Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-10 18:18:36    
Kasar Sin ta fi mayar da hankali kan ba da tabbaci da kyautata zaman rayuwar jama'arta a wannan halin da ake ciki na fuskantar matsalar kudi ta duniya

cri
Bisa yaduwar matsalar kudi ta duniya, da fuskantar sabon kalubale da tattalin arzikin kasar Sin ke yi, a gun taron shekara-shekara da aka saba yi na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, wanda ake shiryawa a nan birnin Beijing, an fi mayar da hankali kan batun ba da tabbaci da kyautata zaman rayuwar jama'ar kasar.

'Dan majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, kuma shugaban sashen nazarin harkokin jama'a, da kwadago da tattalin arziki na cibiyar nazarin harkokin rayuwar jama'a ta kasar Mr. Cai Fang ya nuna cewa, ko za a iya warware matsalar ba da tabbacin taimako ga jama'a kamar yadda ya kamata, ko a'a, wannan ya zama wani muhimmin dalilin da ke da tasiri kan ko za a iya tabbatar da inganta bukatun gida, da ciyar da saurin bunkasuwar tattalin arziki gaba a nan kasar Sin, ko a'a. Mr. Cai Fang ya ce,

'Yanzu, jama'ar kasarmu sun fi son ajiye kudinsu a bankuna, amma ba sayen kayayyaki ba, muhimmin dalili shi ne, suna damuwa kan matsalolin da ke shafar makomarsu, ciki har da biyan kudi kan zaman rayuwarsu a lokacin da suka zama tsofaffi, da haduwa da ciwo, da rashin aiki yi, da kuma biyan kudin karatu na yaransu. Idan gwamnatinmu ta kara bayar da kudi, don shigar da mutane mafi yawa cikin tsarin ba da tabbacin taimako, to za a iya inganta sayen kayayyaki.'
A cikin rahoton ayyukan gwamnati da firayin ministan kasar Sin Wen Jiabao ya yi a ranar 5 ga wata, ana iya ganin cewa, ko da yake saurin bunkasuwar tattalin arzikin kasar yana ta raguwa a sakamakon matsalar kudi ta duniya, amma yawan kudin da za a yi amfani da su kan ba da tabbacin taimako ga jama'a, da ayyukan zaman rayuwar jama'a bai ragu ba, har ma ya yi yawa bisa na da. Mr. Wen Jiabao ya bayyana cewa, a cikin shekaru uku masu zuwa, kasar Sin za ta bayar da kudin Sin RMB biliyan 850, don bunkasa gyare-gyaren tsarin asibiti da kiwon lafiya na sabon zagaye.

'Za mu ciyar da yunkurin inganta babban tsarin ba da magani gaba. Za a tanadi mazaunan birane da kauyuka na dukkan kasar Sin cikin babban tsarin inshorar lafiya na ma'aikata na birane da garurruka, da babban tsarin inshorar lafiya na mazaunan birane da garurruka, da kuma sabon tsarin ba da magani ga manoma cikin hadin guiwa a kauyukanta, kazalika kuma, yawan mutanen da za a shigar da su cikin tsare-tsaren uku zai wuce kashi 90 cikin dari a cikin shekaru uku.'

Ban da batun asibiti, kuma an mayar da batun tallafa wa tsofaffi a kauyuka a matsayin muhimmin aiki na gaggawa a gaban gwamnatin kasar Sin. Yanzu, yawan tsofaffin da shekarunsu na haihuwa suka wuce 60 ya kai miliyan 153 a nan kasar Sin, wadanda kashi 70 cikin dari suke zama a kauyuka. Ko da yake a shekarar 1986 kasar Sin ta soma aiwatar da babban tsarin inshorar tsofaffi kan mutanen da suka yi ritaya a birane da garurruka, amma a kauyuka, yawancin tsofaffi suna zama dogarar da iyalansu.

'Dan majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, kuma shugaban hukumar kwadago da ba da tabbacin taimako ga jama'a ta lardin Anhui Mr. Zhu Yong ya ce, kyautata wannan tsari ya zama wani aiki ne na gaggawa.

'Yanzu, ya kamata mu kafa wani sabon tsarin inshorar tsofaffi a kauyuka da sauri, don warware wannan matsala, ta yadda za a shigar da manoma cikin tsarin ba da tabbacin taimako.'