Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-30 21:00:10    
Kasar Sin tana fuskanta yadda tattalin arzikin duniya yake cikin tangarda a shekara ta 2008

cri
A shekarar 2008, tattalin arzikin duniya ya gamu da tangarda sakamakon rikicin hada hadar kudi na duniya da ya auku sakamakon matsalar ba da lamuni ga kasuwar gidajen kwana ta kasar Amurka. Sakamakon haka, an kawo mummunan tasiri ga tattalin arzikin kasar Sin. Mr. Cheng Siwei, wani mai ilmin tattalin arziki, kuma tsohon mataimakin shugaban majalisar dokokin kasar Sin ya yi nazarin cewa, saurin karuwar tattalin arzikin kasar Sin zai ragu da kimanin kashi 10 cikin kashi dari sakamakon raguwar saurin karuwar kayayyakin da ake fitarwa zuwa kasashen waje. Mr. Cheng Siwei ya ce, "Tabbas ne za a rage yawan kayayyakin da muke fitarwa zuwa kasashen waje, kuma za a rage yawan ribar da muke samu sakamakon raguwar saurin karuwar tattalin arzikin duniya. Sakamakon haka, saurin karuwar tattalin arzikinmu zai kuma ragu. Na kiyasta cewa, saurin karuwar tattalin arziki zai kai kimanin 10% a shekara ta 2008."

Yanzu sabuwar kididdigar da aka bayar ta sheda cewa, maganar da Mr. Cheng Siwei ya yi ta yi daidai. Bisa kididdigar da hukumar kididdiga ta kasar Sin ta bayar a watan Oktoba, a cikin farkon watanni 9 da suka gabata na shekara ta 2008, saurin karuwar tattalin arzikin kasar Sin ya kai kashi 9.9 cikin kashi dari, wato ya ragu da kashi 2.3 cikin kashi dari bisa na makamancin lokaci na shekara ta 2007.

Lokacin da ake raya tattalin arziki, idan wani sashen tattalin arziki ya hadu da matsala, nan da nan ake samun illa ga sauran sassan tattalin arziki da suke da nasaba da wannan sashe. Sabo da haka, yanzu kanana ko matsakaitan masana'antu da kamfanoni na kasar Sin wadanda suke fitar da kayayyakinsu zuwa kasashen waje suna fuskantar matsin lamba sosai wajen kokarin kasancewarsu a duniya sakamakon raguwar yawan kayayyakin da ake fitarwa zuwa kasashen waje. Har ma an riga an rufe wasu kananan masana'antu da kamfanoni wadanda ba su da karfin yin takara a kasuwa.

A gabanin hali mai tsanani da tattalin arzikin duniya ke ciki, tun daga karshen rabin shekara ta 2008, gwamnatin kasar Sin ta daidaita manufofin raya tattalin arziki daga dukkan fannoni bisa hakikanin halin da ake ciki cikin lokaci. Alal misali, tun daga watan Agusta, gwamnatin kasar Sin ta kula da nauyin farko da ke bisa wuyanta na "yin rigakafin cigaban tattalin arziki fiye da kima" da ya zama "tabbatar da cigaban tattalin arziki cikin sauri ba tare da tangarda ba, da kuma kayyade karuwar farashin kayayyaki cikin sauri fiye da kima". Amma bayan watanni 2 kawai, gwamnatin kasar Sin ta sake daidaita manufofinta na kudi, wato ta soma dan bude bakin aljihunta.

Masana sun bayyana cewa, wadannan jerin manufofin tattalin arziki da gwamnatin kasar Sin ta dauka sun bayyana cewa, yanzu gwamnatin kasar Sin tana kara karfinta na daidaita tattalin arziki daga dukkan fannoni. Madam Zuo Xiaolei, mai ilmin tattalin arziki na farko ta kamfanin cinikin takardun hannun jari na Yinhe na kasar Sin ta ce, "Bayan an shiga rabin shekarar da ta gabata, halin da tattalin arziki ke ciki ya samu sauye-sauye, kuma an samu dalilai marasa tabbaci. Mun riga mun sha fama da bala'u daga indallahi, kamar su bala'in girgizar kasa da bala'in guguwar iska da ruwan dusar kankara. Yanzu rikicin ba da rancen kudi ga gidajen kwana da ya auku a kasar Amurka yana kawo illa ga kasuwar cinikin waje ta kasar Sin. Sabo da haka, matakin da ya wajaba shi ne a daidaita manufar raya tattalin arziki a cikin wannan hali mai tsanani domin tabbatar da cigaban tattalin arziki ba tare da samun tangarda ba a nan gaba."

