Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-11 17:12:06    
Wakar da ke da lakabin "furen da ke sheki tare da wakar da ke jawo mana alheri da sa farin ciki"

cri

"Hua Er" wata wakar tsaunuka ta musamman ce da aka rera da harshen Han kuma take yaduwa a wuraren da wasu kabilun kasar Sin wato kabilun Han da Hui da Dongxiang da Tu da Sala da Bao'an da Tibet da Yugu da Mongoliya da sauransu suke zaune a cunkushe wadanda suka hada da lardin Gansu da jihar Ningxi da Xinjiang da lardin Shanxi na kasar Sin, a kasashen waje, wakar ta kuma yadu a kasashen Hazakhstan da kirghistan da Uzbekstan. Game da wace shekara ce da aka samu wakar da ke da lakabin "Hua Er", masu nazarin wakar suna da bambancin ra'ayi, amma dukkansu sun bayyana cewa, an sami irin wakar ne a kalla a karshen daular Qing ta kasar Sin.

A da, rera wakar "Hua Er" ya zama wata muhimmiyar hanyar jin nishadi da manoma na arewa maso yammacin kasar Sin suke bi. A lokacin da manoma suke aikin noma ko aikin kiwon dabbobi ko suke hutawa wajen yawon shakatawa su kan rera irin wannan waka. Wata tsohuwa mai suna Li Fenglian ta jihar Ningxia tana rera wakar cikin shekaru da dama. Ta gaya wa manema labaru cewa, a lokacin da take budurci, ta kan rera wakar, manoma suna aiki suna rera irin wannan waka don rage nauyin aiki. In mutane da yawa suka taru gu daya, to su kan rera wakar daya bayan daya ko cikin tarayya, game da abubuwan da ake rerawa, babu ka'idojin da aka bi, sai abubuwan da ake tunawa ake rera su yadda ake ga dama.

Akwai wata wakar da ke da lakabin "wakar walima" da ake rerawa tamkar yadda wakar "Hua Er" da ake rerawa take. Wakar ita ce wakar kabilar Hui kawai. A kan rera wakar a yayin bikin aure don kara farin ciki da annashuwa ga mutanen da ke halartar bikin. Abubuwan da ke cikin wakar sun yi tamkar yadda aka bayyana al'amuran da suke gudana, kuma ana rera wakar tare da raye-raye, kai, wakar tana bayyana halin da ake ciki a wuraren da kanana kabilu suke zaune cikin nishadi da annashuwa. Wata wakiliyar majalisar ba da shawarwari ga harkokin siyasa ta kasar Sin mai suna Hong Meixiang ta bayyana wa manema labaru wasu abubuwa dangane da "wakar walima" , kuma ita da kanta ta rera wa manema labaru irin wannan wakar dangane da yadda wani saurayi mai sayar da kayayyaki ya nemi aure daga wata budurwa kyakyawa. To ga wakar da ta rera:

budurwar ta rera wa saurayin waka da cewa,mahaifana dukkansu ba su gida, me ya sa ka sayar da kayayyaki a nan?

Saurayin da ke sayar da kayayyaki ya amsa cewa, ina mahaifanki suke ? Me ya sa na zo na sayar da kayayyaki a nan, amma ban gan su ba?

Budurwar ta rera cewa, harkoki a gaba mahaifana, za su aurar da ni a watan Disamba na shekarar da muke ciki.

Sa'anan saurayin ya kira budurwar da ta zo ta sayi kayayyaki daga wajensa. Da budurwar ta sayi kayayyaki daga wajensa, sai saurayi ya dube ta sosai da sosai, kuma ya rera cewa, da kyau! da kyau ! da Kyau sosai, a watan Disamba na shekarar da muke ciki, zan aure ki.

Sai budurwar ta ji kunya sosai, ta koma gida, daga nan saurayi ya rera cewa, mai sayar da kaya yana jan rakumi ne kawai, don duba budurwa, sai ya je sayar da kayayyaki a nan, daga nan sai ya tafi yana talla .

A lokacin da ake aikin kiyaye abubuwan gargajiya na kananan kabilu, Hong Meixiang da abokanta suna yi kokari sosai . Wato sun taba zuwa kauyuka da ke kusan da iyakacin kasa don samun fasahar kago wakoki, a sa'I daya kuma, 'yan kananan kabilu suna maraba da su sosai, kuma suna kaunar al'adunsu na gargajiya sosai. Ta bayyana cewa, lokacin da muka sauka gidan 'yan kabilar Hui, sai suka dauke mu tamkar dangoginsu ne, abubuwan da suka yi mana sun burge mu sosai da sosai.

Amma malama Hong Meixiang ita ma ta nuna damuwa kan aikin kiyaye al'adun gargajiya na kananan kabilu da ake yi yanzu da kuma aikin gadonsu. Ta ce, alal misali, wajen aikin kiyaye wakar "Hua Er" da "wakar Yanxi", kulawar da ake yi bai kai na dagulewarsu ba. Hong Meixiang ta bayyana cewa, a cikin 'yan shekaru fiye da 20 da suka wuce, masana'antun kasar Sin sun sami bunkasuwa sosai, saboda haka wannan ya kawo tasiri ga zamantakewar al'umma da ke yin aikin noma . Manoma samari sun tafi sauran wurare don yin aikin ci rani, inda suke rera wakokin da ke iya yaduwa a ko'ina, hanyoyin jin dadi da nishadi da manoma suke bi sun sami sauyawa sosai, shi ya sa irin salon wakokin gargajiya ya gamu da babbar matsala , har ma yana neman bacewa. Hong Meixiang ta bayyana cewa, muhallin zamantakewar al'umma da na al'adu da na halittu da wakar "Hua Er" da "wakarYanxi" suke kasancewa dukkansu sun sami sauyawa sosai , har ma an kawo tasiri gare su daga kasashen waje. Wadannan abubuwa sun riga sun kawo cikas ga bunkasuwar irin wadannan wakoki na gargajiya.

Taruruka biyu da ake yi yanzu a nan birnin Beijing sun mai da hankali sosai ga kiyaye al'adun gargajiya na kananan kabilu da yi gadonsu, wakilan tarurukan biyu sun bayar da shawarwari da yawa ga yadda za a kiyaye al'adun gargajiya na kasar Sin. Hong Meixiang ta bayyana cewa, a gun taron majalisar ba da shawarwari kan harkokin siyasa da ake yi yanzu a nan birnin Beijing, wakilai da yawa sun gabatar da wani shiri, inda suka nuna cewa, ya kamata kowace kabila ta kafa gidan baje kolinta, in hakan za a yi, to tabbas ne nagartattun al'adun al'ummar kasar Sin za su kara haske a idon jama'ar duniya.

Yanzu, kasar Sin ta riga ta kafa tsarin kiyaye al'adu, kuma ta tsara ranar yin aikace-aikacen kiyaye kayayyakin al'adun gargajiya. Amma an bayyana cewa, ya kamata a kara saurin kafa dokar kiyaye abubuwan tarihi na gargajiya na al'adu ba kayayyaki ba, muhimmancin aikin shi ne kare al'adun kananan kabilu, kuma ya kamata gwamnati ta kara zuba jari don kiyaye wadannan kayayyaki.(Halima)