Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-10 21:46:45    
Jin dadin wasa da dusar kankara a Jilin

cri
Masu sauraro, barka da war haka! Da zarar lokacin hunturu ya yi a arewa maso gabashin kasar Sin, sai dusar kankara ta dinga sauka. A cikin shirinmu na yawon shakatawa a kasar Sin, mun ba ku wata takardar gayyata daga lardin Jilin da ke arewa maso gabashin kasar Sin da zummar mu gayyace ku dan jin dadin kallo da ku yin wasa da dusar kankara tare.

A yammacin Jilin, kogin Songhuajiang da na Nenjiang sun hadu a nan daga arewa da kuma kudu, ta haka mun sami wani tabki mai fadin murabba'in kolimita 420, sunansa Chaganhu. A karshen ko wane watan Disamba, fuskar tabkin ta kan daskare, wadda zurfin kankarar ya kai mita 1 zuwa 2. Masu kama kifi da kakannin-kakanninsu suka fara zama a wurin, su kan fara haka kankara domin kama kifi ta hanyar da ta fi dadewa a duk duniya. Wannan shi ne al'adun kama kifi da masu ilmin al'adar gargajiya suka mayar da shi tamkar al'ada daya tilo na kama kifi da ke kasancewa har zuwa yanzu tun daga can da. Ta irin wannan hanyar zaman rayuwa ne ake iya kiyaye al'adun dan Adam, wadda kuma take matsayin tarihin al'ummar Sin da ke zaune a arewacin kasar a fannin zaman rayuwa.

Tabkin Chaganhu na cikin gundumar Qianguo ta kabilar Mongolia mai cin gashin kanta a arewa maso yammacin lardin Jilin. Yau da shekaru fiye da dubu 1, mazauna wurin suka fara kama kifi a lokacin hunturu.

A ko wace shekara, a gabannin kama kifi, masunta da ke zaune a kusa da tabkin Chaganhu kan shirya bikin nuna girmamawa ga tabkin da kuma tada tsimin ragar kama kifi da zummar kawo wa mazauna wurin zaman rayuwa mai dadi. Masu kama kifi su kan sa sukari da gasasshiyar shinkafa da 'ya'yan itatuwa da busasshiyar madara da sauran abubuwan nuna girmamawa kan fuskar tabkin da ya daskare, kuma za su haka wani rami a kanta domin shigar da ragar kama kifi. Ban da wannan kuma, su kan kunna kyandil da turare. Bayan da Lama suka yi rawar Chama ta gargajiya tare da karanta akibar addinin Buddha da suka yi domin korar dodo, mutane suna jefa abubuwan nuna girmamawa cikin ramin, mai jagorar masu kama kifi yana kara karanta kalmomin nuna girmamawa ga tabkin.

Bayan da suka sha giyar karfafa gwiwarsu, masu kama kifi su kan hau kekunan doki, su kama hanyarsu ta kama kifi.

Tsawon ragar kama kifi da masunta su kan yi amfani da ita a tabkin Chaganhu a lokacin hunturu ya wuce mita dubu 3, kuma fadinta ya wuce mita 2. Da misalin karfe 4 na sassafe, masu kama kifi suna huda kankara suna haka rami na farko a fuskar tabkin bisa umurnin mai jagorarsu. Daga baya sun haka ramuka daya bayan daya a ko wane tsayin mita 15 a kan fuskar tabkin, su kuma shata wata shiyya mai da'ira kuma mai fadin murabba'in kilomita 1 a kewayen ko wane rami da suka haka don jefa ragar. Sa'an nan kuma, sun yin amfani da sanda sirirriya mai tsayin mita 18 zuwa 20, su shigar da ragar da wannan sandar sirirriyar cikin ramukan da suka haka.

Tare da yin waka da masu kama kifi suka rera da babbar murya, a wurin da ke da nisan daruruwan mita a tsakaninsa da rami na farko, dawaki 4 suna ta jan ragar kama kifin. Sannu a hankali, ragar kama kifin mai tsayi ta fito daga rami tare da rayayyun kifaye. Wadannan kifayen da aka fitar da su daga karkashin fuskar tabkin suna tsalle-tsalle a kan fuskar tabkin da ya daskare, nan take ana iya ganin dimbin kifaye masu rai da ke tsalle-tsalle a kan fuskar tabkin. Wannan ya kan jawo yin ihu daga matafiya."Na zo nan ne cikin motar haya ta taksi. Na taba yin ziyara a wurare da yawa a kasarmu, amma ba safai na kan ga irin wannan ba. Ya sha bamban da saura sosai.""Wannan ya ba ni mamaki sosai. Na taba ji, amma ban taba gani ba. Wannan yana nuna kasaita kwarai."

Akwai kifaye masu nau'o'i fiye da 70 da suke cikin tabkin Chaganhu. Kayan abincin da aka dafa da kifaye da aka kamo daga wannan tabki yana da dadin dandano kuma yana amfanawa wajen kiwon lafiya.

