Masu sauraro, a halin da ake ciki yanzu, gasar cin kofin duniya ta wasan kwallon kafa ta shekarar 2010 tana kusantowa sannu a hankali, mutanen kasar Afirka ta kudu wato kasar dake shirya daukar nauyin gasar suna kara sha'awarsu ta wasan kwallon kafa a kwana a tashi. Musamman ma samarin kasar Afirka ta kudu wadanda suka fi sha'awar wasan suna sanya matukar kokari domin nuna karfinsu a yayin gasar cin kofin duniya. A sanadin haka, wasu hanyoyin musamman na horaswa sun fito, alal misali, 'yan wasa sun hada hanyar horaswa ta wasan kwallon kafa da atisayen rawar ballet tare, kuma sun riga sun samu sakamako na musamman.
A cikin zaman rayuwarmu, wasan kwallon kafa da rawar ballet sun yi bambanta sosai tsakaninsu, kuma bayan da kwararru kan ilmin wasannin motsa jiki suka yi nazari game da fasahar wasan kwallon kafa ta shahararren 'dan wasa Diego Maradona na kasar Argentina, sun tarar da cewa, siffar motsin jikinsa a yayin wasan kwallon kafa ta yi kama da motsin rawar ballet ta gargajiya. Saboda haka, daga shekarar bara wato kafin shekara daya, an shirya kwas na atisayen rawar ballet musamman domin 'yan wasan kwallon kafa a kwalejin yin cudanya tsakanin wasan motsa jiki da fasaha ta kasar Afirka ta kudu. Daga nan, ana fatan 'yan wasan kwallon kafa wadanda ke samun horaswa a nan za su kara kyautata fasahar wasansu kamar yadda Maradona ya yi.
Dirk Badenhorst, mai kula da kwas na rawar ballet a kwalejin ya yi mana bayani cewa, kafin shekara daya, wato yayin da aka kafa wani sabon sansanin horaswa a wani wurin dake tsakanin birnin Johannesburg da birnin Pretoria, sun fara shigar da fasahar rawar ballet a cikin horaswar wasan kwallon kafa, kawo yanzu, sun riga sun samu sakamako mai faranta ran mutane. Badenhorst ya ce, ana iya yin amfani da wasu fasahohin rawar ballet a yayin wasan kwallon kafa, wato fasahar rawar ballet tana taimakawa aikin horaswar wasan kwallon kafa. Alal misali, 'yan wasa suna iya kara kyautata hanyar sarrafa jikinsu musamman ma kafarsu bayan da suka yi atisayen rawar ballet.
Amma, tun farkon da aka fara aikin, da kyar aka shawo kan 'yan wasa da su shiga ajin horas da rawa, kuma wasu 'yan wasa ba su so su sa tufafin rawar ballet ba, har sun kyautata tunani cewa, namiji ya yi rawa abin dariya ne. Amma bayan da suka ga amfanin rawa ga wasansu, wato bayan da suka samu sakamako a bayyane, ba ma kawai sun fara mai da hankali kan atisayen rawar ballet ba, har ma sun fara yin gasa tsakaninsu. Yanzu dai, matsayinsu na rawar ballet ya riga ya daga cikin sauri, ana iya cewa, 'yan wasa sun riga sun fara fahimtar fasahar rawar ballet.
Yanzu, dukkan 'yan wasan kwallon kafa na kasar Afrika ta kudu suna karban horaswar rawar ballet a kwalejin, ban da wannan kuma, wasu 'yan wasa samari da suka zo daga sauran kasashen Afirka kamarsu kasar Botswana da ta Zambia da ta Kenya da sauransu su ma sun je kwalejin domin samun horo na rawar ballet tare da wasan kwallon kafa.
Amm kudin karatu a kwalejin ya yi yawa, shi ya sa wasu yaran da suka zo daga gidajen dake fama da talauci ba su iya shiga kwalejin domin samun horaswa ba. A sanadin haka, kwalejin ta tsai da cewa, za ta ba da izni ga wadannan yara don su samu shiga ba tare da biyan kudi ba.
Botshelo Madumo yana da shekaru 14 da haihuwa kacal, yana sha'awar wasan kwallon kafa sosai, amma ba shi da isasshen kudin shiga wannan kwalejin, don haka kwalejin ta samar masa iznin karatu ba tare da karbar kudi ba, Maduma ya yi farin ciki kwarai gaske, yanzu yana karatu a kwalejin kuma yana jin dadin horaswar wasan kwallon kafa tare da rawar ballet. (Jamila Zhou)
|