Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-20 17:28:33    
Amsoshin wasikunku

cri
To, kwanan nan, mun yi farin ciki da samun dimbin sakonnin da masu sauraronmu suka aiko mana, don mu yi musanyar ra'ayoyi a kan harkoki daban daban. Ga wani sakon da ke hannuna, da Nuraddeen Ibrahim Adam, daga Chiromawa QTRS, jihar Kano, tarayyar Nijeriya, ya aiko mana, inda ya ce, "Na saurari shirinku na 'Ilimin Zaman Rayuwa' na yau, kuma na ji dadi kan yadda kuka yi bayani dangane da hadarin shakar hayakin taba sigari. Na ji cewa idan mutum na shakar hayakin taba to zai iya kamuwa da ciwon sankarar huhu." To, malam Nuraddeen, mun yi farin ciki da ka ji dadin bayaninmu, kuma da fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da mu a ko da yaushe.

Sa'an nan, mun kuma sami sako daga iyalin Garba Umar Kongo, wato wasikar da Abudullahi Abubakar da Usman Abubakar da Umar Abubakar da Sa'idu Abubakar da Fatima Abubakar da Amina Abubakar da Aisha Abubakar da dai sauransu wadanda ba mu karanta sunayensu duka ba sabo da karancin lokaci, wato yara ga malam Garba Umar Kongo, Nasarawa 'yan Lemu Dutse Reme Funtua, jihar Katsina, tarayyar Nijeriya, suka hada kai suka aiko mana, inda suka ce, "dalilin rubuta muku wannan wasikar tamu shi ne domin mu mika ma dukan ma'aikatan gaisuwar fatan alheri, kuma muna son mu mika maku gaisuwar ga sabbin ma'aikatan da suka samu aiki a gidan rediyonku, Allah ya ba mu sa'a, Amin, kuma muna shaida muku irin farin cikin da muke yi da sauraron gidan rediyonku." To, mun gode ga duk wadanda suka aiko mana sakon gaisuwa daga iyalin Garba Umar Kongo, kuma dukan ma'aikatan sashen Hausa na CRI muna isar da gaisuwarmu zuwa gare ku duka.

Sai kuma wani labarin da ya faranta mana rai, wanda muka samo shi daga kungiyar masu sauraronmu ta Jeyrala, wato cewa aka yi, shugaban kungiyar, Musa Adamu Abubakar ta daure aure da amaryarsa Aishatu Adamu Abudullahi, a ran 30 ga watan Janairu da ya wuce. Mun ji dadin wannan labari, muna kuma taya Musa Adamu Abubakar da amaryarsa murna kan daurin aure da suka yi, kuma da fatan Allah ya ba ku zaman lafiya da kazantar daki.

To, masu sauraro, kada dai a shagala, Amsoshin Wasikunku ne kuke saurara daga nan sashen Hausa na CRI. To, ga shi kuma a cikin wasikar da malama Hajara Nasiru daga birnin Yola, jihar Adamawa, tarayyar Nijeriya ta aiko mana tambayar da ta ce, shin wadanne kasashe ne ke da shugabanninsu da suka kasance mata, kuma ina so a ba ni tarihin shugabar kasar Liberia, wato madam Ellen Johnson-Sirleaf. Ban da ita, akwai kuma Bello Abubakar malam Gero, daga tudun Wada Riyojin Dan Umma, bayan Rima rediyo, jihar Sokoto, tarayyar Nijeriya, wanda ya aiko da tasa tambayar irinta. To, a cikin shirinmu na yau, bari mu amsa tambayar, da fatan za ku gamsu da bayaninmu, kuma sauran masu sauraronmu ma za ku karu.

