Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-30 18:18:01    
An gabatar da rahoto kan bunkasuwar jihar Tibet a fannonin tattalin arziki da zaman al'umma

cri
Ran 30 ga wata, cibiyar nazarin harkokin da suka shafi yankin Tibet na kasar Sin, wato hukumar koli ta kasar Sin a fannin nazarin ilmin Tibet ta kaddamar da "rahoto kan bunkasuwar jihar Tibet a fannonin tattalin arziki da zaman al'umma", inda ake gano cewa, a sakamakon goyon bayan da gwamnatin tsakiya da larduna da birane na kasar suke bayarwa, Tibet ta sami saurin bunkasuwar tattalin arziki.

Wannan rahoto ya nuna cewa, a cikin shekaru 50 da aka yi gyare-gyare a Tibet ta fuskar dimokuradiyya, Tibet ta sami karin albarkatun zaman al'ummar kasa, tare da samun kyautatuwar rayuwar mutane da kuma tabbatar da kiyaye hakkokin dan Adam. Mazauna Tibet, musamman ma 'yan kabilar Tibet sun sami karin kudin shiga da tsawon rai da kuma ilmi, wadanda ba su taba samu ba a tarihin Tibet.

Zhu Xiaoming, wani manazarci na cibiyar nazarin harkokin da suka shafi yankin Tibet na kasar Sin ya yi karin bayani da cewa,"A duk fadin kasar Sin, a matsayin wata jiha mai cin gashin kanta, Tibet ta fi samun babban ci gaba a fannoni masu yawa. An canza tsarin bauta na gargajiya zuwa tsarin gurguzu a Tibet tare da samun matsaloli da yawa, a sakamakon karuwar yawan 'yan kananan kabilu a wurin, wadanda suke bin addinai masu nau'o'i da dama. Gwamnatin tsakiya ta aiwatar da manufofi da yawa da suka sha bamban da saura, ta haka Tibet ta iya samun irin wannan babban ci gaba lami lafiya."

Ban da wannan kuma, rahoton ya yi nuni da cewa, kudaden da gwamnatin tsakiya ta zuba wa Tibet da kuma taimakon da sauran larduna da birane suke ba ta sun rage wa Tibet albarkatun da take iya amfana, sun kuma sassauta matsin lambar da Tibet ke fuskanta ta fuskar kiyaye muhalli. Sa'an nan kuma, sun taka muhimmiyar rawa wajen raya muhalli a Tibet. Lhorong Dradul, wani manazarci na daban na cibiyar nazarin Tibet ta kasar Sin ya bayyana cewa,"Jihar Tibet mai cin gashin kanta tana cikin tudun Qingzang, tana da muhimmanci matuka a fannin muhalli. Amma a kan gurbata muhallin Tibet cikin sauki matuka. A ganina, makudan kudaden da gwamnatin tsakiya ta zuba wa Tibet da kuma tallafin da sauran larduna suke ba mu sun fi ba da gudummawa wajen kiyaye muhalli a Tibet. Mazauna Tibet suna amfani da wadannan kudade wajen raya aikin kawo albarka kai tsaye, a maimakon haka ma'adinai da cire itatuwa da ciyayi. Na taba zuwa ko ina a duniya, ban da iyakacin duniya na arewa da na kudu. Duk da haka, iska ta fi samar da ni'ima a Tibet."

Domin hana gurbata muhalli, Tibet ta tabbatar da manyan tsare-tsare kan samun bunkasuwa, wato ta dauki jagoranci wajen raya aikin yawon shakatawa da likitancin Tibet na gargajiya da maganin Tibet tare da kiyaye muhalli.

Duk da haka, rahoton ya nuna cewa, a halin yanzu Tibet ba ta sami daidaito a fannin raya birane da kauyuka ba. Haka kuma, tana bukatar yin namijin kokari wajen kyautata rayuwar mutane da daidaita matsalar karancin albarkatun kwadago. Game da wannan, Mr. Lhorong Dradul ya kara da cewa,"Gwamnatin tsakiya da sauran lardunan kasar sun bai wa Tibet taimako da yawa, ta haka Tibet ta sami damar raya kanta da kuma samar da guraban aikin yi. Babu wanda zai iya samun aikin yi, sai ya mallaki fasaha. Amma mazauna Tibet da yawa ba su da isasshiyar fasaha da ilmi. Yau da shekaru 2 da suka wuce, hukumar Tibet ta fito da wata manufa, inda ta bukaci a bai wa makiyaya guraban aikin yi wadanda suke iyawa a fannin raya Tibet. Sa'an nan kuma, tilas ne a dauki makiyaya na wurin wajen gudanar da ayyukan da gwamnatin ta zuba jari a kai. Yawan makiyayan zai wuce sulusi bisa jimillar 'yan kwadago."

Nan da shekaru 2 masu zuwa, gwamnatin tsakiya za ta bai wa Tibet kudin Sin kusan yuan biliyan 80. A sakamakon irin wadannan makudan kudade, Tibet za ta iya ta samun saurin bunkasuwar tattalin arziki.(Tasallah)