Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-05-08 21:42:20    
Fatan alheri ga Sichuan

cri
Masu sauraro, idan ba ku manta ba, a ran 12 ga watan Mayu na shekarar 2008 da ta gabata, girgizar kasa mai tsanani da karfinta ya kai digiri 8 bisa ma'aunin Richter ta afka wa lardin Sichuan da ke kudu maso yammacin kasar Sin, kuma a sakamakon girgizar, mutane 68712 sun mutu, a yayin da wasu 17921 suka bace tare kuma da wasu miliyoyi da suka rasa gidajensu. Girgizar kasar ta kuma jawo hankulan kasashen duniya sosai, ciki har da masu sauraronmu a kasashen Hausa. Ina iya tunawa da dimbin sakonnin da kuka turo mana bayan aukuwar girgizar kasar, inda kuka bayyana bakin ciki da ta'aziyya ga asarorin jama'a da dukiyoyi a sanadiyyar girgizar kasar. Girgizar kasar ta girgiza zaman rayuwar jama'ar lardin Sichuan gaba daya, ta kuma jikkata wannan yanki mai ni'ima.

Amma abin farin ciki shi ne, yanzu ayyukan farfado da yankunan da bala'in ya shafa a lardin Sichuan na gudana yadda ya kamata, kuma jama'ar Sichuan suna samun sauki daga raunukan da wannan babbar masifa ta haddasa musu, kuma suna zaman rayuwa cikin kwanciyar hankali. Kwanan baya, a gun wani taron manema labarai da hukumar lardin Sichuan ta kira, an ce, za a kammala ayyukan sake gina gidajen kwana a kauyukan lardin Sichuan kafin karshen wannan shekara, kuma kafin karshen watan Mayu na shekara mai kamawa, za a kammala aikin sake gina gidajen kwana a birane da garuruwa na lardin. Ban da wannan, hukumar lardin Sichuan ta kuma gabatar da cewa, ya zuwa watan Satumba na shekarar 2010, za a tabbatar da kowane iyali ya samu gidan kwana da kuma aikin yi, kuma kowa na samun tabbacin zaman rayuwa. Bayan haka, za a kuma yi kokarin neman cimma burin samun ci gaban tattalin arziki da kyautatuwar muhallin zama a wurin. Bayan aukuwar girgizar kasa a lardin Sichuan, bangarori daban daban sun samar da taimako sosai ga yankunan da bala'in ya galabaitar, kuma ya zuwa yanzu, yawan kudin taimako da bangarori daban daban suka samar wa lardin Sichuan ya kai kudin Sin yuan biliyan 15 da miliyan 750.

Bayan haka, a gabannin zagayowar ranar cika shekara guda da aukuwar girgizar kasar, wakilanmu sun kai ziyara ta musamman zuwa yankunan da girgizar ta galabaitar a lardin Sichuan, inda suka gane wa idonsu farfadowar wuraren bisa taimakon da bangarori daban daban ke samar musu.

Hasali ma dai, tun daga ran 5 ga wata, mun fara gabatar muku jerin shirye-shiryenmu na musamman game da ziyarar da wakilanmu suka yi a lardin Sichuan, domin tunawa da cika shekara daya da aukuwar girgizar kasa a lardin, kuma a yanzu haka muna ci gaba da gabatar muku da shirye-shiryen a shirinmu na kowace rana har zuwa Litinin mai zuwa. Muna fatan za ku bi sawun wakilanmu zuwa yankunan da girgizar kasar ta shafa, ku saurari sauye-sauyen da ke aukuwa a wuraren, da kuma farfadowar lardin Sichuan.

A kusantowar ran 12 ga watan Mayu, wato ranar cika shekara daya da aukuwar girgizar kasa mai tsanani a lardin Sichuan na kasar Sin, masu sauraronmu sun kuma aiko mana sakwanni, don isar da gaishe-gaishensu da kuma fatan alheri ga jama'ar Sichuan da girgizar kasar ta galabaitar.

Shehu Abdullahi daga Funtua, jihar Katsina, tarayyar Nijeriya, ya ce, "Ina mai mika matukar alhinina ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu a bala'oin da sukai ta faruwa a kwanakin baya, da kuma fatan Allah zai kawo mana taimako da kare mu daga fuskantar irin wadannan balairar."

Mamane Ada a birnin Yamai, jamhuriyar Nijer, wanda ya ce, "Hakika ranar 12 ga watan mayu na wannan shekara za ta kasance rana ta juyayi ga al'ummar Sinawa da ma duniya baki daya, domin yin tunanin abun tashin hankalin da ya abku yau da shekara guda a lardin Sichuan da girgizar kasa mai tsanani ta yi sanadiyar mutuwar dimbin mutane da kuma jawo asarar dukiyoyi. Ina aika ta'aziyya da juyayina ga dangin da wannan bala'i ya rutsa da su amen.

Bayan haka, Lami Sulaiman daga garin Bauchi, tarayyar Nijeriya, ta ruwaito mana sakon cewa, "yau da shekara da ta wuce, girgizar kasa ta auku a lardin Sichuan na kasar Sin, wadda ta haddasa manyan asarori ga aminanmu Sinawa, kuma ta bata mana rai sosai. A zagayowar wannan rana ta bakin ciki, ina sake nuna muku ta'aziyya ga wadanda suka mutu, kuma ina nan ina addu'ar Allah ya kare mu daga karin bala'u, kuma ina yi wa mutanen lardin Sichuan fatan alheri na samun zaman rayuwa cikin kwanciyar hankali da jin dadi."

Sai kuma sakon da Mohammed Talle a Kano, tarayyar Nijeriya, ya aiko mana ya nuna cewa, "Ina yi maku jaje bisa ga abin da ya faru na girgizar kasa da kuma yi muku ta'aziyya ga wadanda suka mutu bisa wannan bala'i."

Har wa yau kuma, Bala Mustafa ya ce, "ina fatan Allah zai saka wa jama'ar Sichuan da alheransa, ina kuma mai addu'ar ya kare mu baki daya daga sharri."

To, mun ji gaishe-gaishenku, kuma mun gode. Masu sauraro, a nan kasar Sin, mutanen lardin Sichuan sun shahara ne musamman da hazaka da jaruntaka da kuma walwala, ga shi bisa kokarinsu, lardin Sichuan na farfadowa, har ma muna iya hango makomarsu mai kyau, kuma muna yi musu addu'ar samun alherai a zaman rayuwarsu.

Hasali ma dai, bayan aukuwar girgizar kasa a lardin Sichuan, gwamnatin kasar Sin ta tabbatar da ran 12 ga watan Mayu na kowace shekara da ta zama ranar yaki da bala'u daga indallah ta kasar, kan wani kokari na fadakar da jama'a kan ilmin yaki da bala'u daga indallah da na fasahohin ceton kai a gabannin aukuwar bala'u, ta yadda za a sassauta hasarorin da bala'un ke haddasawa.

To, a karshe, muna sake nuna fatan alheri na samun makoma mai kyau ga jama'ar Sichuan da sauran wadanda bala'u suka rutsa da su a duniyarmu, kuma muna addu'ar Allah ya kare 'yan Adam baki daya daga bala'u. (Lubabatu)