Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-04-15 08:48:47    
Kungiyar wasan kwallon ragar mata ta birnin Tianjin ta zama tambarin sana'a na birnin

cri

Kamar yadda kuka sani, kungiyar wasan kwallon ragar mata ta kasar Sin ta yi suna sosai a duniya, ta taba zama zakara a wasannin duniya sau biyar, ana iya cewa, a zukatun jama'ar kasar Sin, kungiyar wasan kwallon ragar mata ta kasar Sin tana da matsayi na musamman. Duk da haka, a birnin Tianjin dake arewacin kasar Sin, shi ma ya kasance da wata kungiyar wasan kwallon ragar mata, a cikin shekaru bakwai da suka wuce, 'yan wasan kungiyar sun samu damar zama zakarun babbar gasar wasan kwallon ragar mata ta kasar Sin sau shida, a zukatun mazauna birnin, kungiyar nan ita ma tana da matsayin musamman, 'yan wasan kungiyar suna samun karbuwa kwarai da gaske a birnin. A cikin shirinmu na yau, bari mu yi muku bayani kan wannan.

Birnin Tianjin daya ne daga cikin birane hudu masu cin gashin kansu na kasar Sin, kuma ya fi kusa da birnin Beijing. A ran 25 ga watan Disamba na shekarar 2008, an zabi birnin da ya zama birni mafi samar da jin dadin zaman rayuwa a kasar Sin. Amma, abu mafi faranta ran mazauna birnin Tianjin shi ne suna mallakar wata kungiyar wasan kwallon ragar mata wadda ta kan ci nasara a ko da yaushe. A yayin karawa ta karshe ta babbar gasar wasan kwallon ragar mata ta kasar Sin ta wannan shekarar da aka kawo karshenta kwanakin baya ba da dadewa ba, kungiyar birnin Tianjin ta lashe kungiyar birnin Shanghai ta sake zama zakara a wannan gasa, wannan a karo na shida ne da ta zama zakarar babbar gasar wasan kwallon ragar mata ta kasar Sin, ana iya cewa, kungiyar birnin Tianjin ta samu sakamakon da ba a taba ganin irinsa ba a tarihi.

Ko shakka babu, kungiyar wasan kwallon ragar mata ta birnin Tianjin tana da karfi, a ran 21 ga watan Maris na shekarar 2008, kungiyar Tianjin ta taba yin gaba da gaba da kungiyar kasar Amurka, a yayin gasar, kungiyar birnin Tianjin ta lashe kungiyar kasar Amurka da 3:0. Bayan watanni biyar, kungiyar kasar Amurka ta samu lambar azurfa a yayin gasar wasannin Olympic ta Beijing. Kan wannan batu, babban malamin horaswa na kungiyar wasan kwallon ragar mata ta birnin Tianjin Wang Baoquan ya kyautata tunani cewa, dalilin da ya sa kungiyar birnin Tianjin ta ci nasara shi ne 'yan wasan kungiyar suna sanya iyakacin kokarin neman samun damar zama zakarun gasa a ko da yaushe. Wang Baoquan ya ce:  "'Yan wasan kungiyarmu suna yin kokari tare domin neman samun damar zama zakaru, shi ya sa mu kan ci nasara a yayin gasa. "

Koda yake ba mai yiwuwa ba ne wata kungiyar wasa ta ci nasara a ko da yaushe, amma kungiyar wasan kwallon ragar mata ta birnin Tianjin ta samu dammar zama zakara a babbar gasar wasan kwallon ragar mata ta kasar Sin sau shida a cikin shekaru bakwai, ana iya cewa, kungiyar birnin Tianjin ta samu wani matsayin bajimta mai faranta ran mazauna birnin. A sanadin haka, mazauna birnin Tianjin suka fi sha'awar wasan kwallon raga, daga nan, kungiyar wasan kwallon ragar mata ta birnin Tianjin ta zama alamar birnin.

