Bikin wasan zandoro wani muhimmin biki ne na kabilar Yarabawa, ko da yake ana yinsa ne tsakanin al'ummar Yorubawa a birnin Lagos da ke kudancin kasar Nijeriya, amma yayin da ake shirya wannan gagarumin biki, mutane su kan yi dafifi a kan tituna, haka kuma, mutanen kasashen waje da dama su ma su kan je kallon wannan biki.
Ba wai ana yin wannan biki ne a ko wace shekara ba, ana yinsa ne musamman yayin da manyan mutane suka mutu, a shekarar da muke ciki, an yi bikin wasan zandoro domin tunawa da wani marigayi kuma babban basarake na birnin Lagos Tos Benson. An shafe mako guda ana bikin.
A ranar 25 ga wata, jiga-jigan 'yan siyasa da sauran jama'a na birnin Lagos sun ci ado sosai, kuma sun taru a dandalin Tafawa balewa, domin taya murnar wannan biki. Haka kuma, domin kara ba da hidima mai kyau ga jama'ar da suka je domin halartar wannan biki, gwamnatin birnin Lagos ta kebe motar safa-safa ta musamman a kyauta domin daukar mutane. Amma sabo da mutane sun yi yawa, an cika samun cunkoson mutane a dandali.
Da misali karfe 12 da rana, aka fara yin bikin fareti a hukunce, jama'ar da ke cikin kungiyar faretin sun sa fararen taguwoyi, kuma sun sa kyallaye sun rufe fuskokinsu. Kuma dukkan kyallaye da ake sawa, ya danganta da mukamin mutum, akwai kyallaye na launukan baki da ja da rawaya da kore da shudi. Babban basarake yana da mukamin koli, sabo da haka ya kan sa kyallen baki, kuma an hana mutane su dauki hoto gare su, kana kuma mutanen da ke sa kyallaye suna rike wani dogon sanda a hannayensu, suna rera waka yayin da suke yin rawa. Game da wannan sanda, ba ma kawai wani abin ado ba ne, ana yi amfani da shi wajen dukan mutane da addu'o'i. Sabo da bikin zandoro na da ka'idoji da yawa masu ban mamaki da ke shafar bugun mutane ya jawo hankulan mutane sosai.
Yayin da ake yin wannan biki, an yi bikin faretin a wurare da dama a birnin Lagos, duk inda da masu fareti suka je, dole ne 'yan kallo su mutunta al'adunsu, wanda ya kunshi, 'yan kallo ba za su iya sa takalma ba, kana ba za su iya daukar hoto ba, kuma an hana shan taba da tukin babur, kuma mata za su iya sa siket ne kawai, kuma ba za su iya yin saka ba, kuma in an keta daya daga cikinsu, to, za a bugi wanda ya taka dokar. Sabo da haka, mutane da dama su kan nisanta kansu daga mutanen da ke sa kyallaye a fuskokinsu. Yayin da wakilimu ke zantawa da masu shirya wannan biki, ya yi tambaya da cewa, idan ya sa takalma kuma ya dauki hoto, ko za a buge shi. An ce, sa takalma da daukar hoto, dukkansu ba matsala ba ce, sabo da masu shirya bikin, suna son su shirya wannan biki don ya zama biki ne na dukkan duniya, sabo da haka, ba za su iya bugun mutanen kasashen waje ba. Yayin da yake zantawa da masu shirya bikin, wasu mutane suka dauke shi a matsayin wanda ya keta ka'idojinsu, kuma sun tambaye shi. Amma sabo da ya yi musu shiru, sai kowa ya kyale shi. Mutanen da ke kewaye da shi, suka ci gaba da murnar bikinsu.
Masu sauraronmu, idan ka girmama bikin Yarubawa na gargajiya, mutunen da ke sa kyallaye, za su so ka kuma za su yi maka a'ddu'o'i.(Bako)
|