Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-04-02 10:18:58    
Kasashen Sin da Amurka sun amince da inganta kyakkyawar dangantakar hadin gwiwa tsakaninsu a karni na 21

cri

Aminai 'yan Afrika, ko kuna sane da cewa, shugaban kasar Sin Hu Jintao ya sauka a birnin London na Burtaniya  a ranar 1 ga wata da maraice don halartar taron koli na biyu na shugabannin kasashe 20 masu karfin tattalin arziki a duniya da aka yi a yau Alhamis. Jim kadan bayan saukarsa a London, shugaba Hu Jintao ya gana da takwaran aikinsa na kasar Amurka Barack Obama, inda gaba dayansu suka amince da sanya kokari matuka wajen inganta kyakkyawar dangantakar hadin gwiwa tsakaninsu daga dukkan fannoni. Lallai ganawar da suka yi ta fi janyo hankalin mutane bisa sauran shawarwarin bangarori biyu da aka yi a wannan rana tsakanin shugabannin kasashen waje mahalartan taron kolin.

A gun ganawar, shugaba Hu Jintao ya buga take ga ci-gaban da aka samu a fannin inganta dangantakar dake tsakanin kasashen Sin da Amurka tun bayan da Obama ya zama sabon shugaban kasar ta Amurka. Sa'annan shugaba Hu ya furta cewa, a yanzu haka dai, dangantakar dake tsakanin kasashen biyu tana kan sabon mataki yayin da take fuskantar kyakkyawar damar samun ci-gaba. Kamata ya yi kasashen biyu su sanya kokari wajen inganta kyakkyawar dangantakar dake tsakanin kasashen Sin da Amurka a karni na 21. Kazalika, shugaba Hu Jintao ya nuna cewa, ko da yake akwai bambanci tsakanin bangarorin biyu a fannin tsarin zamantakewar al'umma, da tarihi, da kuma na al'adun gargajiya da dai sauran fannoni, amma duk da haka, ya kamata bangarorin biyu su duba kowanensu da ido mai basira yayin da suke fuskantar kalubale da kuma matsaloli iri daban-daban masu sarkakkiya. Dadin dadawa, shugaba Hu Jintao ya ce, ya kamata bangarorin biyu su dinga zurfafa hadin gwiwa da yin musanye tsakaninsu a fannin tattalin arziki, da yaki da ta'addanci, da riga-kafin yaduwar makaman nukiliya, da aiwatar da dokokin shari'a, da makamashi da kuma na sauyin yanayi da dai sauran fannoni yayin da suke kara tuntubar juna a kan batutuwan shiyya-shiyya har da na duk duniya.

A nasa bangaren, shugaba Obama ya yaba da kasar Sin sosai da sosai bisa muhimmiyar rawa da take takawa a duniyar yau yayin da yake jaddada muhimmancin kyautata huldodin dake tsakanin kasashen Amurka da Sin. Yana mai cewa :' Babu tantama akwai kyakkyawar dangantakar dake tsakanin kasashen Amurka da Sin a halin yanzu. Na sha furtawa kuma har ila yau na hakkake cewa ba ma kawai irin wannan dangantaka na da muhimmancin gaske ga jama'ar kasashen biyu ba, har ma ta kirkiro sharadi mai amfani ga kasashen duniya wajen tinkarar kalubale iri daban-daban.' Daga baya shugaba Hu Jintao ya kara da cewa : ' Wata irin kyakkyawar dangantakar dake tsakanin kasashen Sin da Amurka ba kawai ta dace da babbar moriyar kasashen biyu da jama'a'su ba, har ma ta amfana wa zaman lafiya mai dorewa da kuma wadata na kasashen Asiya da tekun Pacific har da na duk duniya.' ' Bangaren kasar Sin', in ji shi, 'yana so ya sanya kokari matuka tare da bangaren kasar Amurka wajen kara ingiza huldodin dake tsakanin kasashen biyu'.

Jama'a masu sauraro, shugabannin kasashen biyu sun jaddada cewa, a matsayin muhimman kasashe guda biyu masu karfin tattalin arziki, kasashen Sin da Amurka za su sanya kokari tare da sauran kasashe daban-daban wajen farfado da tattalin arzikin duniya da kara zaunar da tsarin kudade na duniya. Shugaba Obama ya ce, gwamnatin Amurka tana tsayawa tsayin daka kan manufar Sin daya tak a duniya da kuma sanarwar hadin gwiwa guda uku da suka rattaba hannu a kai. Ya kuma jaddada cewa, Tibet, wani yanki ne na kasar Sin. Saboda haka, kasar Amurka ba ta goyon bayan yunkurin samun 'yancin Tibet. A karshe dai, shugabannin kasashen biyu sun amince da sanya kokari tare wajen daidaita batun nukiliya na Zirin Korea, da batun Iran, da batun tallafa wa Sudan da kuma batun yanayin siyasa na kudancin Asiya da dai sauran batutuwa. ( Sani Wang )