Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-11 09:07:03    
Kasar Sin ta nuna halayyar aikin natsuwa kan neman samun bakuncin gasar cin kofin duniya ta wasan kwallon kafa

cri
Kasar Sin kasa ce da aka fi samun yawan masu sha'awar wasan kwallon kafa a duk fadin duniya. A matsayin gasa ta matakin koli na wasan kwallon kafa, tun can da har zuwa yanzu masu sha'awar wasan kwallon kafa ta kasar Sin na fatan ganin gasar cin kofin duniya ta wasan kwallon kafa wato World Cup. Bayan da kasar Sin ta sami nasarar shirya gasar wasannin Olympic ta Beijing, runkunin wasan kwallon kafa na duniya sun zura ido kan ganin kasar Sin ta nemi samun damar karbar bakuncin gasar cin kofin duniya na shekarar 2018 ko kuma shekarar 2022. Wannan shi ne ya kasance burin dimbin masu sha'awar wasan kwallon kafa na kasar Sin. Amma abin ba zata shi ne bayan da bangaren kasar Sin da abin ya shafa ya sha yin nazari kan batun a tsanake, a karshe dai bai mika wannan roko ba.

Ran 2 ga watan Fabrairu da sassafe da karfe sifiri bisa agogon birnin Zurich, wa'adin karshe ne da hadaddiyar kungiyar wasan kwallon kafa ta duniya wato FIFA ta tsara kan mika bukatar neman samun damar karbar bakuncin gasar cin kofin duniya ta shekarar 2018 da ta shekarar 2022. Kasashe 11 na Asiya da Turai da Amurka da kuma Oceania sun mika bukatunsu, ciki banda kasar Sin.

Birnin Beijing, hedkwatar kasar Sin ya samu nasarar shirya gasar wasannin Olympic ta lokacin zafi a karo na 29 a shekarar bara, shi ya sa akasarin ra'ayoyin jama'a na duniya shi ne cewa kasar Sin za ta nemi shirya gasar cin kofin duniya ta wasan kwallon kafa. Sa'an nan kuma, dimbin masu sha'awar wasan kwallon kafa na kasar Sin su ma sun nuna fatan samun damar kallon wannan kasaitacciyar gasa a cikin gida. Duk kasashen duniya sun jira ganin mika wannan bukata cikin annashuwa da kasar Sin za ta yi. Dan haka rashin gabatar da roko da kasar Sin ta yi a yayin da wa'adin karshe ya cika ya ba wa kafofin watsa labaru da yawa a gida da wajen kasar Sin mamaki sosai. Wasu masu sha'awar wasan kwallon kafa na kasar Sin su ma sun nuna bakin ciki. He Huali, wani mai sha'awar wasan kwallon kafa na kasar Sin, kuma mazauni birnin Beijing ya gaya mana cewa,?Ni wani mai sha'awar wasan kwallon kafa ne. Ina matukar Alla-Alla wajen ganin kungiyar wasan kwallon kafa ta kasar Sin ta iya nuna gwanintarta a yayin gasar cin kofin duniya a cikin gidanmu tare da kallon gasanni na babban mataki da ke tsakanin kungiyoyin sauran kasashe. Gasar za ta samar wa masu sha'awar wasan kwallon kafa da yawa ainihin murnar da wasan kwallon kafa ke sakawa. Sa'an nan kuma, zan iya ganin 'yan wasan kwallon kafa taurari kuma kwararru masu yawa suna nuna fasaharsu a filin wasa, mu karfafa gwiwarsu a filin wasa kai tsaye. Dukkansu muna zura ido kan haka.?

Yaushe ne kasar Sin za ta iya karbar bakuncin gasar cin kofin duniya? Ma Dexing, mataimakin babban edita na jaridar wasannin motsa jiki na Mako-mako, wata kafar yada labaru ta kasar Sin da ta kware a wasanni yana ganin cewa, mai yiyuwa ne a shekarar 2034, kasar Sin za ta iya shiga takarar samun karbar bakuncin gasar cin kofin duniya. Mr. Ma ya ce,?A ganina, saboda mun rasa wannan dama, ba za mu iya samun irin wannan dama ba sai shekarar 2034. Ko da yake kungiyar FIFA ta yi watsi da tsarinta na da, wato shirya gasar cin kofin duniya bi da bi a dukkan nahiyoyin duniya, amma a yayin da ta tsai da kuduri kan wannan batu, ta kan nuna ra'ayin shirya gasar bi da bi a nahiyoyi. Yanzu ya kamata mu lura da wani muhimmin abu. Turai na matsayin cibiyar duniya ce a wasan kwallon kafa, shi ya sa wata kasar Turai ta kan shirya gasar cin kofin duniya a ko wadanne karo 3. Bisa halin da ake ciki a yanzu, mai yiwuwa ne kasar Birtaniya ce za ta shirya gasar a shekarar 2018, daga baya, wata kasar Asiya za ta shirya gasar a shekarar 2022, daga baya, sai wata kasar nahiyar Kudancin Amurka ko kuma nakiyar Arewacin Amurka a shekarar 2026. A shekarar 2030, gasar za ta koma ga wata kasar Turai. Shi ya sa a shekarar 2034, watakila kasar Sin za ta iya neman shiryar gasar.?

