A da, abin musamman na addinin Buddaha na gargajiyar Tibet shi ne tsarin mulki irin na gwamutsa siyasa da addini. Ba kawai manyan mabiya addinin Buddah suna da tasiri a fannin addini ba, kuma suna yin mallakar harkokin Tibet. A fannin tattalin arziki kuma, gidajen ibada na addinin Buddah na gargajiyar Tibet suna mallakar yawan kasa, da bayi manoma.
Bayan da aka yi gyare-gyaren dimokuradiya a Tibet, an soke tsohon tsarin mulki irin na gwamutsa siyasa da addini. Yanzu, ban da kudin da gwamnatin kasar Sin ta bayar, kuma yawancin gidan ibada na gudanar da harkokinsu ta yin amfani dukiyoyinsu, da kuma ayyukan da mabiya addinin Buddah suke yi.
1 2 3
|