Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-04-28 17:19:46    
Rukunin farko na jiragen ruwan soja masu ba da kariya ga zirga-zirgar jiragen ruwa na kasar Sin sun dawo Sanya na kasar Sin

cri

Cikin kwanaki 124 a jere na yin tafiye-tafiye cikin ruwan teku, rukunin farko na jiragen ruwan soja masu ba da kariya ga zirga-zirgar jiragen ruwa na kasar Sin masu sunayen"Wuhan" da "Haikou" kuma masu daukar makamai masu linzami sun dawo birnin Sanya na lardin Hainan a ranar 28 da safe ga wannan wata da karfe 9 da rabi, wannan ya bayyana cewa, sojojin ruwa na kasar Sin sun sami cikakiyyar nasara wajen aiwatar da dawainiyarsu ta ba da kariya ga zirga-zirgar jiragen ruwa a matakin farko a Somaliya da tekun Aden.

A ranar 28 ga wannan wata da safe da karfe 9 da rabi, rukunin farko na jiragen ruwan soja na kasar Sin masu ba da kariya ga zirga-zirgar jiragen ruwan teku masu sunayen "Wuhan" da "Haikou" kuma masu daukar makamai masu linzami sun shiga tashar ruwa, sai aka soma gaggarumin bikin maraba da su a tashar ruwa na wata rundunar soja da ke jibge a birnin Sanya .

A gun bikin, mataimakin ministan harkokin waje na kasar Sin Li Hui ya bayyana cewa, rukunin farko na jiragen ruwan teku masu ba da kariya sun kammala dawainiyarsu ta ba da kariya tare da cikakiyyar nasara , wannan na da  ma'ana mai muhimmanci ga kare moriyar kasa bisa manyan tsare-tsare da kara daga karfin kasa a dukkan fannoni da hakikanin karfi na rundunar soja da kara daga halin karamci na al'ummar kasar Sin da kafa alamar babbar kasa da ke daukar nauyi bisa wuyanta. Li Hui ya bayyana cewa, a ruwan teku da ke nesa sosai da kasar mahaifa, dukkan sojoji da hafshoshi sun yi yake-yake cikin jarumtaka, kuma sun sadaukar da ransu ba tare da kafa sharadi ba, kuma sun cin ma burin kammala dawainiyarsu da kuma cim ma hakkin da aka dora musu tare da kawar da wahalhalu da yawa, sun ba da kariya ga rukunoni fiye da 40 na jiragen ruwan teku, sa'anan kuma sun yi ma'amalar sada zumunta sosai da rukunonin jiragen ruwa na sauran kasashe.

Rukunin farko na jiragen ruwan soja masu ba da kariya ga zirga-zirgar jiragen ruwa sun tashi a ranar 26 ga watan Disamba na shekarar da ta shige , kuma sun yi ayyukansu a teku na Aden da Somaliya. A cikin watanni 4 ko fiye, sun yi tafiye-tafiye da nmi 33000, sun ba da kariya ga jiragen ruwa 212 na rukunoni 41, kuma sun ceci jiragen ruwa uku da suka sha harin da aka kai musu, sa'anan kuma sun karya matsayin bajinta na yawan tafiye-tafiye da lokuta a cikin teku.

Janar Li Jinai, direktan ofishin siyasa na rundunar sojan kasar Sin kuma mamban kwamitin soja na tsakiya na kasar Sin ya isar da gaisuwa da shugaban kwamitin soja na tsakiya na kasar Sin Hu Jintao ya yi wa sojoji da hafshoshi na jiragen ruwan soja masu ba da kariya cikin aminci. Ya bayyana cewa, wannan karo na farko ne da jiragen ruwan soja na kasar Sin suka tafi kasashen waje don kare moriyar kasa bisa manyan tsare-tsare, kuma karo na farko ne da suka yi aikin jin kai a kasashen waje, wannan na da ma'ana mai muhimmanci a tarihin raya ayyukan sojojin ruwa na kasar Sin.

Janar Du Jingchen , mai ba da jagoranci na rukunin ya gaya wa manema labaru cewa, rukunin ya kao abubuwa da yawa, na farko, shirya rundunonin sojoji iri iri na jiragen ruwan teku da yawa don kaddamar da ayyuka a kasashen waje da kuma kare moriyar kasa bisa manyan tsare-tsare; na biyu, karo na farko ne suka aiwatar da ayyukansu ba tare da yada zango a tashoshin ruwa ba, na uku, karo na farko ne suka aiwatar da dawainiyarsu a teku tare da rundunonin soja na kasashen waje da yawa a cikin teku, kuma suka yi ma'amala da yin hadin guiwar samar wa juna labarai; na hudu, karo na farko ne suka ba da guzuri da kayayyaki a yankin ruwa da ba su san shi sosai ba, kuma suka sami fasahohi da yawa.(Halima)