In mun yi nazari mai zurfi, za mu iya ganin cewa, kasar Sin tana nuna halayyar aikin natsuwa kan gasar cin kofin duniya.

Neman samun damar karbar bakuncin gasar cin kofin duniya da kuma shirya ta sun hada da dimbin ayyuka. Saboda a kan shirya wannan gasa a birane 9 zuwa 12 na wata kasa ko kuma wani yankin da ya sami damar shiryawa, shi ya sa tilas ne a yi tunanin tsaron lafiyar masu sha'awar wasan kwallon kafa dubbai da ba su wurin kwana da zirga-zirga. Za a bukaci ayyukan shiryawa filla-filla na dogon lokaci. Samun nasarar gudanar da gasar wasannin Olympic ta Beijing ya shaida cewa, kasar Sin na da kwarewar shirya gaggarumar gasar duniya. Amma shi ma ya nuna wa kasar Sin sosai cewar, a kan yi ayyuka masu tarin yawa domin tabbatar gudanar da gasa yadda ya kamata. A kwanan baya, Cui Dalin, mataimakin shugaban hukumar wasannin motsa jiki ta kasar Sin ya bayyana cewa, neman samun bakuncin gasar cin kofin duniya da gudanar da ita sun yi wuya sosai kamar yadda samun bakuncin gasar wasannin Olympic da gudanar da ita. Inda ya ce,?Bisa nazarin da muka yi cikin natsuwa, mun iya gano cewa, ko da yake gasar cin kofin duniya ta shafi wani irin wasa ne kawai, amma wahalar neman samun bakuncinta ta yi daidai da ta neman samun damar shiryar gasar wasannin Olympic. A sakamakon a kan gudanar da gasar cin kofin duniya a wurare da dama, ta haka masu sha'awar wasan kwallon kafa za su yi zirga-zirga a tsakanin wadannan wurare. Ana bukatar nazari da tabbatar da batutuwa masu yawa yadda ya kamata.?

Samun nasarar gudanar da gasar cin kofin duniya ta wasan kwallon kafa ba kawai yana iya kyautata surar kasar da ta sami damar karbar bakunci ba, har ma yana iya kawo mata babban zarafin raya tattalin arzikinta. Su ne dalilan da suka sa kasashe da yawa suke son samun damar gudanar da wannan gasa da farashi mai tsada. Duk da haka Xiong Xiaozheng, shehun malami na jami'ar ilmin wasannin motsa jiki ta Beijing yana ganin cewa, a daidai domin muhimmancin da wannan gasa ta duniya take da shi, shi ya sa kafin a gabatar da roko, tilas ne a bukaci a yi tunani sosai da sosai da kuma share fage yadda ya kamata. Bisa halin da kasar Sin ke ciki a fannoni daban daban, yanzu ya fi dacewa ta shiga cikin gasar cin kofin duniya a maimakon shirya ta. Mr. Xiong ya ce,?In an gudanar da gasar cin kofin duniya a birane daban daban a duk fadin wata kasa, to, za a kara samun matsin lamba da kuma yawan kudaden gudanarwa. Muna da karfin gudanar da gasar. Amma wannan bai nuna cewa, mun sami lokaci mai kyau ba. A kasarmu, ana habaka bukatu a gida kan raya tattalin arziki sosai, saboda haka, ba mu bukatar yin amfani da damar shirya irin wannan kasaitacciyar gasar, kamar gasar cin kofin duniya domin raya tattalin arzikinmu. Ban da wannan kuma, bisa ayyukan da gwamnatinmu ta tsara a harkokin wasanni, yanzu lokaci bai yi ba na mu gudanar da gasar cin kofin duniya ta wasan kwallon kafa.?

A shekarun nan da suka wuce, kungiyar wasan kwallon kafa ta maza ta kasar Sin ba ta sami sakamako mai kyau a cikin gasannin duniya ba. Wannan shi ne wani dalili na daban da ya sa kungiyar wasan kwallon kafa ta kasar Sin ta yi watsi da rokon samun damar karbar bakuncin gasar cin kofin duniya. A 'yan kwanaki, Nan Yong, mataimakin shugaban kungiyar wasan kwallon kafa ta kasar Sin ya nuna cewa, inganta aikin horar da matasa da yara da bunkasa hadaddiyar gasar wasan kwallon kafa ta kasarmu domin kyautata karfin kasar Sin na yin gogayya a cikin gasannin wasan kwallon kafa ta duniya daga dukkan fannoni suna matsayin muhimmin aiki da rukunin wasan kwallon kafa na kasar Sin zai yi cikin gaggawa.

Watakila in karin matasa da yara sun nuna sha'awa kan wasan kwallon kafa da kuma shiga cikinsa a kasar Sin, to, lokaci ya yi da kasar Sin za ta bude kofarta ga shirya wannan gasar cin kofin duniya, wadda ke matsayin gasar wasan kwallon kafa ta matsayin koli a duk duniya.(Tasallah)