Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-04-27 17:55:04    
Kamfanoni masu zaman kansu da suka bulla daga birnin Wenzhou

cri
Yau da shekaru 30 da suka gabata, an soma aiwatar da manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje a kasar Sin. Sakamakon haka, tsarin tattalin arziki mai zaman kansa ya soma kafuwa, har ma ya samu cigaba cikin sauri. Yanzu kamfanoni masu zaman kansu sun riga sun zama wani muhimmin karfi a fannin tattalin arzikin kasar Sin. A cikin shirinmu na yau, za mu gabatar muku da wani bayani kan yadda tsarin tattalin arziki mai zaman kansa yake bunkasa a birnin Wenzhou, inda aka soma samun kamfanoni masu zaman kansu a kasar Sin.

A shekarar 1979, yarinya Zhang Huamei, mai shekaru 19 da haihuwa a waccan shekara wadda ita da iyalanta suka yi fama da talauci ta soma yin sana'a da kanta. Ba zato ba tsammani ta samu takardar farko ta yin kasuwanci da ake bayar wa wadanda suke tafiyar da harkokin tattalin arziki da kansu. Madam Zhang Huamei ta ce, "Na yi farin ciki lokacin da na samu wannan takarda. Wannan takardar yin kasuwanci ta nuna amincewa da aikina. Na iya yin kasuwanci kamar yadda ya kamata."

Kafin madam Zhang Huamei ta samu wannan takardar yin kasuwanci, mutanen birnin Wenzhou sun riga sun soma bude kananan kantunansu domin sayar da wasu kayayyakin masarufi. Amma gwamnatin kasar Sin ta wancan lokaci ta hana a raya tattalin arziki mai zaman kansa. Lokacin da aka soma yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje, ko da yake an soma bunkasa tsarin tattalin arziki mai zaman kansa, amma wadanda suke kasuwanci ba kallonsu da mutunci. Madam Zhang Huamei ta ce, "Mutane da yawa sun fi son samun wani gurbin aikin yi a cikin masana'anta ko wani kamfani mallakar gwamnati. Amma ni wata 'yar kasuwa ce kawai, ba wanda yake girmama ni."

Bayan da ta samu takardar yin kasuwanci, Zhang Huamei ta yi amfani da kudin Sin yuan dari 1 da 50 ta soma yin kasuwanci cikin mawuyacin hali. Ya zuwa shekara ta 2007, Zhang Huamei ta kafa wani kamfanin cinikin maballi da ke da jari kudin Sin yuan dubu dari 5.

Akwai kananan kamfanoni da yawa da suka kasance kamar kamfanin da Zhang Huamei ta kafa a birnin Wenzhou. Yanzu, yawan irin wadannan kamfanoni masu zaman kansu ya kai fiye da dubu 140, wato ya kai kashi 99.5 cikin kashi dari na jimillar kamfanonin birnin Wenzhou. Haka kuma, yawan kudaden masana'antu da suke samarwa ya kai kashi 95.5 cikin kashi dari. Har ma ana iya samun kananan kayayyakin masana'antu da aka yi a birnin Wenzhou a kusan dukkan kasuwannin kasar Sin.

Mr. Zhu Xianliang, jagoran birnin Wenzhou yana ganin cewa, dalilin da ya sa aka samu cigaban tattalin arziki mai zaman kansa a birnin Wenzhou shi ne hakikanin halin da ake ciki a birnin Wenzhou a fannin samun bunkasa. Mr. Zhu ya ce, "kafin a soma aiwatar da manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje, halin da ake ciki a birnin Wenzhou a fannin neman cigaba ba shi da kyau. Birnin Wenzhou ba shi da albarkatun halittu, ayyukan yau da kullum ma sun yi koma baya. Kuma babu isassun gonaki domin renon mutane, har ma ba a iya samar da isassun guraban aikin yi ga 'yan kwadago ba. Bunkasa tattalin arziki mai zaman kansa hanya ce mafi muhimmanci kuma mafi amfani wajen fama da talauci da kuma neman cigaban yankuna daban daban cikin daidaito."

Kowa yana son samun arziki. Bisa goyon bayan da gwamnatin birnin Wenzhou ta nuna a fannin manufofi, mutanen Wenzhou sun soma yin kasuwanci domin neman arziki. Mr. Ma Jinlong, shehun malami na jami'ar Wenzhou yana ganin cewa, mutanen Wenzhou sun yi kokarin neman hanyoyin bunkasa tattalin arziki. Sakamakon haka, sun kirkiro wani salon neman cigaba, wato "salon neman cigaba na Wenzhou". Mr. Ma ya ce, "A lokacin da aka soma yin gyare-gyare, a sana'o'in da kamfanoni da masana'antu masu zaman kansu suka iya shiga, an ga masana'antu masu zaman kansu sun zama muhimmin karfi a kasuwa. Birnin Wenzhou ya soma tsara sabbin tsare-tsare domin sa kaimi wajen raya masana'antu masu zaman kansu bisa tsarin kasuwanci."