Lokacin da gwamnatin kasar Sin take daidaita manufofin tattalin arziki bisa hakikanin halin da ake ciki, masana'antun kasar Sin sun kuma yi fama da hali mai tsanani da suke ciki a fannin tattalin arziki ta hanyoyi iri daban daban. Wasu masu tafiyar da harkokin masana'antu sun canza hanyoyinsu na neman cigaba cikin sauri sosai. Kamfanin Xie Wei na yin kayayyakin roba da ke birnin Yongzhou na lardin Hunan, kamfani ne da aka kauratar da shi daga lardin Guangdong zuwa lardin Hunan. Mr. Lin Zhimin ya gaya wa wakilinmu dalilin da ya sa hakan ta faru da cewar, "Bayan da na dauke kamfanina daga yankin da ke bakin teku zuwa lardin Hunan, na yi tsimin kudade da yawa. A waje daya kuma, za mu iya yin tsimin wasu kudaden wajen yin amfani da 'yan kwadago a lardin da muke ciki yanzu. A takaice dai, jimillar kudaden da za mu iya yin tsiminsu ta ragu da kimanin 18%."

Bugu da kari kuma, wasu masana'antu da kamfanoni na kasar Sin yanzu suna neman cigaba bisa sabbin fasahohin da suka kirkiro da kansu domin kara darajar kayayyakinsu da neman karin kwangilolin sayar da kayayyakinsu a kasuwa. Kamfanin Hua Wei da ke birnin Shantou na lardin Guangdong wani babban kamfani ne da ke samar da kayayyakin wasa na yara. A kowace shekara, yawan kayayyakin wasa na yara da wannan kamfani ya kan samar ya kai guda miliyan 60 da darajarsu ta kai kudin Sin yuan miliyan dari 8. Lokacin da ake rufe sauran masana'antun samar da kayan wasa na yara sakamakon rikicin hada hadar kudi na duniya, wannan kamfani yana cigaba da samun sabbin kwangiloli. An yi hasashen cewa, yawan kudaden kwangilolin da zai samu a duk shekara ta 2008 zai karu da 30%. Mr. Qiu Liang, mataimakin babban direktan wannan kamfani ya ce, muhimmin dalilin da ya sa aka iya samun cigaba ba tare da tangarda ba shi ne zuba karin kudade kan aikin nazari. Mr. Qiu ya ce, "Yawan kudaden nazarin sabon salon kayan wasa na yara da muke zubawa a kowace shekara ya kai fiye da kudin Sin yuan miliyan 10. Dalilin da ya sa muka zuba wadannan kudade masu dimbin yawa shi ne kafa tambarin kasuwanci na kayayyakinmu da kirkiro sabbin fasahohin tabbatar da ingancin kayayyakinmu. Sakamakon haka, za mu iya tabbatar da samun kwangiloli a kasuwa a kullum."

A lokacin da ake tinkarar rikicin hada hadar kudi na duniya, wasu kasashe suna fatan kasar Sin wadda take da dimbin adanannun kudaden musaya za ta iya ceton tattalin arzikin duk duniya. Amma kwararru da masanan ilmin tattalin arziki masu dimbin yawa sun ce, idan an kwatanta ta da kasashen yammacin duniya, tattalin arzikin kasar Sin ba shi da karfi sosai. Yanzu a lokacin da ake tinkarar rikicin kudi, idan kasar Sin ta iya tabbatar da samun cigaban tattalin arzikinta cikin sauri ba tare da tangarda ba, wannan shi ne gudummawar da kasar Sin za ta bai wa duk duniya. A waje daya, shugabannin kasashen duniya sun bayyana cewa kasar Sin tana son hada kan sauran kasashen duniya domin tinkarar rikicin hada hadar kudi tare. Mr. Danilo Turk, shugaban kasar Slovenia ya ce, "Kasar Sin na daya daga cikin muhimman karfin raya tattalin arziki. Sabo da haka, a ganina, da farko dai a tabbatar da ci gaba da samun bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin kamar yadda aka saba a da. Idan an iya tabbatar da samun cigaban tattalin arzikin kasar Sin, tabbas ne za a amfana wa duk duniya."

A shekara ta 2008, ban da rikicin hada hadar kudi na duniya, kasar Sin ta kuma sha wahalhalu iri iri, kamar su bala'in ruwan sama da dusar kankara da bala'in girgizar kasa mai tsanani a lardin Sichuan, wadanda suka yi sanadiyyar mutuwar mutane masu dimbin yawa da hasarar dukiyoyin da yawansu ya kai fiye da biliyoyin yuan kudin Sin. Sabo da haka, kasar Sin tana da shirin zuba biliyoyin kudade domin farfadowar yankunan da suka yi fama da bala'u daga indallahi. Mr. Wang Siguang, mataimakin shugaban kwamitin neman bunkasuwa da yin kwaskwarima na lardin Sichuan ya ce, "Za mu kara zuba jari a kan ayyukan da ke da nasaba da zaman rayuwar jama'a. Da farko dai za a warware matsalar rashin wuraren kwana da ke kasancewa a gaban jama'a. Sannan za a daidaita sauran matsalolin da suke shafar ayyukan samar da ruwan sha da wutar lantarki da hanyoyin mota da gidajen waya da rediyo da kuma talibijin da sauran ayyukan jama'a. Bugu da kari kuma, za a zuba jari kan wasu muhimman ayyukan yau da kullum." (Sanusi Chen)