Lokacin da tattalin arzikin duniya yake cikin tangarda sakamakon rikicin hada hadar kudi na duniya, kasuwannin cinikin motoci ma ba su tsira daga wannan rikici ba. A nahiyoyin Turai da Amurka na arewa da kasashen Japan da Koriya ta kudu wadanda suke kera kuma suke amfani da motoci sosai, an samu raguwar yawan motocin da ake saya ko sayarwa. Sakamakon haka, manyan kamfanonin samar da motoci na duniya sun soma zura idanunsu kan kasuwar kasar Sin, wato sabuwar kasuwar da ke cinikin motoci sosai. Dukkansu sun kyautata zantonsu kan kasuwar kasar Sin, kuma bi da bi sun bayyana cewa, za su zuba karin kudade a kasuwar kasar Sin. Sakamakon haka, kasuwar motoci ta kasar Sin tana kasancewa tamkar wata "tashar ruwa" da ke tinkarar rikicin hada hadar kudi na duniya ga manyan kamfanonin kera motoci na duniya.
Mr. Wang Dazong, shugaban kungiyar kasar Sin ta yin musaya kan harkokin mota a tsakanin kasashen Sin da Amurka, kuma babban direktan rukunin kamfanonin kera motoci na Beijing ya bayyana cewa, "Kasuwar kasar Sin muhimmiyar kasuwa ce ga kamfanonin kera motoci na duniya. Ko da yake muna kuma shan wasu wahalhalu kamar yadda sauran kasashen duniya suke sha yanzu, amma har yanzu kasuwar kasar Sin wata muhimmiyar kasuwa ce da ke jawo hankalin mutane a cikin kasuwannin duk duniya. Ko da yake mun ce, a cikin karshen watanni 3 na shekarar da muke ciki, saurin karuwar motocin da za a sayar a kasuwar kasar Sin zai ragu da kashi 25 cikin kashi dari, amma wannan yana almanta raguwar 'saurin karuwa' kawai, ba ya nuna yawan motocin da za a sayar zai ragu ba. Sabo da haka, tabbas ne manyan kamfanonin samar da motoci na duniya ba za su yi watsi da kasuwar kasar Sin ba, har ma za su mai da hankalinsu kan kasuwar kasar Sin sosai a nan gaba."
Jama'a masu sauraro, a shekara ta 2007, yawan motocin da aka kera a kasar Sin ya kai miliyan 8 da dubu 880. A waje daya kuma, yawan motocin da aka sayar a kasuwar kasar Sin ya kai kusan miliyan 8 da dubu 800. Sabo da haka, kasar Sin ta zama kasuwa mafi girma ta biyu bayan kasar Amurka a duk duniya. Bayan da muka shiga shekara ta 2008, sakamakon illar da rikicin hada hadar kudi na duniya ya kawo musu, yawan motocin da aka sayar a kasuwannin nahiyar Amurka ta arewa da Japan da Turai ya samu raguwa sosai. Sakamakon haka, dimbin motocin da ake bukata a kasuwar kasar Sin ya fi muhimmanci a gare su. Sabo da haka, kamfanonin samar da motoci na duniya sun kara saurin zuba jarinsu a kasuwar kasar Sin a kai a kai.
Ra'ayin Wang Dazong ya samu amincewa daga manyan kamfanonin kera motoci na duniya. Alal misali, ko da yake kamfanin General Motors da kamfanin Ford Motor na kasar Amurka ba su ji farin ciki ga yawan motocin da suka sayar a kasuwar kasar Amurka ba, amma yawan motocin da kamfanin Shanghai-General da kamfanin Chang'an-Ford na kasar Sin suka sayar a kasuwar kasar Sin yana karuwa cikin sauri har yanzu. A ran 17 ga watan Disamba na shekara ta 2008, sabuwar masana'antar harhada motoci ta Shanghai-General da kamfanin General Motors ya zuba kudin Sin yuan biliyan 2.7 ya kafa a birnin Shanghai ta soma aiki. Sakamakon haka, yawan sabbin motocin da kamfanin Shanghai-General zai kera a kowace shekara zai kai dubu 760. Sakamakon haka, kamfanin Shanghai-General ya zama daya daga cikin kamfanoni mafi girma wajen kera kananan motoci. Mr. Kevin E Wale, shugaba kuma babban direktan kamfanin Shanghai-General na kasar Sin ya bayyana cewa, kamfaninsa yana daidaita harkokinsa a kasuwar kasar Sin da kansa, kuma yana samun riba a kasar Sin.
