Ya zuwa shekarar 1948, an sake shirya gasar wasannin Olympic a birnin London, kodayake an daina shirya gasar a cikin shekaru 12 da suka shige saboda faruwar yaki a duk fadin duniya. Kuma a gun gasar wasannin Olympic ta London, 'yan wasa maza ba su samu sakamako mai gamsarwa ba, amma 'yan wasa mata ba haka ba ne, sun fi jawo hankulan mutanen kasashen duniya, Fanny Blankers Koen tana daya cikinsu. A gun wannan gasar wasannin Olympic, 'yar wasa daga kasar Holand Koen ta samu lambobin zinariya hudu. A wancen lokaci, Koen tana da shekaru 30 na haihuwa, kuma ta riga ta haifi yara biyu, ana iya cewa, Koen ta kago sakamakon ban mamaki a tarihin wasannin Olympic.
Kafin gasar wasannin Olympic ta London, Koen ta yi iyakacin kokarin horon gudu kowace rana, wani lokaci kuma ta kasa kula da yaranta, shi ya sa wasu mutane sun kai mata suka cewa, ita ba mama mai kyau ba ce, amma Koen ta nace ga horonta a karkashin goyon bayan mijinta wanda shi ne malamin koyar da wasanta.
A gun zagaye na karshe na gasar gudun mita 100 na mata, Koen ta samu zama ta farko da dakika 11 da 9, alkalin wasa ya kiranta 'matar aure wadda ta tashi sama wato wadda ta fi saurin gudu'.
A gun gasar gudun tsallake shinge na mita 80 na mata, Koen ta ji dan tsoro har ba ta ji muryar bindigar ba da umurnin fara gudu ba, sai ta tashi bayan sauran 'yan wasa, amma ta zarce su, ta isa wurin karshe tare da wata 'yar wasa daga Ingila. To, wace ce ta samu zama ta farko? Ana jiran sakamako, a karshe dai, alkalin wasa ya sanar da cewa, Koen ta zama zakara.
Ya zuwa wannan lokaci, Koen ta riga ta samu lambobin zinariya biyu, kila ne ta gaji sosai, sai ta tsai da cewa, za ta janye jiki daga gasanni domin kallon yaranta. Mijinta ya yi kokarin shawo kanta ya ce, "A kullum kina girmamawa jarumi Jesse Owens wanda ya samu lambabin zinariya hudu a gun gasar wasannin Olympic ta Berlin, yanzu kin samu izni, me ya sa ba ki ci gaba da yin kokari ba?" Da haka, Koen ta ci gaba, kuma ta shiga gasar gudun ba da sanda tsakanin 'yan wasa mata hudu na mita 400 da gasar gudun mita 200 na mata, ta kara samun lambobin zinariya biyu. (Jamila Zhou)
Saboda babban sakamakon da Koen ta samu, ana mayar da gasar wasannin Olympic ta London gasar wasannin Olympic ta Koen, abun ban mamaki shi ne bayan Koen ta koma kasarta, ta tarar da cewa, yayin da take shiga gasar wasannin Olympic ta London, ta riga ta sami ciki.
|