Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-04-15 17:20:24    
Jihar Guangxi tana raya masana'antu ta hanyar kirkiro sabbin fasahohi

cri
A cikin shekaru 50 da suka gabata bayan da aka kafa jihar Guangxi ta kabilar Zhuang mai cin gashin kanta, an soma kafa masana'antu, kuma an raya su cikin sauri. Yanzu, ba ma kawai masana'antun jihar Guangxi suna kera kayayyaki ba, har ma su kan mai da hankali kan kirkiro sabbin fasahohin zamani na kera sabbin kayayyaki. Yanzu ga wani bayani, inda aka bayyana yadda wasu masana'antun jihar Guangxi suke kirkiro sabbin fasahohin zamani da kansu.

Lokacin da ake zantawa kan masana'antun jihar Guangxi, tabbas ba za a iya mantawa da kamfanin kera injunan da ke birnin Liuzhou ba wanda yake gaban kusan dukkan kamfanonin kera injuna na duk kasar Sin. A cikin shekaru 48 da suka gabata, an kera ire-iren injunan da ake hada su na farko sau da yawa a wannan kamfani. Mr. Zhang Erping, wanda ke shugabantar hukumar yin nazarin sabbin fasahohin zamani a kamfanin ya gaya wa wakilinmu cewa, "Injin hako tabo da muka kera yana aiki daidai cikin sauki kamar yadda wani injin robot ke yi."

Mr. Zhang Erping ya fadi haka ne cike da alfahari. Lokacin da wakilinmu yake ziyara a kamfanin kera injuna na Liuzhou, ana gasar sabbin manyan injuna a fannin fasahar aikin injiniya. Ko da yake wadannan injuna suna da girma sosai, amma ana nuna mamaki sosai ga abin da suke yi a gun gasar. Ba ma kawai sun iya hako tabo ba, har ma sun iya yin amfani da alkalamin gargajiya na kasar Sin da kidaya takardun kudi da kuma buga bakake.

Ba ma kawai kamfanin kera injunan injiniya na Liuzhou yana kan matsayin farko a cikin kamfanonin da suke kera injunan daukar kaya da na ayyukan injiniya ba, har ma yana sayar da kayayyakinsa a kasuwannin kasashe da yankuna fiye da 60 ta hanyar yin nazari da kirkiro sabbin fasahohin zamani da kansa. Mr. Huang Zhaohua, mataimakin babban direktan sashen kula da kasuwannin ketare a kamfanin kera injuna na Liuzhou ya ce, "Bisa kason da muka samu a kasuwa, mun riga mun zama wani kamfanin takara mai karfi a kasuwannin kasashen duniya. Alal misali, yawan injuna masu daukar kaya da muka sayar a kasuwar kasar Indiya ya kai fiye da kashi 60 cikin kashi dari bisa dukkan injuna masu daukar kaya da ake sayarwa a kasar, wato yawan injunan da muke sayarwa a kasar Indiya ya fi na kamfanin kere-kere na Caterpillar yawa. A waje daya kuma, muna matakin farko a kasuwannin kasashe masu arziki, kamar a yankunan nahiyar Amurka ta arewa. Amma muna da imani wajen samun nasara a kai a kai a wadannan yankuna. Bugu da kari kuma, yankunan Gabas ta tsakiya da na Afirka tamkar kasuwanninmu ne na gargajiya."

Kamfanin Caterpillar da Mr. Huang Zhaohua ya ambata a baya wani babban kamfani ne da ke cikin jerin kamfanoni mafi girma guda 500 a duniya. Yanzu wannan kamfani yana gaban sauran takwarorinsa a duk duniya a fannin samar da injunan da ake kerawa. Mr. Huang Zhaohua ya ce, kamfanin kera injunan da ake kerawa na Liuzhou ya zama wani muhimmin mai yin takara ga kamfanin Caterpillar, wannan abu ne da ba a taba ambata ba lokacin da aka kafa kamfanin kera injunan da ake kerawa na Liuzhou. A lokacin da kamfanin kera injunan da ake kerawa na Liuzhou yake soma neman cigaba, injiniyoyin kamfanin su kan yi nazari kan tsarin injunan da aka kera a kamfanin Caterpillar domin sanin yadda ake iya samar da injunan da ake kerawa na zamani. Sabo da haka, kamfanin Caterpillar ya kasance ga kamfanin kera injunan da ake kerawa na Liuzhou tamkar malaminsa.