Muhimman harkokin da kamfanin Ford Motor yake yi a kasar Sin su ne mota kirar "Ford na Chang'an" da mota kirar Jianglin, inda kamfanin Ford Motor na Amurka yake da takardun hannun jari 30%. Mota kirar Focus da ya samar a shekara ta 2007 ta jawo hankalin Sinawa sosai. Sabo da haka, kamfanin Ford Motor yana da imani ga kasuwar kasar Sin ta nan gaba. Mr. Liu Chunwei, mataimakin babban direktan kamfanin sayar da motoci kirar Chang'an Ford na kasar Sin ya ce, "Dalilin da ya sa nake da imani ga kasuwa shi ne ko da yake kasuwar da muke ciki yanzu ba ta yi kyau kamar yadda ake fata ba, amma har yanzu muna samun cigaba. A waje daya, mutane masu yawan gaske sun yi hasashen cewa, kasuwar kasar Sin za ta zama kasuwar motoci mafi girma a duk duniya a nan gaba. Sannan, ko da yake rikicin hada hadar kudi na duniya ya kawo illa sosai ga tattalin arziki, amma gwamnatin kasar Sin ta riga ta canja manufofin tattalin arziki, wato tana kokarin tabbatar da cigaban tattalin arziki daga dukkan fannoni. Ko ba da tallafin kudi ga kanana ko matsakaitan masana'antu, ko rage yawan harajin da ake bugawa kan masu saye da sayarwa, dukkansu suna tabbatar da habaka bukatu a cikin kasuwannin gida. Sabo da haka, tabbas ne bukatun da ake nema a kasuwar kasar Sin zai karu a nan gaba."
Kamar yadda kamfanin General Motors da kamfanin Ford Motor suke yi, kamfanin Mercedes-Benz wanda ya yi suna a duniya wajen samar da motoci masu inganci yana kuma kara zuba jari a kasuwar kasar Sin. Mr. Cai Gongming wanda ke kula da aikin sayar da motoci kirar Mercedes-Benz a kasar Sin ya ce, a cikin wasu lokuta na nan gaba, kamfanin Mercedes Benz zai ci gaba da kara karfin zuba jari a kasuwar kasar Sin domin tabbatar da ganin tambari Mercedes-Benz ya yi rinjaye a kasuwar kasar Sin. Mr. Cai ya ce, "Ina tsammanin cewa, abubuwa guda biyu suna kasancewa a bayyane sosai a duniya, wato ba za a iya canja muhimmancin kasuwar kasar Sin ga kamfanin Mercedes-Benz ba, kuma za mu iya fadin cewa, kasuwar kasar Sin tana kara samun muhimanci. Sabo da kasashen duniya suna da imani ga kasar Sin, kuma suna fatan kada rikicin hada hadar kudi na duniya ya kawo wa kasar Sin illa sosai. Bugu da kari kuma, za mu ci gaba da zuba karin jari a kasuwar kasar Sin, kuma ba za a iya canja halin da muke ciki wajen samun karuwa ba."
Ko da yake kamfanonin kera motoci na duniya suna cike da imani ga makomar kasuwar kasar Sin, amma a hakika dai yanzu yawan motocin da ake sayarwa a kasar Sin yana raguwa, kuma an soma samun sabbin sauye-sauye a kasuwar motoci ta kasar Sin, wato masu kashe kudi na kasar Sin suna mai da hankali kan motocin da suke iya tsimin makamashi, kuma ba za su gurbata muhalli ba. Madam Liu Xiaozhi, wadda ta taba kulawa da aikin sayar da motocin kamfanin General Motors a Taiwan ta ce, "Masana'antun kera motoci na kasar Sin suna da karfin neman cigaba. Za su iya samun lokaci wajen nazarin motocin da ke amfani da man fetur da gas tare, ko karfin batir, kuma za su iya yin nazari kan kayayyakin gyara mafi muhimmanci ga motoci. Yanzu za su iya yin amfani da damar da aka samu sakamakon rikicin hada hadar kudi domin yin nazari kan motocin da za su iya yin tsimin makamashi tare da kiyaye muhalli. Idan wani kamfani ya iya samun cigaba kan wadannan fannoni, tabbas ne zai samu nasara a kasuwar kasar Sin."
A hakika dai, wasu kamfanonin kera motoci suna yin irin wannan aiki. Kamfanin Chang'an-Suzuki, wato kamfani ne da kamfanin Suzuki Motor na kasar Japan wanda ya yi suna sosai wajen kera motoci masu kananan injuna ya zuba jari kuma ya kafa shi a kasar Sin. Mr. Tang Qing, wanda ke kulawa da aikin raya kasuwar motocin Chang'an-Suzuki ya ce, "A hakika dai, yanzu rikicin hada hadar kudi na duniya ya riga ya zama wata kyakkyawar dama ga motoci masu kananan injuna, kamar motocin Chang'an Suzuki. Yanzu gwamnatin wuri da gwamnatin tsakiya na kasar Sin dukkansu suna goyon bayan motoci masu kananan injuna. Bisa adadin da muka samu a shekara ta 2008, Sinawa sun soma amincewa da motoci masu kananan injuna a kai a kai. Sabo da haka, wannan wata kyakkyawar dama ce ga kamfaninmu."
Ko da yake wasu kamfanoni sun riga sun canja shirinsu na yawan motocin da za su sayar a kasar Sin a shekara ta 2009, amma har yanzu kamfanoni da yawa ba su canja shirinsu ba. Mr. Ren Yong, mataimakin babban direktan kamfanin kera mota kirar Dongfeng-Nissan na kasar Sin ya bayyana cewa, kamfaninsa ba zai canja shirinsa ba. Mr. Ren ya ce, "Burinmu da za mu cimma shi ne ya zuwa shekara ta 2012, yawan motocin da za mu sayar a kasar Sin zai kai fiye da dubu 550 a kowace shekara." (Sanusi Chen)
|