Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-04-06 22:09:45    
An shimfida hanyoyin mota a kan manyan tuddai??Aikin sufuri a jihar Tibet ya sami kyautatuwa

cri

Kafin jihar Tibet ta samu 'yancin kai ta hanyar lumana, aikin sufuri da harkokin jigilar kayayyaki na jihar ba su bunkasa ba sosai. A wancan lokaci, a dukkan jihar Tibet da fadinta ya zarce murabba'in kilomita miliyan 1.2, ko wata hanyar mota ma babu, a kan labtawa mutane ko dabbobi kayayyaki a lokacin da suke yin jigilar kayayyaki.

Mataimakin shugaban gwamnatin jihar Tibet mai cin gashin kanta ta kasar Sin Mista Salung Phunlha ya ce, sauye-sauyen da aka samu a harkokin sufuri a jihar a cikin 'yan shekarun nan sun burge shi kwarai da gaske: "Na fito daga gundumar Lhatse. A da, duk lokacin da na koma gida don gaishe da iyayena, ina shafe tsawon kwanaki uku ko hudu ina tafiya da kafa a kan hanya tare da kayayyaki. Saboda rashin hanyoyi, ina shan wahalhalu sosai. Amma halin da ake ciki yanzu shi ne, bayan da na shafe tsawon awanni uku ko hudu kawai a cikin mota, na kan isa kauyenmu."

Masu saurare, a ranar 25 ga watan Disamba na shekara ta 1954, an kaddamar da hanyoyin mota guda biyu da jimillar tsawonsu ta kai kilomita 4360, wato hanyar mota da ta hada lardin Sichuan da jihar Tibet, da hanyar mota da ta hada lardin Qinghai da jihar, hakan ya dasa aya ga tarihin rashin hanyar mota a jihar Tibet. A waje guda kuma, fara zirga-zirgar wadannan muhimman hanyoyin mota biyu, ya inganta huldodi da mu'amala a tsakanin jihar Tibet da sauran sassan kasar Sin, da bude wani sabon babi a harkokin sufuri na jihar.

1 2