wanda ke kula da makarantar midil ta Beichuan ya bayyana cewa, a watan Satumba na shekarar da ta gabata, wasu dalibai masu koyon ilmin kide-kide na jami'ar horar da malamai ta babban birni na birnin Beijing sun je makarantar midil ta Beichuan a matsayin masu aikin sa kai. Sabo da haka, an gwada bude kwas din kide-kide da zane-zane domin kwantar da hankalin dalibai wadanda suka tsorata su a sanadiyyar bala'in girgizar kasa. Mr. Li ya ce, "Yanzu muna amfani da wadannan dalibai da malamai na jami'ar horar da malamai ta babban birni na birnin Beijing muna gwada koyar da ilmin kide-kide da zane-zane. A cikin aji na farko da na biyu na matakin karshe na makarantarmu, mun bude kwas din ga dalibai wadanda suke son koyon ilmin kide-kide da zane-zane. Ba ma kawai muna koyar da ilmin kide-kide da zane-zane domin dalibai su nuna sha'awarsu ba, har ma muna koyar da su bisa bukatun da dalibai suke da su domin cin jarrabawar shiga jami'o'in koyar da ilmin kide-kide da zane-zane."
Bayan bala'in girgizar kasa, daliban makarantar midil ta Beichuan da yawa sun zama nakasassu. Sabo da haka, makarantar midil ta Beichuan ta bude kwas din kide-kide da zane-zane domin kwantar da hankalinsu.
Zhang Zhujun wadda ke koyon ilmin kide-kide a aji na 3 na jami'ar horar da malamai ta babban birni na birnin Beijing ta gaya wa wakilinmu cewa, yanzu, tana koyon wani kidan fiyano mai suna "oriental cherry", kuma tana son koyar wa dalibai wannan kida. Yarinya Zhang Zhujun ta ce, tana fatan dalibai za su iya sake samun imani da farin ciki daga kide-kide.
"Na girme su shekaru da 3 ko 4 da haihuwa ne kawai. Muna fahimtar juna sosai. Kafin in zo wannan wuri, lokacin da nake koyon kide-kide, ina tsammani kide-kide hanya ce kawai a gare mu domin bayyana abubuwan da muke zata. Amma bayan isowata a nan, na gano cewa, kide-kide sun iya hada mu duka."
A hakika dai, bala'in girgizar kasa bai yi illa ga fatan da ke cikin zukatun yara ba. Yarinya Guo Dongmei, mai shekaru 16 da haihuwa ta rasa kafa ta hagu a sanadiyyar bala'in, amma ta gaya wa wakilinmu cewa, fata mafi muhimmanci a cikin zuciyarta shi ne tana son zama wata likitar da za ta iya taimakawa sauran mutane a nan gaba.
"Ina son zama wata likita sabo da wannan aiki yana da kyau. Bayan na zama likita, zan iya taimakawa mutane da yawa. Marasa lafiya za su iya samun sauki."
Mr. Li Xueyan, shugaban makarantar midil ta Beichuan ya bayyana cewa, yanzu hukumar da abin ya shafa tana tsara shirin gina wata sabuwar makarantar zamani domin samar da kyawawan sharudan koyon ilmi ga yara.
An labarta cewa, yawan makarantun da suka lalace a sanadiyyar bala'in girgizar kasa da ya auku a ran 12 ga watan Mayu na shekarar da ta gabata a duk lardin Sichuan ya kai fiye da dubu 13. A cikin wannan shekara daya da ta gabata, ana ta kokarin farfado da aikin koyarwa cikin sauri fiye da kima. Alal misali, a kashegari bayan aukuwar bala'in, nan da nan ne dalibai suka sake bude kwas a cikin wani tanti a birnin Dujiangyan. A cikin watanni 4 bayan bala'in girgizar kasa, dukkan makarantu sun sake bude kwas a cikin kwarya-kwaryan dakunan koyarwa. Bisa shirin da aka tsara, kafin ran 1 ga watan Satumba na shekarar da ake ciki, galibin daliban yankunan da suka gamu da bala'in girgizar kasa yau da shekara daya da ta gabata za su shiga sabbin zaunannun makarantu.
Sabo da haka, lokacin da wakilanmu suke neman labaru a wadannan yankuna, sun ga ana gina sabbin makarantu cikin gaggawa. Makarantar firamare ta Xiang'e wadda ke arewa maso gabashin karkarar birnin Dujiangyan na daya daga cikinsu.