Yanzu, yawan kudaden da kamfanin kera injunan da ake kerawa na Liuzhou ke zubawa kan yin nazari da kirkiro sabbin fasahohi ya kai kashi 4 cikin kashi dari bisa na jimillar kudaden da ya samu bayan da ya sayar da injuna a kasuwa. A da, yawan ma'aikatan hukumar yin nazari da kirkiro sabbin fasahohi bai kai guda 20 ba, amma yanzu kamfani yana da hukumomin yin nazari guda 18 tare da ma'aikata fiye da 500. Sakamakon haka, yawan injunan da kamfanin ke sayarwa a kowace shekara da kuma yawan kudaden da kamfanin yake samu a kasuwa dukkansu suna karuwa. Bisa kididdigar da aka yi, a cikin farkon watanni 9 na shekara ta 2008 da ta gabata, yawan injuna iri iri da kamfanin ya sayar ya kai fiye da dubu 32 da dari 5, yawan kudaden da kamfanin ya samu sakamakon sayar da injuna ya kai kudin Sin yuan biliyan 8. Game da jimillar kudaden da kamfanin ya samu a duk tsawon shekara ta 2008, Mr. Huang Zhaohua yana cike da imani, ya ce, "Muna takara da takwarorinmu a kasuwa bisa darajar injunanmu, ba bisa farashi ba. Yawan injunan da muke sayarwa a kasuwa ya karu da kashi 70 cikin kashi dari bisa na makamancin shekara ta 2007, kuma yawan kudaden da muke samu ya karu da kashi 90 cikin kashi dari."

Lokacin da wakilanmu suke neman labaru a jihar Guangxi, abubuwan da wakilanmu su kan gani ko suka saurara su ne "kirkiro sabbin fasahohi da kanmu". Kamar yadda kamfanin kera injunan da ake injiniya na Liuzhou yake yi, kamfanin samar da injunan motoci na Yuchai ya kuma samu kasuwa bisa sabbin fasahohin da ya kirkiro da kansa. Lokacin da ake gasar wasannin Olympic ta Beijng a shekara ta 2008, injuna 2000 da kamfanin Yuchai ya kera bisa ma'aunin mataki na IV na Turai sun zama tambari daya tak da wani kamfanin kasar Sin ya kera kuma sun zama injunan bus na gasar Olympic ta Beijing. Mr. Lin Zhiqiang, mataimakin shugaban cibiyar yin nazari ta kamfanin Yuchai ya ce, dalilin da ya sa kamfanin Yuchai ya samu nasara shi ne fasahohinsa suna gaba da takwarorinsa.

"A cikin 'yan shekarun da suka gabata, yawan kudaden da muka zuba domin yin nazari kan sabbin fasahohi ya kai kashi 3 cikin kashi dari bisa na jimillar kudaden da kamfanin ya samu bayan da ya sayar da kayayyakinsa a kasuwa, wato ya kai kudin Sin yuan kusan miliyan dari 3 a shekara ta 2007. Yanzu muna da ma'aikata 18 da suka samu digiri na 3 da suke aiki a cibiyar kirkiro sabbin fasahohin zamani. Yanzu ana bin ma'auni na mataki na III na Turai a kasar Sin, amma mun riga mun soma yin nazari kan yadda za mu iya yin amfani da ma'auni na mataki na VI a cikin injunanmu."

Sabo da kamfanin yana bin tunanin kirkiro sabbin fasahohi da kansa a kullum, kamfanin Yuchai, wato wata karamar masana'antar da wasu iyalai suka kafa a shekarar 1951, yanzu ya riga ya zama wani babban rukunin kamfanonin samar da injunan motoci da injunan da ake kerawa da kayayyakin gyara na mota da kayayyakin sinadari da motocin musamman da kuma sauran kayayyakin wutar lantarki. A shekara ta 2007, yawan manyan injunan da ake kerawa kawai da kamfanin ya sayar a kasuwa ya kai fiye da dubu 37 da dari 8. Mr. Qiu Ruixing, babban injiniya na kamfanin samar da injuna na rukunin Yuchai ya bayyana cewa, "Yanzu burinmu da muke kokarin cimmawa shi ne mu iya kirkiro sabbin kayayyaki domin maye tsoffin kayayyakinmu."

Jama'a masu sauraro, ba ma kawai ana samar da injuna a jihar Guangxi ba, har ma jihar Guangxi tana samar da sauran kayayyaki. Alal misali, jihar Guangxi tana arzikin kayayyakin yin maganin gargajiya na kasar Sin. Sabo da haka, mutanen jihar Guangxi sun yi amfani da irin wadannan kayayyaki sun yi man goge baki na samfurin Liangmianzhen. Yanzu wannan man goge baki ya riga ya zama tambarin man goge baki mafi suna a kasar Sin. Mr. Lin Zuanhuang wanda ke shugabantar kamfanin samar da man goge baki na samfurin Liangmianzhen ya bayyana cewa, lokacin da aka kafa kamfanin Liangmianzhen yau da shekaru 50 da suka gabata, ana harhada kayayyaki ne a cikin wasu kananan dakuna kawai, amma yanzu kamfanin ya riga ya zama wani babban kamfani mai hannun jari da ke da kadarorin samar da kayayyaki da yawansu ya kai fiye da kudin Sin yuan biliyan 4. Kamfanin Liangmianzhen ya samu wannan sakamako ne bisa sabbin fasahohin da ya kirkiro da kansa. Mr. Lin Zuanhuang ya bayyana cewa, "Yanzu kamfanin Liangmianzhen yana neman cigaba bisa ka'idoji biyu, wato kafa tambarin da ke nuna al'adun Sinawa, sannan muna kirkiro sabbin fasahohi da kanmu. Kamfanin Liangmianzhen ya samu cigaba ne bisa fasahohin yin amfani da maganin gargajiya na kasar Sin wajen yin man goge baki." (Sanusi Chen)