Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-04-27 17:53:35    
Wasu labarai dangane da kananan kabilun kasar Sin

cri

------ Kwanan baya, majalisar wakilan jama'ar jihar Tibet mai cin gashin kanta ta kasar Sin ta tsai da kudurin ware ranar 28 ga watan Maris na kowace shekara don ta zamanto ranar tunawa da 'yantar da miliyoyin bayi manoma na jihar Tibet, domin tunawa da muhimman gyare-gyare ta hanyar dimokuradiyya da aka gudanar a jihar shekaru 50 da suka gabata. Bangarori daban-daban na jihar sun nuna babban yabo ga wannan lamari.

Tsohuwa Eji mai shekaru 86 da haihuwa wadda ke zaune a garin Dargye na gundumar Dagze ta birnin Lhasa ta nuna yabo ga ware irin wannan rana, haka kuma ta bayyana fatanta ga matasa da kada su manta da tarihi.

A nata bangare, zaunanniyar memba ta musamman ta majalisar bada shawara kan harkokin siyasa ta jihar Tibet Madam Ramba Yangien Drolkar tana ganin cewa, ware ranar 28 ga watan Maris na kowace shekara don ta zamanto ranar tunawa da 'yantar da miliyoyin bayi manoma na jihar Tibet wata kyakkyawar manufa ce. Ta kuma cigaba da cewa, an samu manyan sauye-sauye a fannonin tattalin arziki da zaman rayuwar jama'a sakamakon gyare-gyaren da aka soma gudanarwa a shekaru 50 da suka gabata, jama'ar jihar kuma sun kara samun iko da 'yancin kai.

------ Bisa sabuwar kididdigar da aka bayar, an ce, a cikin shekaru 9 da suka gabata, gwamnatin tsakiya ta kasar Sin ta ware makudan kudaden da yawansu ya tasam ma Yuan biliyan daya, domin gina muhimman ayyukan samar da tsabtaccen ruwan sha da adadinsu ya kusa dubu 10 a jihar Tibet mai cin gashin kanta ta kasar Sin, ta yadda manoma da makiyaya da yawansu ya kai miliyan 1.44 a jihar za su samu tsabtaccen ruwan sha ba tare da matsala ba.

Shugaban sashen kula da harkokin ruwa na kauyuka na ma'aikatar harkokin ruwa ta kasar Sin Mista Wang Xiaodong ya nuna cewa, babban burin da gwamnatin kasar ke kokarin neman cimmawa shi ne, zuwa shekara mai kamawa, za'a daidaita matsalar karancin tsabtaccen ruwan sha da manoma da makiyaya a jihar Tibet suke fama da ita. A waje daya kuma, yawan mutanen da suke samun ruwan fanfo a yankunan ayyukan gona da makiyaya na jihar Tibet ya karu daga kashi 12 bisa dari na shekarar 2000 zuwa kashi 61 bisa dari na yanzu.