Ran 2 ga wata, a birnin London, hedkwatar kasar Birtaniya, an rufe taron koli da shugabannin kasashe mambobin kungiyar G20 suka yi kan harkokin kudi a karo na 2, inda shugabannin suka cimma daidaito a kan bai wa hukumar ba da lamuni ta duniya wato IMF da sauran hukumomin harkokin kudi na duniya karin kudi da inganta sa ido kan harkokin kudi da sauran batutuwan da ke shafar yin hadin gwiwa a tsakanin kasa da kasa domin daidaita matsalar kudi.
Bayan taron, Gordon Brown firayim ministan Birtaniya, wadda ta sami damar karbar bakuncin wannan taron koli ya gaya wa 'yan jarida cewa, mahalarta taron sun tsai da ra'ayi daya kan daidaita matsalar kudi cikin hadin gwiwar kasashen duniya. Inda ya ce,"Mun yi imani da cewa, a cikin sabon karni, ba za a iya samun wadatuwa ba, sai mun hada kanmu. Ana bukatar dukkan kasashen duniya su bullo da dabara tare domin daidaita matsalar kudi da ke addabar duniya. Ba za mu iya samun bunkasuwa mai dorewa ba, sai mun samu ci gaba tare. Tilas ne a tabbatar da ganin, ciniki ya sake karfafa gwiwar samun bunkasuwar tattalin arziki."
A yayin taron, shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya yi jawabi mai lakabi haka "yin hadin gwiwa domin jure wahala tare", inda ya sa muhimmanci kan jaddada muhimmancin inganta sa ido kan harkokin kudi da gaggauta yin gyare-gyare kan tsarin kudi na duniya.
Sa'an nan kuma, a bayyane shugaba Hu ya nuna cewa, kasar Sin na goyon bayan bai wa hukumar IMF karin kudi. Tana son yin tattaunawa da bangarori daban daban tare da ba da gudummawa. A sa'i daya kuma, ya jaddada cewa, kasar Sin na ganin cewa, ya kamata a yi amfani da karin kudin kan kasashe marasa ci gaba tukuna. Haka kuma, kamata ya yi a kafa tsarin ceton harkokin kudi na duniya mai amfani, ta haka za a iya kimanta kasashe ta hanyar kimiyya a kan ko suna da uzurin karbar rancen kudi daga dukkan fannoni bisa hakikanin halin da suke ciki.
A cikin jawabinsa, shugaba Hu ya nuna cewa, ya kamata a yi yaki da batun samar da kariyar ciniki ta hanyoyi daban daban da kuma kiyaye kyakkyawan muhalli a fannin yin ciniki ba tare da shinge ba. Ban da wannan kuma, ya ce, kasar Sin na fatan kasashen da abin ya shafa za su iya sassauta kayyadewa kan kasashe masu tasowa a fannin aikin fitar da kayayyaki ta yadda za su iya habaka yin ciniki a tsakaninsu, haka kuma, za su iya sa kaimi kan samun sakamako a yayin shawarwari na zagaye na Doha daga dukkan fannoni cikin sauri.
Bayan taron, Chen Deming, ministan kasuwanci na kasar Sin ya jaddada wa 'yan jarida matsayin kasar Sin kan yin yaki da samar da kariyar ciniki. Yana mai cewar,"An sami sakamako mai kyau kan daidaita matsalar kudi cikin hadin gwiwar kasashen duniya a yayin taron koli na G20. Na lura da cewa, a yayin taron, an sami sakamako kan tabbatar da zaman kasuwar harkokin kudi da gaggauta yin gyare-gyare kan tsarin harkokin kudi, tare da nuna kin yarda da samar da kariyar ciniki. Sa'an nan kuma, taron ya gabatar da sa kaimi kan gudanar da shawarwari na zagaye na Doha cikin himma. Matsalar kudi ta kara nuna mana muhimmancin yaki da samar da kariyar ciniki."
A cikin sanarwar da shugabannin suka bayar bayan taron, sun nuna cewa, dukkansu sun yarda da kara hada kai kan sa ido ga tsarin harkokin kudi na duniya. Game da wannan, Mr. Brown ya ce"A karo na farko mun dauki matakin bai daya, za mu fito da ka'idoji kan yin gyare-gyare a tsarin bankuna na duniya. Mun kuma yarda da kafa ma'aunin ilmin akanta na duniya da yin gyare-gyare kan hukumomin kimanta samun amincewar jama'a domin magance samun rikici ta fuskar moriya."
A yayin taron, shugaba Hu ya jaddada cewa, kasar Sin za ta ci gaba da ba da gudummawarta wajen farfado da tattalin arzikin duniya.
Jawabinsa ya jawo hankali sosai da kuma babban yabo. Shugabannin kasashe da dama sun nuna fatansu na inganta hadin gwiwa da kasar Sin domin daidaita matsalar kudi ta duniya tare.(Tasallah)
|