Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-13 22:02:49    
Murnar ranar matan duniya

cri
A farkon shirinmu na yau, muna son taya masu sauraronmu mata murnar ranarsu, wato ranar mata ta duniya, wadda ta zo a ran 8 ga wata. A nan kasar Sin, an gudanar da wannan ranar mata ta hanyoyi daban daban. Hadaddiyar kungiyar matan Sin ta kira taro a nan birnin Beijing, don murnar cika shekaru 99 da aka fara ranar mata ta duniya, kuma wakilan mata da suka zo daga bangarori daban daban na Sin da jakadun kasashen waje a Sin da mata 'yan diplomasiyya da masana mata na waje da dai sauransu 1500 sun halarci taron. A gun taron, shugabar kungiyar, Madam Chen Zhili ta isar da fatan alheri ga matan Sin da na kasashen duniya baki daya. To, masu sauraro, ku fa, me kuka yi domin murnar ranar, muna fatan za ku rubuto mana su?

To, bayan haka, zan fara shirinmu na yau ne da tarihin ranar matan duniya, domin amsa tambayar Habiba Ibrahim, daga garin Gumel, jihar Jigawa, tarayyar Nijeriya.

Ran 8 ga watan Maris na kowace shekara rana ce ta matan duniya, wadda kuma ke da tsawon tarihi na kusan shekaru 100. A ran 8 ga watan Maris na shekarar 1909, ma'aikata mata a birnin Chicago na kasar Amurka sun yi yajin aiki da zanga zanga don neman 'yanci da daidaici, kuma sun bayyana bukatunsu na siyasa da na tattalin arziki, ciki har da samun ikon zabe da na aiki cikin awa takwas a kowace rana da kara albashinsu da sauransu. Yajin aiki da zanga-zangar da suka yi sun nuna wa duniya karfin mata, kuma kiransu ya sami amsa da goyon baya daga matan duk fadin duniya. Sa'an nan, a shekarar 1910, wakilan mata da suka zo daga kasashe 17 sun halarci taron wakilan matan duniya a karo na biyu, inda aka amince da shawarar da madam Klara Zetkin, sakatariyar hadaddiyar kungiyar dimokuradiyya ta matan duniya ta gabatar game da tsai da ranar 8 ga watan Maris a matsayin ranar mata ma'aikata ta duniya, kan yunkurin karfafa hadin kan mata da nemo musu 'yanci da zaman daidaici.

A shekarar 1911, karo na farko ne kasashen Amurka da Jamus da Austria da Denmark da Switzerland suka gudanar da bikin tunawa da ranar, kuma daga baya, bikin ya fara samun karbuwa daga kasashen duniya.

A nan kasar Sin, a ran 8 ga watan Maris na shekarar 1924, karo na farko ne mata daga bangarori daban daban sun yi taron tunawa da ranar mata. Bayan kafuwar sabuwar kasar Sin, gwamnatin kasar ta tsai da ran 8 ga watan Maris a matsayin ranar mata.

A duk duniya kuma, a shekarar 1977, a hukunce ne babban taron MDD ya tsai da ran 8 ga watan Maris a matsayin ranar hakkin mata da zaman lafiyar duniya".

A duniyar yanzu, matsayin mata ya dagu sosai, kuma mata na ta kara taka muhimmiyar rawa a fannonin siyasa da tattalin arziki da al'adu da zaman al'umma da dai sauran fannoni daban daban.

Matan Afirka ma suna ta kara taka muhimmiyar rawa a fannoni daban daban na Afirka, har da na duniya baki daya. Cikinsu kuwa har da Anna Tibaijuka, wadda ita ce mataimakiyar babban sakataren MDD kuma shugabar zartaswa ta hukumar matsugunan jama'a ta MDD, da Ngozi Okonjo-Iweala, zaunanniyar mataimakiyar shugabar bankin duniya, wadda ta taba kasancewa ministar kudi da ministar harkokin waje ta Nijeriya, da Asha-Rose Migiro, wadda ita ce mataimakiyar babban sakataren MDD, kuma a cewar babban sakataren MDD, Ban Ki-moon, "ita jagora ce da ke samun girmamawa". Bayansu, akwai kuma shugabar kasar Liberia, Ellen Johnson-Sirleaf, wadda ita ce zababbiyar mace shugaba ta farko a tarihin nahiyar Afirka. Wadannan fitattun mata suna kokarin neman cigaban Afirka, kuma bisa karfinsu ne suka kawo wa Afirka albarka. Bisa ga kwanciyar hankalin siyasa da saurin bunkasuwar tattalin arziki a Afirka, za a sami karin mata da ke taka muhimmiyar rawa a fagen Afirka, har ma da na duniya.

To, amsarmu ke nan ga malama Habiba Ibrahim, kuma da fatan kin gamsu da ita.

Bayan haka, mun kuma sami sakon Email daga wajen Ibrahim A.Ahmed daga Yola, jihar Adamawa, tarayyar Nijeriya, inda a cikin sakon, ya ce, "ni de mai sauraron ku ne ayau da kullum amma wannan shi ne sakona na fari. Amma ba tare da bata lokaci ba, ina jinjina a gare ku sabo da ainihin shirye-shiryen da kuke gabatarwa na ilimantarwa da nishanantarwa sabo da haka Allah ya taimake ku ya kuma kara muku hazaka."

To, amin amin, kuma mun gode kwarai, tun da wannan sako ne na farko da ka aiko mana, muna fatan za ka ci gaba da aiko mana su, mu dinga yi mu'amala da juna, da fatan Allah ya karfafa dankon zumunci a tsakaninmu.

Bayan haka, mun kuma sami sakonnin gaisuwa daga Nasir Nusha da sauran wadanda ba mu yi tsammanin karanta sakonninsu duka ba, sabo da karancin lokaci, amma muna godiya gare su duka, kuma Allah ya bar zumunci a tsakaninmu. (Lubabatu)