Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-04-01 11:15:56    
Kasar Sin za ta hada kai da sauran kasashe don neman cimma tudun dafawa a taron koli na G-20

cri
Cikin shirin yau za mu yi bayani kan ra'ayin gwamantin kasar Sin kan taron koli na kasashe masu karfin tattalin arziki na G-20 wanda za a fara yinsa gobe a birnin London, hedikwatar kasar Birtaniyya. Hu Jintao, shugaban kasar Sin, kafin ya je halartar taron, ya sanar da cewa, kasar Sin za ta dauki nauyi, ta hada kai da sauran kasashe masu halartar taron, don neman cimma tudun dafawa a wajen taron. Ya ce, bisa mawuyacin halin da ake fama da shi a wajen tattalin arziki, ya zama wajibi  a dauki matakan kare kasuwannin hada-hadar kudi, da sa kaimi ga tattalin arziki a gida, da kau da kariyar ciniki, da kuma yi kwaskwarima ga tsarin harkar hada-hadar kudi ta duniya.

A wajen zaman taron koli na G-20 na farko da aka yi a birnin Washington na kasar Amurka, Shugaba Hu na kasar Sin ya furta cewa, 'Kasar Sin za ta dauki nauyi, ta kara hadin kai da kasashen duniya, don neman kiyaye zaman karko a kasuwannin hada-hadar kudi na duniya.' Sa'an nan bisa kokarin da bangarori daban daban suka yi, shugabannin kasashen G-20 sun samu ra'ayi daya kan hada karfin kasashen duniya don raya tattalin arziki da tinkarar rikicin hada-hadar kudi, inda nasarar da aka samu ya sa ake sa rai kan makomar taron koli da za a yi a London. Dangane da haka, He Yafei, mataimakin minista mai kula da harkokin waje na kasar Sin, ya nuna cewa, "Kasar Sin na da ra'ayi na daukar nauyi da neman taka rawa, yadda za ta yi kokari tare da sauran bangarorin duniya don neman cimma tudun dafawa kan batutuwa masu muhimmanci."

Bayan samun jin radadin rikicin kudi, kasashen duniya sun dauki matakai daban daban don farfado da tattalin arzikinsu. Kasar Sin ita ma ta ware makudan kudade da yawansu ya kai Yuan biliyan 4000 don raya masana'antu da aikin gona, da kuma kara samar da guraben aiki, ta yadda za a iya kare saurin bunkasuwar tattalin arzikin kasar. Kamar dai yadda Wen Jiabao,firayin ministan kasar, ya ce, "Mun shirya sosai don tinkarar mawuyacin hali mai dorewa. Komai matsalar da muke fuskanta a nan gaba, za mu iya daukar sabon mataki don kau da ta."

Bisa matsayinta na wata kasa mai tasowa, kasar Sin ta tsaya kan kare moriyar kasashe masu tasowa, don neman raya kanta tare da sauran kasashe, haka kuma, a wajen taron koli da aka yi a birnin Washington, Shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya yi kira ga kasashen duniya da su mai da hankali kan kasashe masu tasowa, lokacin da suke daukar matakai don tinkarar rkicin kudi, ta yadda za a magance kawo lahani ga kasashe marasa karfin tattalin arziki. Ban da wannan kuma, wasu jami'an kasar Sin sun nuna ra'ayi na bukatar sake fasalin tsarin kungiyoyin hada-hadar kudi na duniya, don karfafa wakilcin da kasashe masu tasowa ke samu a cikin kungiyoyin, haka kuma an yi kira da a kirkiro wata taswairar tafiyar da aikin a taron koli da za a yi a London. Sa'an nan He Yafei, mataimakin ministan waje na kasar Sin ya bayyana ra'ayin da kasar Sin ta nuna wa sauran kasashe masu tasowa da cewa, "Za mu tsaya kan kokarin neman cimma burin raya kasa na karni, da cika alkawaran da muka yi wa kasashe masu tasowa, da kuma sauran alkawaran da shugabannin kasarmu suka yi."(Bello Wang)