Tun lokacin da matan kasar Finland suka sami ikon zabe da kuma ikon a zabe su a shekarar 1906, wanda ya nuna mana cewa, mata sun fara shiga fagen siyasa, yanzu karin mata shugabanni na taka kyakkyawar rawa cikin fagen siyasar duniya. Daga cikinsu kuma, akwai shugabar Indiya Pratibha Patil, wadda ta dare mukamin shugabar kasar a shekarar 2007, kana kuma ta kasance shugaba mace ta farko tun bayan da aka sami 'yancin kan Indiya yau da shekaru fiye da 60 da suka wuce. Sa'an nan, akwai Madam Michelle BACHELET Jeria, shugabar kasar Chile, wadda ta hau kan kujerar shugabancin Chile a shekarar 2006, kuma ita ce shugaba mace ta farko a tarihin kasar. Sai kuma madam Tarja Halonen, shugabar kasar Finland, wadda ta ci zaben zama shugaba mace ta farko a tarihin kasar a shekarar 2000, kuma a shekarar 2006, ta sake cin zaben. Ban da su, sai shugabar kasar Phillippines, Gloria Macapagal ARROYO, kuma ita ce shugaba mace ta biyu a tarihin kasar. Sa'an nan, Angela Merkel, ta ci zaben zama firaministar kasar Jamus a shekarar 2005, kuma sakamakon hakan, ta zama firaminista mace ta farko a tarihin kasar. Sai kuma Helen Clark, ita ce firaministar kasar New Zealand. Akwai kuma Mary MCALEESE, wadda ita ce shugabar kasar Ireland. To, a nahiyar Afirka ma, akwai wasu shugabannin da suka kasance mata, ciki har da shugabar kasar Liberia, madam Ellen Johnson-Sirleaf, da firaministar kasar Mozambique, Luisa Dias Diogo.

An haifi madam Ellen Johnson-Sirleaf ne a shekarar 1938, kuma ta taba samun digiri na biyu a jami'ar Harvard ta Amurka. Daga shekarar 1977 zuwa ta 1980, Madam Johnson-Sirleaf ta taba rike mukaman mai taimakawa ministan kudi na Liberia da mataimakiyar ministan kudi da kuma ministar kudi ta kasar. A shekarar 1985, ta ci zaben zama 'yar majalisar dokokin kasar. Sa'an nan, daga shekarar 2003 zuwa ta 2005, madam Johnson-Sirleaf ta zama shugabar gwamnatin wucin gadi ta Liberia.

A watan Nuwamba na shekarar 2005, Madam Johnson-Sirleaf ta ci zaben zama shugabar Liberia, sakamakon haka, ta zama shugaba mace ta farko da jama'a suka zaba a tarihin kasashen Afirka, kuma a watan Janairu na shekara ta 2006, ta yi rantsuwar kama aiki.

Da ma Madam Johnson-Sirleaf ta taba yin aiki da wasu kungiyoyin duniya da hukumomin kudi, har ma ta taba zama babbar jami'a a bankin duniya da hukumar UNDP.

A matsayinta na jagorar jam'iyyar Unity ta Liberia, Madam Johnson-Sirleaf ta sami girmamawar jama'a sabo da halayyarta, har ana bayyana ta a matsayin mace mai jan hali.

Sai kuma Madam Luisa Dias Diogo?firaministar kasar Mozambique, wadda ta fara aiki a ma'aikatar kudi ta Mozambique a shekarar 1980, kuma a shekarar 1999, ta zama ministar tsara shirye-shirye da kudi ta kasar. A watan Faburairu na shekarar 2004, Madam Luisa Dias Diogo ta zama firaministar Mozambique, haka kuma firaminista mace ta farko a kasar.

Amsarmu ga malama Hajara Nasiru da kuma Bello Abubakar malam Gero ke nan, da fatan kun gamsu. Ban da su, akwai kuma Hassan A.MainaKaina daga Damaturu, jihar Yobe, tarayyar Nijeriya, da Ali Jauro mai gidan wanka kurna, da sauran wadanda suka aiko mana sakonnin gaishe-gaishe da sada zumunta, amma mun kasa karanta sakonninsu duka, sabo da karancin lokaci, amma muna godiya a gare su duka, da fatan za ku ci gaba da aiko mana sakonninku. (Lubabatu)