Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-12 20:52:56    
Ya kamata a sa muhimmanci kan yanke hukunci cikin adalci

cri
A ran 12 ga wata da safe, 'yan majalisar wakilan jama'ar kasar Sin na jihar Ningxia ta kabilar Hui mai cin gashin kai sun ci gaba da tattaunawa kan rahotannin aiki da kotun koli da kuma hukumar koli ta gabatar da kararraki na kasar Sin suka bayar, inda suka bayyana yabo sosai da yadda otun koli da kuma hukumar koli ta gabatar da kararraki suka iya gabatar da kasancewar abubuwa marasa kyau a cikin ayyukan shari'a lokacin da suke gabatar da ayyukan da suka gudanar a cikin shekarar da ta gabata.

'Yan majalisar kuma sun nuna cewa, wani abu mafi tsanani a cikin dukkan munanan abubuwan shari'a shi ne ba a iya yanke hukunci yadda ya kamata ba a wasu lokuta.

Ma Ruiwen, mataimakin shugaban zaunannen kwamiti na majalisar wakilan jama'ar jihar Ningxia ya bayyana cewa, kamar yadda wani masani ya taba bayyana cewa, illar da yanke hukunci ba cikin adalci ba ya yi a wani karo ta fi aikata laifuffuka har sau 10 tsanani. Dalilin da ya sa haka shi ne sabo da aikata laifuffuka ya karya dokoki, wanda ya yi kama da gurbata ruwan kogi, amma yanke hukunci ba cikin adalci ba yana lalata dokoki, wanda ya yi kama da gurbata da mafarin kogi. Sabo da haka yanke hukunci cikin adalci wani tushe ne wajen samun daidaito a zaman al'umma, ya kamata aikin warware wannan matsala ya zama wani muhimmin aiki da kotun koli da hukumar koli ta gabatar da kararraki za su gudanar a cikin dogon lokaci. Kuma Mr. Ma ya ba da shawarar cewa, ya kamata a kyautata tsarin alkalai da kuma masu gabatar da kararraki da kuma daukar nagartattun matasa masu kwarewa sosai a wannan fanni, hakan zai taimaka wjen magance cin hanci da rashawa da kuma warware matsalar yanke hukunci ba cikin adalci ba.