Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-04-27 17:56:24    
Sauye-sauyen zaman rayuwar mazauna jihar Tibet a cikin shekaru 50 da suka gabata

cri

Kafin kaddamar da gyare-gyare ta hanyar dimokuradiyya a shekara ta 1959 a jihar, tsohuwar jihar Tibet tana karkashin tsarin bayi manoma. Tsohuwa So Que Chol Gar wadda aka haife ta a shekara ta 1946 a yankin arewacin jihar Tibet, ta sha wahala sosai har na tsawon shekaru 13 sakamakon wannan mummunan tsari. Tun lokacin da shekarunta suka kai 8 da haihuwa, So Que Chol Gar ta fara bautawa iyayen gijin bayi a fannin kiwon dabbobi. Kullum iyayen gijin bayi su kan doddoke ta su kuma zazzage ta da azabtar da ita. Har ila yau kuma, a shekara ta 1953, an yi girgizar kasa a yankin ciyayi dake arewacin jihar Tibet. Duk wadannan munanan al'amura sun kawo babbar illa ga So Que Chol Gar a lokacin kuruciyarta, inda ta bayyana cewa: "An yi girgizar kasa a garinmu a shekara ta 1953, wadda ta kara tsunduma manoma da makiyaya cikin mawuyacin hali. Amma a wancan lokaci, ba ma kawai tsohuwar gwamnatin wurin ba ta rage yawan harajin da ta buga kan manoma da makiyaya ba, har ma ta cigaba da kwace dukiyoyinmu."

A jihar Tibet ta tsohun zamani, jami'ai, da attajirai, gami da manyan mabiya addinin Buddah, mutane ne wadanda suka mallaki ikon musamman a fannin siyasa da tattalin arziki. Amma bayi manoma masu tarin yawa wadanda suke bautawa iyayen gijin bayi sun sha wahala sosai. Wani manazarci mai suna Kelzang Yeshe na cibiyar nazarin ilimin zaman rayuwar jama'a ta jihar Tibet mai cin gashin kanta ta kasar Sin ya ce: "Miliyoyin bayi manoma sun shafe shekara da shekaru suna bautawa iyayen gijinsu, wadanda ake wulakantawa yadda aka ga dama, kuma ba'a mayar da su a matsayin 'yan Adam ba. Kafin kaddamar da gyare-gyare ta hanyar dimokuradiyya a jihar Tibet, mabiya addinin Buddah, da attajirai da yawansu bai fi kashi 5 bisa dari ba sun mallake dukkanin albarkatun kasa da Allah ya horewa jihar, amma sauran jama'a sun kasance marasa abin hannunsu."

Masu saurare, kafa Jamhuriyar Jama'ar kasar Sin a shekara ta 1949 ya bude wani sabon babi ga zaman rayuwar mazauna jihar Tibet. A ranar 23 ga watan Mayu na shekara ta 1951, gwamnatin tsakiya ta kasar Sin ta rattaba hannu tare da hukumar jihar Tibet ta lokacin akan yarjejeniyar 'yantar da jihar Tibet cikin lumana. Bisa ga la'akari da tarihin jihar da hakikanin halin da take ciki, yarjejeniyar ta yi taka-tsantsan wajen kaddamar da gyare-gyare a jihar.

Amma a wancan lokaci, akwai mutanen dake mulkin jihar Tibet wadanda suka nuna adawa da gudanar da gyare-gyare a jihar, a wani kokarinsu na aiwatar da tsarin bayi manoma har abada. A ranar 10 ga watan Maris na shekara ta 1959, irin wadannan mutane sun gama baki tare da 'yan a-ware daga kasashen ketare domin yin bore, a wani yunkurin balle jihar Tibet daga kasar Sin. Don kiyaye cikakken yankin kasa da babbar moriyar jama'ar jihar Tibet, gwamnatin kasar Sin ta dauki kwararan matakai ba tare da wata-wata ba, har ta kwantar da tarzoma tare da jama'ar wurin, da fara yin gyare-gyare ta hanyar dimokuradiyya a jihar. Manazarci Kelzang Yeshe ya cigaba da cewa: "Gwamnatin tsakiya ta kasar Sin ta fito da manufar kwantar da tarzoma yayin da ake yin gyare-gyare ta hanyar dimokuradiyya, wato da farko a yi gyare-gyare a wuraren da suke fama da tashe-tashen hankula. Sa'annan kuma ana aiwatar da tsarin tafiyar da mulki irin wanda ba ruwansa da addini sau da kafa, da yin kokarin yaki da iyayen gijin bayi da suka tada zaune-tsaye, da rarraba dukiyoyinsu ga dimbin bayi manoma."

Gyare-gyaren da aka gudanar ta hanyar dimokuradiyya sun 'yantar da miliyoyin bayi manoma, da ba su karin 'yancin kai. Sakamakon taimako daga gwamnati, a shekara ta 1959, So Que Chol Gar, mai shekaru 13 da haihuwa, ta sami damar shiga makarantar firamare. So Que Chol Gar ta bayyana cewa: "A shekara ta 1959, sojojin 'yantar da jama'ar kasar Sin wadanda suka kwantar da tarzoma da yin gyare-gyare a garinmu sun karbe ni, daga baya kuma sun aike da ni zuwa birnin Lhasa don yin karatu. Kamar sauran yaran 'yantattun bayi manoma, na shiga cikin makaranta. Bayan da na kammala karatu a makarantar, na fara aiki, har na zama daya daga cikin shugabannin wata jami'a ta zamani."

A halin yanzu, tsohuwa So Que Chol Gar ta riga ta yi ritaya, tana jin dadin zaman rayuwa tare da 'ya'yanta.