Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-04-30 17:48:28    
Birnin Shanghai yana kokarin zama cibiyar sha'anin kudi da cibiyar zirga-zirga na duniya

cri
A ran 29 ga wata, ofishin watsa labaru na gwamnatin kasar Sin ya shirya wani taron manema labaru a birnin Shanghai, inda aka bayyana kan yadda birnin Shanghai, wato birni mafi girma wanda ke gabashin kasar Sin yake raya sana'o'in ba da hidima da masana'antun zamani domin kokarin zama cibiyar sha'anin kudi da cibiyar zirga-zirga na duniya.

Kafin wannan taron manema labaru, gwamnatin kasar Sin ta taba bayar da manufofi, inda ta tsai da kudurin cewa, za a kara saurin raya sana'o'in ba da hidima da masana'antun zamani a birnin Shanghai domin sanya birnin Shanghai ya zama cibiyoyin sha'anin kudi da zirga-zirga na duniya. Game da wannan kuduri, Mr. Liu Tienan, mataimakin shugaban kwamitin ci gaba da yin gyare-gyare na kasar Sin ya ce, "Tsarawa da kuma aiwatar da wannan shiri, ba ma kawai yana da muhimmiyar ma'ana ga kokarin sauya tsarin tattalin arziki da neman ci gaban birnin Shanghai cikin hali mai dorewa kuma cikin dogon lokaci ba, har ma abin da ya fi muhimmanci shi ne a wani muhimmin lokacin da ake fama da matsalar hada hadar kudi ta duniya, gwamnatin kasar Sin tana da niyyarta na ci gaba da yin gyare-gyare da bude kofa ga duniya, da kuma daidaita tsarin tattalin arziki da kyautata sana'o'in kasar domin tabbatar da karfin yin takara na kayayyakin kirar kasar Sin, da kuma karfin yin takara na duk kasar."

Bisa shirin da gwamnatin kasar Sin ta tsara, ya zuwa shekara ta 2020, birnin Shanghai zai zama cibiyar sha'anin kudi ta duniya wadda za ta yi daidai da karfin tattalin arzikin kasar Sin da matsayin da kudin Renminbi yake ciki a duniya. A waje daya kuma, lokacin da ake raya birnin Shanghai da ya zama cibiyar sha'anin kudi ta duniya, za a kara kyautata hanyoyin sa ido kan harkokin kudi. Sabo da haka, Mr. Tu Guangshao, mataimakin magajin birnin Shanghai ya bayyana cewa, "A lokacin da ake raya birnin Shanghai da ya zama cibiyar sha'anin kudi ta duniya, ba ma kawai za a kara yin gyare-gyare da bude kofa da kirkiro sabbin fasahohin daidaita harkokin kudi ba, har ma za a kyautata hanyoyin sa ido kan harkokin kudi. A gare ta, gwamnatin birnin Shanghai za ta dukufa ka'in da na'in wajen nuna goyon baya ga hukumomin sa ido kan sha'anin kudi domin kyautata hanyoyi da tsarin sa ido kan sha'anin kudi."

Game da batun raya birnin Shanghai da ya zama cibiyar zirga-zirga ta duniya, Mr. Yang Xiong, shi kuma mataimakin magajin birnin Shanghai ya bayyana cewa, "A cikin manufar da gwamnatin tsakiya ta bayar, a bayyane ne aka tabbatar da cewa, wani muhimmin nauyi shi ne kara saurin kafa tsarin zirga-zirga a birnin Shanghai. Sakamakon haka, zai zama nauyi mafi muhimmanci da ke bisa wuyanmu a nan gaba."

A gun taron manema labaru da aka shirya a birnin Shanghai, Mr. Liu Tienan, mataimakin shugaban kwamitin ci gaba da yin gyare-gyare na kasar Sin ya bayyana cewa, "Ta hanyar raya wadannan cibiyoyi biyu a birnin Shanghai, za a iya kara yin amfani da fifiko na birnin Shanghai domin kyautata tsarin sana'o'in masana'antu da canja hanyoyin neman ci gaban birnin Shanghai. Haka kuma, za a kara saurin kafa tsarin bude kofa mai amfani kuma mai kuzari. Sabo da haka, birnin Shanghai zai iya zama tamkar wani abin koyi ga duk kasar Sin wajen ci gaban tattalin arziki mai inganci cikin sauri, sannan birnin Shanghai zai ba da hidima ga duk kasar domin neman ci gaban tattalin arzikin duk kasar." (Sanusi Chen)