Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-24 18:48:18    
Ana kokarin dasa itatuwa da ciyayi a gabobin kogin Yarlung Zangbo a jihar Tibet

cri

A halin da ake ciki yanzu,'yan kabilar Tibet a yankin Shannan suna kokarin dasa itatuwa da ciyayi a gabobi biyu na kogin Yarlung Zangbo a jihar Tibet, domin tsare iska da rairayi. Yankin Shannan yana sashen tsakiya na kogin Yarlung Zangbo, wanda ya dade yana kasancewa daya daga cikin wuraren jihar Tibet da suka fi jin radadin zaizayar kasa a jiki.

Shugaban jam'iyyar kwaminisanci ta kasar Sin a kauyen Menggarong Mista Jampa ya ce, a shekarar da muke ciki, mazauna kauyen sun fara dasa itatuwa jim kadan bayan shigowar sabuwar shekara bisa kalandar gargajiya ta kabilar Tibet:

"Mazauna kauyenmu suna cike da kuzari a yayin da suke dasa itatuwa. A wannan shekara, gwamnatin kasar ta ba mu karin kudaden tallafi. A yau, za mu iya samun kudin Sin Yuan 1.5 daga kowane rami da muka haka. Mazauna kauyenmu suna farin-ciki sosai."

A kowace shekara, gwamnatin jihar Tibet ta kan ware kudaden da yawansu ya kai Yuan miliyoyi a fannin dasa itatuwa da ciyayi a gabobi biyu na kogin Yarlung Zangbo, ciki har da kudaden da za ta baiwa 'yan kabilar Tibet wadanda suka dasa itatuwa. Shugaban hukumar gandun daji ta yankin Shannan na jihar Tibet Mista Sonam Dorje ya bayyana cewa:

"Jama'a suna cin gajiya daga aikin dasa itatuwa da shimfida gandun daji. A halin da ake ciki yanzu, gwamnatin kasar Sin tana maida hankali sosai kan aikin dasa itatuwa da shimfida gandun daji, da kuma kara bayar da kudaden tallafi. Jama'a suna kara sha'awar aikin dasa itatuwa da ciyayi, da bukatar hukumar gandun daji da ta shirya ayyukan dasa itatuwa, a wani kokarin kyautata muhallin halittu."

Sakamakon kokarin da ake yi a fannin dasa itatuwa da shimfida gandun daji, muhallin halittu a yankin tsakiyar kogin Yarlung Zangbo ya sami kyautatuwa kwarai da gaske. 'Yar kauye Kunga ta gayawa wakilin CRI manyan sauye-sauyen da muhallin yankunan dake kewaye da kauyenta ya samu, inda ta ce:

"Tsofaffi sun gaya mini cewa, a lokacin kuruciyata, akwai kakkarfar iska hade da tsakuwoyin yashi a wannan wuri. Amma a halin da ake ciki yanzu, an rage karfin iska saboda dashen tsare iska da rairayi, zaman rayuwarmu ya sami kyautatuwa sosai."

Aikin dasa itatuwa don tsare iska da rairayi a yankin tsakiyar kogin Yarlung Zangbo, yana daya daga cikin manyan ayyukan da ake gudanarwa a fannin kiyaye muhallin halittu a jihar Tibet mai cin gashin kanta ta kasar Sin. Shugaban hukumar kiyaye muhalli ta jihar Tibet Mista Zhang Yongze ya ce:

"Daga shekara ta 2001 zuwa 2005, yawan kudaden da gwamnatin kasar Sin ta zuba a harkokin kiyaye muhallin halittu na jihar Tibet ya kai Yuan biliyan 3.21, daga shekara ta 2006 zuwa 2008 kuma, yawan kudaden da gwamnatin ta zuba ya riga ya kai Yuan biliyan 3.25."(Murtala)