Ko da yake ba kamar yadda harkar kama kifi ta iya kafafa gwiwar mutane sosai ba, amma wasan Skiing a kan duwatsu na sa sha'awa ga wadanda suka kai wa Jilin ziyara. A duk fadin lardin Jilin, ko ina ana iya ganin filayen wasan Skiing wato gudu a kan faifan musamman ko allo a tsakanin duwatsu. Filayen wasan Skiing a tsakanin duwatsu iri-iri guda 70 ko fiye da suka hada da wanda aka gina a babban dutse na Chang Bai Shan kuma sun hada kansu domin sanya lardin Jilin ya sami kyakkyawan suna, wato al'jannar masu sha'awar wasan Skiing a tsakanin duwatsu.

Yanzu wasan Skiing a tsakanin duwatsu ya riga ya zama wasan mazauna a birnin Changchun. Bayan kwanaki 10 na tsakiya na ko wane watan Nuwamba, dukkan filayen wasan Skiing a tsakanin duwatsu cike suke da murna da kuma ban dariya. A kan hanyoyin wasan Skiing a tsakanin duwatsu masu tsayi da kuma marasa tsayi, masu kishin wasan da ke da fasahohi iri daban daban kan nuna gwanintarsu sosai.

"Wannan shi ne karo na farko da na yi wasan Skiing a tsakanin duwatsu. Na ji matukar farin ciki da zuwan nan. Ina murna sosai saboda ganin dusar kankara mai yawa haka. Wasan Skiing a tsakanin duwatsu ya sa ni zumudi kwarai da gaske."

Masu sauraro, bayan da kuka yi wasan Skiing a tsakanin duwatsu, to, za ku iya yin wasa da kayan wasa na Sliding Board da aka kafa da dusar kankara. Akwai kayayyakin wasa na Sliding Board na dusar kankara masu tsayin mitoci da dama. A kansu kuma, a kan ji ihu da kuma dariya duka.

Masu sauraro, in kuna son kallon dusar kankara da kuma yin wasa da ita, to, babu tantama babban dutse na Chang Bai Shan da ke kuriyar lardin Jilin a gabas zabi ne mafi kyau a gare ku. Bayan da kuka tuka mota har na tsawon awoyi 4 daga birnin Changchun, babban birnin lardin Jilin, kun iya ganin farar dusar kankara da ke rufe duk babban dutse. A lokacin hunturu, an bude kofar babban dutse na Chang Bai Shan, ta haka masu yawon shakatawa kan iya hangen manyan duwatsun dake kewayen babban dutse na Chang Bai Shan daga fuskar tabkin Tianchi da ke babban dutse na Chang Bai Shan, kazalika kuma sun iya shiga cikin tabkin ruwan dumi tare da ganin saukowar dusar kankara, su kuma iya ratsa gandun daji da ke karkashin kasa da zummar kallon rassan itatuwa da dusar kankara ke rufe su a bakin rafuka."Na zo nan ne daga birnin Guangzhou da ke kudancin kasar Sin kai tsaye, shi ya sa ya kasance da babban bambanci a ganina. Abubuwan da nake gani a wurin sai ka ce abubuwan da ke cikin almara.""Ina tsammani cewa, dukkan abubuwan da muke gani na sha bamban sosai. Ban gane sosai ba, me ya sa a wani gefe, akwai ruwan kankara, amma a wani na daban kuma, akwai ruwan dumi."

Meng Fanying, mataimakin shugaban hukumar kula da yawon shakatawa ta kwamitin hula da babban dutse na Chang Bai Shan ya yi mana karin bayanin cewa,"A halin yanzu, ko a cikin kananan motoci, ko kuma a cikin manyan motoci masu dauke da fasinjoji, masu yawon shakatawa suna iya kai ziyawa ga ko wane wurin yawon shakatawa a babban dutse na Chang Bai Shan ba tare da wata matsala ba. Bugu da kari kuma, masu yawon shakatawa suna bukatar biyan rabin kudin kan na lokacin zafi a fannonin cin abinci da yin hayar dakin kwana da kuma harkokin nishadi."

Ban da wannan kuma, wurin shan iska na wasan Skiing a tsakanin duwatsu na duniya da aka bude kofarsa a gindin babban dutse na Chang Bai Shan a yamma shi ne filin wasan Skiing a tsakanin duwatsu da ba mutane suka gina ba daya tilo a kasar Sin, kuma ya fi girma a Asiya. Wannan filin wasa ya kara sanya babban dutse na Chang Bai Shan ya cike da karfi.

"Wasan Skiing a tsakanin duwatsu ya iya sa mu murna a lokacin da muke tafiya a tsakanin duwatsu. Abu mafi muhimmanci shi ne morewa idonmu da kallon ni'imtattun wurare. Sai a babban dutse na Chang Bai Shan kawai, muna iya tafiya cikin matukar murna tare da kallon wurare masu kyan gani."

A lardin Jilin, iska mai ni'ima da ruwan da ke gudana da kuma samun tsit a manyan duwatsu na iya nuna muku jituwar da ke tsakanin mutane da muhalli.