Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-04-10 15:46:58    
Huldar dake tsakanin kasar Sin da kasar Mozambique ta samu cigaba yadda ya kamata

cri

Huldar abokantaka dake tsakanin kasar Sin da kasar Mozambique ta shiga sabon zamani na samun bunkasuwa yadda ya kamata. A cikin shekaru biyu da suka gabata, an kara yin musanyar ra'ayi tsakanin shugabannin kasashen biyu da kuma mutanensu, kuma an kara samun sakamako ta hanyar yin hadin gwiwa a fannin tattalin arziki da cinikayya, yawan kudaden da suka samu ya karu cikin sauri kuma ya kai sabon matsayi a cikin tarihi, sakamakon da aka samu a gun taron koli na Beijing na dandalin tattaunawa tsakanin Sin da Afrika ya kawo moriya da yawa ga jama'ar kasashen biyu. Tian Guangfeng, jakadan kasar Sin dake kasar Mozambique ya yi sharhi kan huldar tsakanin kasashen biyu kamar haka a yayin da yake ganawa da 'dan jaridar kamfannin dillancin labaru na Xinhua.

Mr. Tian Guangfeng ya ce, a cikin shekarar bara kawai, kasar Mozambique ta tura tawagogin gwamnati 13 na ministoci zuwa kasar Sin don yin mu'amala da hadin gwiwa da kasar Sin a fannonin siyasa da tattalin arziki da zaman al'umma da kuma al'adu da dai sauransu, inda suka fahimci sakamakon da Sin ta samu wajen kula da harkokin jama'a da kafa yaukunan musamman na raya tattalin arziki. Sannan kuma, kasar Sin ma ta tura kungiyoyin wakilan gwamnati fiye da goma zuwa kasar Mozambique don tabbatar da manufofin da aka tsara a gun taron koli na Beijing na dandalin tattaunawa tsakanin Sin da Afrika da kuma sakamakon da aka samu wajen ziyarar da shugaba Hu Jintao ya yi a kasar Mozambique a shekarar 2007, haka kuma, kungiyoyin wakilan kasar Sin sun yi kokarin neman karin damar yin hadin gwiwa, sannan kuma sun samu sakamakon a-zo-a-gani.

Mr. Tian ya bayyana cewa, huldar hadin gwiwa tsakanin Sin da Mozambique wajen tattalin arziki da cinikayya ta samu bunkasuwa kuma ta kai wani sabon matsayi. A shekarar 2008, yawan kudaden da aka samu wajen yin ciniki a tsakanin bangarorin biyu ya kai dalar Amurka miliyan 423, wanda ya karu da kashi 48.7 cikin dari bisa makamancin lokaci na shekarar 2007, daga cikinsu, yawan kayayyakin da Sin ta fitar zuwa Mozambique ya kai dalar Amurka miliyan 288, kuma yawan kayayyakin da Sin ta shigo daga Mozambique ya kai dalar Amurka miliyan 135.

Bugu da kari, Mr. Tian Guangfeng ya ce, ayyukan da aka tabbatar a gun taron koli na Beijing na dandalin tattaunawa tsakanin Sin da Afrika da kuma a lokacin ziyarar da shugaba Hu Jintao ya yi a shekarar 2007 sun samu babban cigaba. Gine-ginen da kasar Sin ta gina a kasar Mozambique za su inganta manyan ayyukan yau da kullum na kasar, kuma za su kawo moriya ga jama'ar kasar.

Dadin dadawa, Mr. Tian Guangfeng ya gabatar da cewa, kasar Mozambique dake a kudu maso gabashin Afrika tana da albarkatun gonaki da ma'adinai sosai, amma kasar Sin tana da fasaha ta zamani da karfi, wadannan sun aza harsashi ga bangarorin biyu wajen yin hadin gwiwa. Yana ganin cewa, kasashen Sin da Mozambique suna da makoma mai kyau wajen raya aikin noma da hakar ma'adinai da yin amfani da albarkatun ruwa.

Kazalika, Mr. Tian Guangfeng ya ba da shawara a kan aikin karfafa huldar hadin gwiwa tsakanin Sin da Mozambique wajen tattalin arziki da ciniki. Inda ya ce, ya kamata a himantar da gwamnatocin kanannan hukumomin kasashen biyu wajen kara yin hadin gwiwa. Alal misali, lardin Hubei na kasar Sin da jihar Gaza ta kasar Mozambique sun kafa huldar abokantaka don neman samun moriyar juna, Mr. Tian ya ba da shawara cewa, kamata ya yi, kasashen biyu sun kara hadin gwiwa a tsakanin jihohi da larduna daban daban, yana fatan ganin karin jihohi da lardunan kasashen biyu za su kafa huldar abokantaka.

A karshe dai, Mr. Tian Guangfeng ya ce, kasar Mozambique tana cikin lumana a fannin siyasa, duk mutanen kasar suna neman samun bunkasuwa, suna bukatar sakamakon da Sin ta samu wajen yin gyare-gyare da neman bunkasuwa a fannin tattalin arziki, suna fatan za su kara sanin al'adun kasar Sin da samu horaswa don kara yin mu'amala a fannin al'au tsakanin kasashen biyu a nan gaba.(Lami)