Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-04-21 15:55:08    
An yi zaman na 2 na majalisar wakilan jama'ar jihar Tibet mai cin gashin kanta a karo na 9

cri
An yi zaman na 2 na majalisar wakilan jama'ar jihar Tibet mai cin gashin kanta a karo na 9, inda aka amince da ware ranar 28 ga watan Maris na kowace shekara don ta zamo ranar tunawa da 'yantar da miliyoyin bayi manoma a jihar.

A wajen taron manema labaru da aka shirya bayan taron, mataimakin darektan zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar jihar Tibet Mista Gama ya nuna cewa, a cikin shekaru 50 da suka shige, jihar Tibet ta samu manyan sauye-sauye a fannoni da dama, ciki har da harkokin siyasa, da tattalin arziki, gami da al'adu da dai sauran makamantansu. Amma akwai wasu tsirarun mutane 'yan a-ware wadanda suke kulla makarkashiryar kawo baraka ga jihar Tibet, da yin yunkuri wajen kawo tsaiko ga bunkasuwar jihar Tibet. Don haka, mutanen jihar suna fatan ware ranar tunawa da 'yantar da miliyoyin bayi manoma, ta yadda za su cigaba da kishin kasar Sin da sabuwar jihar Tibet.

Yanzu a jihar Tibet, akwai manoma da makiyaya da adadinsu ya kai dubu 850 wadanda suka samu tsabtaccen ruwan sha. Kwanan baya, shugaban hukumar kula da harkokin ruwa ta jihar Tibet Baima Wangdui ya bayyana cewa, a cikin nan da shekaru 3 masu zuwa, za'a dukufa ka'in da na'in wajen daidaita matsalar karancin tsabtaccen ruwan sha a yankunan gona da makiyaya a jihar.

Masu saurare, rashin isasshen tsabtaccen ruwan sha a jihar Tibet mai cin gashin kanta ta kasar Sin, babbar matsala ce da manoma da makiyaya na wurin suka dade suna fama da ita. Saboda haka, hukumar jihar Tibet ta tsara wani shiri na cewa, za'a gano bakin zaren daidaita matsalar karancin tsabtaccen ruwan sha da manoma da makiyaya da yawansu ya zarce miliyan 1.2 a yankin suke fama da ita daga shekara ta 2006 zuwa shekara ta 2010.

To, masu saurare, laifin dadi Hausawa kan ce karewa, iyakacin shirinmu na yau na "Kananan kabilun kasar Sin" ke nan daga nan sashen Hausa na rediyon kasar Sin. Murtala ne ke cewa a kasance lafiya.