Sakamakon haka, sana'o'i iri daban daban wadanda suke amfani da 'yan kwadago da yawa sun samu bunkasa cikin sauri a birnin Wenzhou. Alal misali, sana'ar yin takalma ta zama sana'ar da ta fi jawo masu zuba jari.

Amma, lokacin da ake neman samun bunkasa, farashin 'yan kwadago da sauran kudaden da aka kashe domin 'yan kwadago suna ta karuwa. Masana'antun Wenzhou sun soma daidaita tsarin sana'o'insu, kuma sun soma kara mai da hankali kan fasahohin da suke amfani da su a cikin kayayyakinsu da karin darajar kayayyakinsu.

Rukunin Kangnai wani muhimmin kamfani mai zaman kansa ne da ke yin takalma wanda aka kafa shi a shekara ta 1980. Mr. Zhou Jinmiao, mataimakin babban direktan rukunin Kangnai yana ganin cewa, kokarin kiyaye tambari da kirkiro sabbin fasahohi sun zama muhimman dalilai wajen cigaban rukunin Kangnai. Mr. Zhou ya ce, "Rukunin Kangnai ya shigo da sabbin injunan zamani da fasahohin zamani daga kasashen waje a gaba da takwarorinsa a kasar Sin. Sabo da haka, ya zama wani kamfanin da ke yin nazarin yin takalma mai inganci a kan gaba da takwarorinsa."

Bugu da kari kuma, rukunin Kangnai ya mai da hankali kan daga darajar kayayyakinsu, kuma ya bude kantunan sayar da takalmoma musamman a kasashen waje domin kokarin neman cigaba. Mr. Zhou Jinmiao ya ce, "Farashin takalma mafi kyau da muke fitarwa ya kai fiye da dalar Amurka 70. Wannan ya yi tsada. Matsakaicin farashin takalma na kasar Italiya shi ne ya kai kimanin dalar Amurka 20. Kuma matsakaicin farashin takalma da ake fitarwa daga kasar Sin zuwa kasuwannin ketare ya kai kimanin dalar Amurka 7 kawai."

A lokacin da ake tinkarar matsalar hada-hadar kudi ta duniya a shekara ta 2008, sanannun kamfanonin yin takalma na duniya sun rage farashin kayayyakinsu da ya kai kashi 30 cikin kashi dari bi da bi, amma yawan kudaden da kamfanin sayar da takalma na rukunin Kangnai da ke kasar Faransa ya samu ya karu da kashi 35 cikin kashi dari.

Rukunin Chint, wani kamfani mai zaman kansa na daban, ya zama sarkin samar da kayayyakin wutar lantarki a nan kasar Sin ta hanyar raya tamburi da kirkiro sabbin fasahohi. An kafa kamfanin Chint ne a shekarar 1984 da jarin kudin Sin yuan dubu 50 kawai. Amma ya zuwa yanzu ya riga ya zama wani kamfanin zamani wanda ke yin nazari da kirkiro sabbin fasahohin kayayyakin wutar lantarki. Yawan kudaden da ya samu ya kai kudin Sin yuan biliyan 20 bayan da ya sayar da kayayyakinsa a kowace shekara. Bisa fasahohin zamani da ya kirkiro da kansa, a shekara ta 2007, kamfanin Chint ya soma yin batir irin na yin amfani da makamashin hasken rana. Mr. Lin Kefu, mataimakin babban direktan rukunin Chint ya bayyana cewa, "Kayayyaki iri na yin amfani da makamashin hasken rana sun zama sabbin kayayyakin da kamfanin Chint ke samarwa. Bayan da ya soma sayar da irin wadannan kayayyaki a kasuwa tun daga shekara ta 2007, ana sayar da su kamar yadda ake fata. Yanzu muna nazarin sabon salon irin wadannan kayayyaki na yin amfani da makamashin hasken rana, wato kayayyaki ne da ke kiyaye ingancin muhalli. Muna ganin cewa, irin wadannan kayayyaki suna da makoma mai kyau."

Bayan da ta ga rukunin Kangnai da rukunin Chint suna samun bunkasa da kyau, madam Zhang Huamei tana da shirinta na bunkasa kamfaninta. Madam Zhang ta ce, "Ina fatan kamfanina zai samu bunkasa kamar yadda sauran kamfanoni masu zaman kansu na kasar Sin suke yi. Ina fatan kamfanina yana da tamburinsa mai suna 'Huamei'." (Sanusi Chen)