An kafa kungiyar wasan kwallon ragar mata ta birnin Tianjin ne a shekarar 1993, kawo yanzu, shekaru 16 sun wuce. A cikin wadannan shekaru 16, 'yan wasan kungiyar sun taba gamuwa da wahalhalu iri daban daban, amma haka bai kawo mugun tasiri ga imaninsu ba. A ko da yaushe, 'yan wasan kungiyar suna yin kokari. Babban malamin horaswa Wang Baoquan ya dauka cewa, nasarorin da suka samu sakamakon kokarin da suka yi ne. Ya ce:  "Muna yin kokari a ko ina kuma a ko da yaushe, in ba haka ba, ba za mu ci nasara ba."

Kungiyar birnin Tianjin ta taba samun damar zama zakara a babbar gasar wasan kwallon ragar mata ta kasar Sin sau shida a cikin shekaru bakwai, a sa'i daya kuma, ta taba samun iznin zama zakarar gasar cin kofin duk kasar Sin ta wasan kwallon raga da zakarar gasar wasannin duk kasar Sin. Ana iya cewa, kungiyar birnin Tianjin ta samu babban sakamako, shi ya sa babban malamin kungiyar Wang Baoquan ya kai matsayin koli a zukatun mazauna birnin.

An ce, "Muna ganin cewa, Wang Baoquan ya riga ya kai matsayin malami mai horaswa na kungiyar wasan kwallon ragar mata ta kasar Sin. Muna goyon bayansa a ko da yaushe."

'Yan wasan kungiyar wasan kwallon ragar mata ta birnin Tianjin su kan yi wasa a dakin wasannin jama'a na birnin, a cikin wannan daki, ana iya jin kuzari da goyon bayan da mazauna birnin ke nuna wa 'yan wasan. Kamar yadda kuka sani, mu kan mayar da wata fitacciyar kungiyar wasa a matsayin tambarin sana'a na wani birni. Lallai ana mayar da kungiyar wasan kwallon ragar mata ta birnin Tianjin a matsayin tambarin sana'a na birnin. Yanzu, ba ma kawai kungiyar wasan kwallon ragar mata ta birnin Tianjin ta zama tambarin sana'a na birnin ba, har ta riga ta zama alamar birnin. Kuma, mazauna birnin Tianjin suna mayar da 'yan wasan kungiyar tamkar 'ya'yansu.

Hali mai karfi na 'yan wasan kungiyar wasan kwallon ragar mata ta birnin Tianjin shi ma ya sa kaimi ga bunkasuwar birnin. Halin kungiyar wasan kwallon ragar mata ta birnin Tianjin shi ma ya zama alamar birnin. A shekarar bara wato shekarar 2008, mazauna birnin da suka zo daga fannoni daban daban sun fara koyon 'halin kungiyar wasan kwallon ragar mata ta birnin Tianjin', alal misali, daliban makaranta da jami'an hukumar kwastan da masu jiyyan asibiti da malaman makaranta da ma'aikatan sauran sana'o'i suna yin amfani da halin nan wato 'halin kungiyar wasan kwallon ragar mata ta birnin Tianjin' a cikin aikinsu da zaman rayuwarsu.

Yanzu, wasu tsoffin 'yan wasa na kungiyar Tianjin za su yi ritaya, saboda haka, wasu sabbin 'yan wasa za su shiga kungiyar, a sanadin haka, ana bukatar lokaci domin yin gyare-gyare da kuma samun kyautatuwa. Game da wannan, babban malami mai horaswa na kungiyar Wang Baoquan ya karfafa magana cewa, za a ciyar da 'halin kungiyar wasan kwallon ragar mata ta birnin Tianjin' gaba har abada. Ya ce,  "Tabbas ne ba za mu canja wannan hali ba, za mu yi matukar kokari a ko da yaushe kamar yadda muka yi a da, kuma za mu mai da hankali kan kowace gasar da za mu shiga."

Lallai 'halin kungiyar wasan kwallon ragar mata ta birnin Tianjin' yana da muhimmanci sosai da sosai, kungiyar birnin Tianjin za ta ci gaba da zama tambarin sana'a na birnin bisa kokarinsu, kuma za ta ci gaba da zama kungiyar zakara a zukatun masu sha'awar wasan kwallon raga.(Jamila Zhou)