Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-08 21:54:51    
Samar wa manoma 'yan cin rani guraban aikin yi bayan da suka koma kauyukansu

cri

"A watan satumba na bara, na koma kauyenmu daga lardin Guangdong, kuma ga shi 'yan watanni sun wuce, har yanzu ban sami aikin yi ba, kuma ina cikin damuwa sosai." Xu Yonghua, wani manomin da ya zo daga kauyen da ke lardin Hebei na kasar Sin, shi ne ya fada mana haka. Yau da shekaru bakwai da suka gabata, ya bar gida domin cin rani, kuma ya sami aikin yi a wani kamfanin da ke birnin Guangzhou a mashigin teku na kasar Sin. Amma a shekarar da ta gabata, sakamakon matsalar kudi da ta galabaitar da kasashen duniya, kamfanin da ya yi aiki da shi ya lalace, shi ya sa ba yadda ya yi sai ya koma gida.

Alal hakika, manoma 'yan cin rani sama da miliyan 20 a nan kasar Sin suna cikin hali iri daya da na malam Xu Yonghuang. Abin da ya kara gurbata halin shi ne, sakamakon matsalar kudi, bayan sabuwar shekara bisa kalandar gargajiyar Sin, yawan kamfanonin da suke shirin daukar ma'aikata ya ragu da kashi 20%.

To, mene ne abin zai kawo wa tattalin arziki da zaman al'ummar kasar Sin? Kuma yaya Sin za ta tinkare shi? A gun taron shekara shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin da ake yi yanzu a nan birnin Beijing, batun samar wa manoma 'yan cin rani aikin yi ya zama abin da ya fi daukar hankulan mahalartan taron.

Mr.Cai Fang, shugaban sashen nazarin al'umma da kwadago na cibiyar nazarin zaman al'umma ta kasar Sin, yana ganin cewa, matsalar na iya kawo wa tattalin arziki da zaman al'ummar kasar Sin babbar illa. Ya ce,"A shekaru da dama da suka wuce, cin rani ya fi jawo wa manoma karuwar kudin shiga, idan sun rasa ayyukansu, ba shakka, kudin shigarsu zai rage saurin karuwa sosai. Ban da wannan, kashi 60% na manoma 'yan cin rani sun kasance 'yan shekaru kasa da 30, wadanda ke fi zuwa wurare daban daban, shi ya sa idan ba mu iya daidaita batun yadda ya kamata ba, to, zai iya kawo illa ga kwanciyar hankalin zaman al'umma."

Gwamnatin kasar Sin ma ya fara mai da hankalinta a kan batun, kuma ta dauki jerin matakai domin tinkararsa. A yayin da firaministan kasar Sin, Mr.Wen Jiabao ke ba da rahoto kan aikin gwamnati a ran 5 ga wata, ya yi bayani a kan yadda za a daidaita matsalar, kuma kamar yadda ya fada,"Ya kamata a fadada hanyoyin samar wa manoma 'yan cin rani aikin yi. Sa'an nan, ya kamata a yi amfani da kudaden jarin da gwamnati ta zuba da kuma manyan ayyukan da ake bunkasa wajen samar wa manoman guraban aikin yi."

A halin yanzu, kananan hukumomin kasar Sin na kokarin samar da guraban aiki ga manoma 'yan cin rani da suka koma gida. A lardin Sichuan da ke kudu maso yammacin kasar Sin, yanzu ana kokarin farfado da wurin daga girgizar kasa mai tsanani da ta auku a shekarar da ta gabata, wanda kuma ya samar da guraban aikin yi ga dimbin manoma 'yan cin rani da suka koma gida. A wasu larduna kuma, ana samar musu kudin tallafi, don ba su kwarin gwiwar raya sana'arsu.

A sakamakon matakan da aka dauka, dimbin manoman sun sake samun ayyukan yi masu gamsarwa. Amma duk da haka, madam Zhu Xueqin, wakiliyar manoma 'yan kwadago da ta zo daga birnin Shanghai ta yi hangen nesa ta ce, kamata ya yi gwamnati ta kara horar da manoma 'yan cin rani, ta ce,"Bisa tallafin gwamnati da muhimmancin da kamfanoni ke dora musu da kuma kokarin da manoma 'yan cin rani suka yi, mu manoma 'yan cin rani mu ma muna iya zama kwararru da ke da kyawawan fasahohi." (Lubabatu)