Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-04-27 16:41:50    
Masaniyar Sin ta kyautata zato ga makomar Afirka ta kudu bayan da Zuma ya ci babban zaben kasar

cri

A ran 25 ga wata da yamma, agogon wurin, gwamnatin Afirka ta kudu ta sanar da sakamakon babban zaben da aka gudanar a kasar, kuma bisa ga yadda aka sanar, jam'iyyar ANC da ke jan ragamar mulkin kasar ta sake cin zaben bisa gaggarumin rinjaye. Sakamakon haka dai, shugaban jam'iyyar, Jacob Zuma zai zama sabon shugaban kasar ba tare da wani cece-kuce ba. To, a yayin da tattalin arzikin duniya ke cikin tabarbarewa, ko Zuma zai canza manufar tattalin arzikin da aka tafiyar a kasar a da, kuma ko zai cika alkawuran da ya dauka a lokacin zaben, sa'an nan, ko jama'a na cike da imani game da mulkin da zai tafiyar? A game da tambayoyin, wakilinmu ya yi hira da madam Yang Lihua, tsohuwar mataimakiyar shugaban sashen nazarin harkokin yammacin Asiya da na Afirka a cibiyar nazarin zaman al'umma ta kasar Sin, don ta amsa mana tambayoyin.

Gaba daya akwai jama'a miliyan 23 da suka kada kuri'ar zaben, kuma bisa sakamakon zaben da kwamitin zabe mai zaman kansa ya sanar a ran 25 ga wata, jam'iyyar ANC ta sami kuri'un da yawansu ya kai 65.9%, a yayin yawan kuri'un da jam'iyyar DA ta samu ya kai 16.7%. A game da wannan, Madam Yang Lihua tana ganin cewa, zaben ya kasance mai muhimmanci sosai. Ta ce,"Kafin zaben, sabo da an sami baraka cikin jam'iyyar ANC, kuma wadanda suka fice daga jam'iyyar sun kafa wata sabuwar jam'iyya. Sabo da haka, ko Afirka ta kudu za ta ci gaba da bin manufar gyare-gyaren tsarin mulki kamar yadda ta yi cikin shekaru 15 da suka wuce, kuma ko za a iya tabbatar da kwanciyar hankalin siyasa da tattalin arziki a kasar ya zama wata tambaya. Bisa ga yadda masu zabe suka yi kokarin shiga zaben, wadanda suka dau kashi 77% daga cikin jama'ar da suka yi rajistar shiga zaben, muna iya gane cewa, jama'a sun nuna kulawa sosai ga zaben, kuma suna sa ran ci gaba da tsarin dimokuradiyya da aka tsara, tare kuma da tabbatar da bunkasuwar harkokin siyasa da tattalin arziki cikin kwanciyar hankali."

Bayan haka, tattalin arzikin Afirka ta kudu na da tushe mai kyau, a cikin shekaru 15 da suka wuce, manufar tattalin arziki, musamman ma manufar kudi da take aiwatarta ta sami yabo daga gamayyar kasa da kasa. Duk da haka, kasar na fuskantar wasu dimbin matsaloli, ciki har da rashin aikin yi da karuwar matalauta. A game da wannan, madam Yang Lihua ta ce,"Ina ganin jam'iyyar ANC da ke karkashin jagorancin Zuma ba za ta yi manyan gyare-gyare ga manufar tattalin arzikin da aka aiwatar a da ba, kawai za ta kara karfin tabbatar da manufar. Hakan na iya daidaita matsalar talauci da rashin aikin yi yadda ya kamata. A cikin shekaru 15 da suka wuce, manufar juya tattalin arziki cikin kwanciyar hankali da kasar ta aiwatar, musamman ma manufar kudinta, ta sami yabo daga kasa da kasa, sabo da haka, matsalar kudi ta duniya ba ta haddasa manyan illoli ga tattalin arzikin kasar ba. Ina ganin jam'iyyar ANC za ta ci gaba da manufar, kuma za ta kara mai da hankali a kan daidaita matsalar talauci da kara samar da aikin yi da kuma ba da tabbaci ga masu fama da talauci."

A lokacin da Zuma ke tsayawa takarar zaben, ya taba daukar jerin alkawura, ciki har da kyautata ayyukan bauta wa al'umma da kara musu kudin shiga da dai sauransu. A game da wannan, Madam Yang Lihua na ganin cewa, al'umma na da imani ga alkawuran. Ta ce,"A ganina, jam'iyyar ANC da ke karkashin jagorancin Zuma za ta fi yin kokarin aiwatar da shirye-shirye da manufofin da gwamnati ta tsara game da bunkasuwar kasar. Wani kiran da ya yi shi ne hukunta jami'an da ba su gudanar da ayyuka tsakaninsu da Allah ba. Ban da wannan, Zuma na da walwala, shi ya sa jama'a na da imani gare shi wajen gudanar da harkokin mulki."(Lubabatu)