Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-05-01 19:29:26    
Yau ya rage shekara guda da bude bikin baje-koli na kasa da kasa na Shanghai a shekarar 2010

cri

Yau wato ran 1 ga wata ya rage saura shekara guda da kaddamar da bikin baje-koli na duniya na birnin Shanghai a shekarar 2010. Yanzu ana gudanar da ayyukan gina dakunan nune-nune da tsara shirin baje-koli da tafiyar da harkokin bikin yadda ya kamata. Masu shirya bikin sun lashi tabokin cewa, nan da shekara guda mai zuwa za su ci gaba da share fagen bikin domin samar wa kasashen duniya wani bikin baje-koli mai nasara da kayatarwa, wanda kuma ba za su iya mantawa ba.

Ran 1 ga wata da safe, a babban filin Tian'anmen da ke nan birnin Beijing, an cire kyallen allon yawan kwanakin da suka rage da bude bikin baje-koli na kasa da kasa na Shanghai na shekarar 2010, inda Wu Bangguo, shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ya ce, gwamnatin Sin da jama'ar Sin sun lashi takobi a hukunce da cewa, za a shirya bikin baje-koli na kasa da kasa mai nasara da kayatarwa, wanda kuma ba za a iya mantawa ba. Yana mai cewar,"Yau mun yi bikin cire kyallen allon yawan kwanakin da suka rage da bude bikin baje-koli na kasa da kasa na Shanghai na shekarar 2010. Mun sake nuna wa kasashen duniya cewa, gwamnatin Sin da jama'ar Sin na mara wa shirya wannan kasaitaccen biki baya sosai. Za mu inganta hadin gwiwa da kasashe da kungiyoyin duniya da za su halarci bikin, za mu yi namijin kokarin share fagen bikin, ta haka za mu iya tabbatar da samun nasarar tafiyar da bikin."

Ya zuwa ran 1 ga wata, kasashe da kungiyoyin kasa da kasa guda 236 sun tabbatar da halartar bikin baje-koli na kasa da kasa na Shanghai. Ta haka bikin da za a yi a Shanghai ya fi samun kasashe da kungiyoyin duniya a tarihi.

Duk da haka a sakamakon lalacewar matsalar kudi ta duniya, bikin baje-koli na duniya na Shanghai shi ma ya samu rashin tabbaci kadan wajen tattara wadanda za su halarci bikin. Amma Yang Xiong, mataimakin magajin gari na birnin Shanghai kuma mamban kwamitin shirya bikin ya gaya wa wakilinmu cewa, ko da yake kasashe da yawa suna sha wahala a fannin tattalin arziki, amma suna fatan halartar bikin baje-koli na duniya zai iya samar da karfin zuciya da yin mu'amalar fasaha.

Carma Elliot, mataimakiyar babban wakilin kula da yankin nune-nune na kasar Birtaniya kuma karamar jakadan Birtaniya a birnin Shanghai ta gaya wa wakilinmu cewa, Birtaniya za ta cika alkawarinta na halartar bikin baje-koli na duniya. Nan da shekara guda mai zuwa za ta ci gaba da gudanar da ayyuka yadda ya kamata, inda ta ce,"Muna gaggauta fitar da shiri na shekarar gobe. Muna kuma neman samar da kudade da shirya harkokin da abin ya shafa. Ban da wannan kuma, mun riga mun fito da kasafin kudi kan shirinmu tukuna, a ganinmu, zuba jari kan shirin na da kyau kwarai da gaske. Shi ya sa a shekara mai zuwa, ba za mu sauya shirinmu da kuma nauyin da aka danko mana ba."

A ran 1 ga wata, a brinin Shanghai kuwa, an soma daukar masu aikin sa kai domin bikin baje-koli na kasa da kasa. Bisa shirin da aka tsara, an ce, masu aikin sa kai kusan dubu 200 za su bayar da hidima ga 'yan kallo daga sassa daban daban na duniya a shekara mai zuwa.

Yu Zhengsheng, sakataren kwamitin Shanghai na Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin kuma darektan kwamitin gudanarwa na bikin baje-koli na duniya na Shanghai ya nuna cewa, a shekara mai zuwa, kasar Sin za ta cika alkawarin da ta yi a yayin da ta samu damar shirya bikin a shekarar 2002, wato a bai wa kasar Sin wata dama, ta haka za ta iya kayatar da duniya sosai. Inda ya ce,"Yanzu ana share fagen bikin yadda ya kamata. Nan da shekara guda mai zuwa, za mu ci gaba da inganta hadin gwiwa da bangarorin da abin ya shafa, za mu bai wa wadanda za su halarci bikin da kafofin yada labaru da masana'antu da kuma 'yan kallo hidima mai kyau, za mu kuma aza harsashi mai kyau wajen samun nasarar shirya bikin mai kayatarwa, wanda kuma ba za a iya mantawa ba."(Tasallah)