A yayin gina sabuwar makarantar firamare ta Xiang'e, 'yan kwadago fiye da dari 1 sun sha aiki. Bisa labarin da aka bayar, an ce, wannan makarantar firamare ta Xiang'e wadda ake ginawa makaranta ce ta farko da aka gina da katako kawai a kasar Sin. Kasar Canada ce ta samar da dukkan katakon da ake bukata kyauta. Mr. Zhang Ping wanda ke kula da aikin gina sabbin makarantu na hukumar ilmi ta birnin Dujiangyan ya bayyana cewa, an rushe tsohuwar makarantar firamare ta Xiang'e a cikin bala'in girgizar kasa. Sakamakon haka, gwamnatin wurin ta zabi wani wuri na daban domin gina wata sabuwar makarantar firamare ta Xiang'e. Ya zuwa yanzu, an riga an kammala manyan tsare-tsare na ajujuwa da dakunan kwana. Mr. Zhang Ping ya ce, "Cibiyar zayyana gine-gine ta jami'ar Tongji ta Shanghai ce ta zayyana sabuwar makarantar firamare ta Xiang'e. Sannan kamfanin injiniya na Lvdi na birnin Shanghai yake gina ta. Za a kammala aikin gina ta baki daya a ran 30 ga watan Yuli, kuma za a iya yin amfani da ita a lokacin da ake soma sabuwar shekara ta karatu tun lokacin kaka na shekarar da ake ciki."
An bayyana cewa, fadin sabuwar makarantar firamare ta Xiang'e wadda take kunshe da ajujuwa da dakunan kwana da dakin cin abinci da filin wasa ya kai murabba'in mita dubu 5. Dalibai 540 za su iya yin karatu a cikin wannan sabuwar makaranta. A waje daya, Mr. Zhang Ping ya bayyana cewa, an dauki ma'aunin fama da bala'in girgizar kasa mafi tsanani lokacin da ake zayyana da kuma gina makarantar firamare ta Xiang'e.
"An zayyana da kuma gina makarantar firamare ta Xiang'e ne bisa ma'aunin musamman da ma'aikatar gine-gine ta kasar Sin ta tsara. Birnin Dujiangyan yana zirin da a kan samu girgizar kasa. Sabo da haka, lokacin da ake gina sabbin gine-gine, gwamnati tana bukatar a gina su bisa karfin girgizar kasa da mai yiyuwa ne za a yi. Sakamakon haka, ana gina sabbin gine-gine a birnin Dujiangyan bisa karfin ma'aunin girgizar kasa na 8. haka kuma, a lokacin da ake yin gine-ginen jama'a, dole ne a kara digiri 1 na karfin ma'aunin girgizar kasa. Sakamakon haka, mun zayyana da kuma gina makarantar firamare ta Xiang'e ne bisa karfin girgizar kasa da mai yiyuwa ne zai kai digiri na 9. Sannan za mu aika da wasu rukunonin sa ido kan ingancin makarantar domin tabbatar da ingancinta."
Abin da ya kamata a ambata shi ne lokacin da ake gina makarantar firamare ta Xiang'e, an yi amfani da fasahohin zamani da yawa. Mr. Yang Jiancheng, injiniya na kamfanin Lvdi na birnin Shanghai ya bayyana cewa, "Tsarin da aka yi da katako yana iya yin fama da girgizar kasa, kuma yana iya tabbatar da ingancin muhalli. Kuma mun manna filasta a kan katako domin maganin gobara. A waje daya, mun shimfida bututuwan sufurin ruwa na maganin gobara a cikin rufin dakunan karatu da na kwana. Bugu da kari kuma, za a kara sabbin na'urorin koyarwa a cikin wannan sabuwar makaranta."
Yanzu, dalibai da malamai na makarantar firamare ta Xiang'e suna fatan za su iya shiga wannan sabuwar makaranta tun da wuri. Pan Jiao wadda take aji na 6 ta gaya wa wakilinmu fatanta cewa, "Sabuwar makaranta tana da kyan gani kwarai. Mutanen kirki da yawa suna taimaka mana. Dukkansu fararen hula ne, amma abubuwa da yawa da suka yi sun burge mu sosai. Sakamakon haka, ina fatan zan iya zama wani mutum mai aikin sa kai a nan gaba."
Jama'a masu sauraro, ko makarantar firamare ta Xiang'e, ko a makarantar midil ta Beichuan, ana nuna tausayi ga wadanda suka sha wahalar bala'in girgizar kasa, kuma ana amfani da fasahohin zamani a cikin sabbin makarantun da ake ginawa. Tabbas ne yara za su iya cimma burinsu a nan gaba. (Sanusi Chen)
|