Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-04-06 20:54:00    
Kungiyar wakilan masana ilimin Tibet ta kasar Sin ta kai ziyara a kasar Amurka

cri
Kwanan baya, kungiyar wakilan masana ilimin Tibet ta kasar Sin ta kai ziyara a kasar Amurka, inda ta yi mu'amala da musayar ra'ayoyi tare da manyan kafofin watsa labarai da hukumomin kwararru na kasar.

A yayin da take Amurka, kungiyar wakilan masana ilimin Tibet ta kasar Sin, wadda ke karkashin jagorancin shugaban sashin nazarin ilimin kabilu da halayya da al'adun dan Adam, kana darektan sashin nazarin tarihi da al'adu na kabilar Tibet na cibiyar nazarin ilimin zaman al'umma ta kasar Sin Mista Hao Shiyuan, ta kai ziyara a kamfanin CBS mai kula da harkokin rediyo da talabijin na kasar, inda bangarorin biyu suka yi musanyar ra'ayoyi kan batutuwa da dama. Bangaren Sin ya bayyana fatansa na bukatar sanannun kafofin watsa labarai na kasa da kasa da su bayar da rahotanni danagne da kasar Sin bisa hakikanin halin da ake ciki.

A waje guda kuma, kungiyar wakilan masana ilimin Tibet ta kasar Sin ta kai ziyara a cibiyar nazarin harkokin gabashi da yammacin duniya, inda kwararrun kasar Sin suka yi shawarwari tare da takwarorin aikinsu na Amurka. A yayin tattaunawar, kwararrun kasar Sin sun bayyana ra'ayoyi da shawarwari kan batutuwan da kwararrun Amurka suka fitar, dangane da al'adu daban-daban da muhallin halittu da dai sauransu. Kazalika kuma, kwararrun kasar Sin sun bayyana cewa, akwai wasu hukumomin nazari na kasashen yammacin duniya wadanda suka yi kuskure a kan batutuwan dake shafar Tibet. Dukkan bangarorin biyu suna ganin cewa, gudanar da shawarwari zai taimaka wajen kawar da bambancin ra'ayi da kara fahimtar juna.