Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-11 14:51:51    
Kasar Masar ta yi iyakacin kokarin binciko kayayyakinta na tarihi dake kasashen waje

cri
A matsayin kasar dake da dogon tarihi, Masar tana da kayayyakin tarihi masu daraja da yawa, amma sakamakon yake-yake da laifukan fasa kwauri, kayayyakin tarihi masu dimbin yawa sun bace a kasashen waje. A shekarun baya, kasar ta kara kokarin binciko wadannan kayayyakin tarihi kuma ta samu sakamako mai kyau.

Wani jami'in hukumar kula da kayayyakin tarihi ta kwamitin kayayyakin tarihi na kasar Masar Mustafa ya ce, a shekarun baya, kasar ta kara ganin muhimmiyar ma'anar aikin binciko kayayyakin tarihi, haka kuma, ta gudanar da wannan aiki ta hanyoyi daban daban.

Mustafa ta gabatar da cewa, babban aikin hukumar kula da kayayyakin tarihi shi ne gano kayayyakin tarihi na Masar dake kasashen waje. Bugu da kari, hukumar ta yi ta dudduba shafuffukan internet fiye da 40 da ke yin cinikin kayayyakin tarihi a duniya, da zarar ta ga kayayyakin tarihi na Masar da ake sayarwa ko nunawa, sai ta tuntubi mutanen dake da wadannan kayayyakin tarihi, kuma ta neme su gabatar mata da takardar shaida.

A sa'I daya kuma, ofisoshin jakadanci na kasar Masar dake kasashe daban daban suna gudanar da aikin gano kayayyakin tarihi, suna zura ido sosai kan ayyukan sayar da kayayyakin tarihi na Masar.

Mustafa ya ce, da zarar an tabbatar da hukumomi ko mutune dake ajiye da kayayyakin tarihi na Masar ba bisa doka ba, sai Masar ta matsa lamba ga kasashen da wadannan hukumomi ko mutane ke ciki ta hanyar diplomasiyya don mayar mata da kayayyakinta na tarihi. Idan wadannan kasashe suka ki amincewa da wannan aiki, Masar za ta dakatar da ayyukan musanyar ra'ayi tare da su a fannin hada kayayyakin tarihi da kuma yin nune-nune.

A cikin kasar Masar, 'yan sanda dake kula da ayyukan kayayyakin tarihi da wuraren yawon shakatawa suna da nauyin kiyaye kayayyakin tarihi. Idan suka ga an yi fashin kayayyakin tarihi, to, 'yan sanda za su hada gwiwa da kwamitin kula da kayayyakin tarihi don hana fitar da wadannan kayayyakin tarihi zuwa kasashen waje.

A shekarun baya, kasar Masar ta tuntubi dakunan ajiye kayayyakin tarihi na kasashe daban daban da bankunan sayar da su da kuma mutanen dake da su, inda ta sake mallakar kayayyakin tarihi da yawa daga kasashen Ingila da Switzerland da Amurka da Spain da kuma Holland, ciki har da "idon sarki" na Masar da aka samu a kasar Switzerland. An dauke wannan kayan tarihi ne daga mutum-mutumi na wani sarkin kasar Masar a shekarar 1972.

Shugaban kwamitin kula da kayayyakin tarihi na kasar Masar ya ce, binciko kayayyakin tarihi da suka bata, muhimmin aikin hukumomin adana kayayyakin tarihi ne. Ya kara da cewa, kamata ya yi, kasashen Masar da Sin su kara hadin gwiwa a fannin kare kayayyakin tarihi da suka bata. Ya yi kira ga Masar da Sin da Girka da kuma Mexico da dai sauran kasashen dake da dogon tarihi da su kira wani taron kasa da kasa don tattauna batun mayar musu kayayyakinsu na tarihi da aka dauke.

An labarta cewa, a cikin shekaru 6 da suka gabata, hukumar kula da kayayyakin tarihi ta Masar ta mayar da kayayyakin tarihi kimanin 5500 daga kasashen waje ta hanyoyi daban daban. Ban da wannan kuma, Masar za ta kara kyautata doka da kara kula da kayayyakin tarihi da kuma yin tuhumar wadanda suka aikata laifuffukan sayar da kayayyakin tarihi don komar da karin kayayyakin tarihi na Masar dake kasashe waje zuwa kasar.(Lami)