Meya fi daukar hankulanku kwanan nan? A nan kasar Sin, abin da ya fi jawo hankulan jama'a yanzu bai wuce manyan tarurruka biyu da ake yi a birnin Beijing ba, wato taron shekara shekara na majalisar ba da shawarwari kan harkokin siyasa ta Sin, wanda aka soma a ran 3 ga wata, da na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, wanda aka fara a ran 5 ga wata. Tarurrukan biyu sun kasance masu muhimmanci a harkokin siyasar kasar Sin, kuma ma iya cewa, ba ma kawai hankulan jama'ar Sin suke dauka ba, har ma kasashen duniya na zura ido sosai a kansu. Muna iya gano hakan ne daga yawan manema labarai da ke zuwa wajen tarurrukan biyu domin ba da rahotanni, wanda ya wuce dubu 3, ciki har da manema labarai na waje da yawansu ya kai sama da 800. Gidan rediyon kasar Sin ma ya tura wakilansa da yawa zuwa wajen tarurrukan, don su samo wa masu sauraronmu labarai da dumi-duminsu, ciki kuwa har da wakiliyar sashen Hausa, wato Kande, kuma tabbas ne kwanan nan kuna shan labarai da bayanai game da tarurrukan biyu daga nan sashen Hausa na CRI. Muna fatan kuna ji dadinsu, kuma za ku turo mana ra'ayoyi da kuma shawarwari.
Bayan haka, zan kawo muku takaitaccen bayani game da tsarin tarurruka biyu na kasar Sin, domin amsa tambayar masu sauraronmu, ciki har da Mudassir Yahaya daga Ikko, Nijeriya, da Safiya Muhammed daga Jalingo Taraba, Nijeriya, da dai sauransu, wadanda ke neman karin bayani game da manyan tarurruka biyu na kasar Sin, kuma da fatan kuna sauraro yanzu.
Tarurruka biyu, wato taron majalisar wakilan jama'ar Sin da na majalisar ba da shawarwari kan harkokin siyasa na kasar Sin, ko kuma NPC da CPPCC a takaice, sun kasance masu muhimmanci cikin tsarin siyasa na kasar Sin. Taron majalisar wakilan jama'ar kasar Sin hukumar koli ce ta kasar Sin, wadda ke tafiyar da ikon mulkin kasa, kuma tana kunshe da wakilan da aka zaba daga larduna da biranen da ke karkashin mulkin gwamnatin tsakiya kai tsaye da jihohi masu cin gashin kansu da yankunan musamman da kuma rundunar soja na kasar Sin, kuma wa'adin aikinsu ya kai shekaru biyar. A kan kira taron a kowace shekara, inda a kan yanke shawarwari kan manyan harkokin siyasar kasar Sin, ciki har da gyara tsarin mulkin kasar da tsara sauran dokokin kasar ko kuma gyara su da duba shirin bunkasa tattalin arziki da zaman al'umma da kuma shirin kasafin kudi da zabar shugabannin kasar da dai sauransu.
Sa'an nan, taron majalisar ba da shawarwari kan harkokin siyasa na kasar Sin muhimmin tsari ne na hadin gwiwar jam'iyyu da dama da yin shawarwari kan harkokin siyasa a karkashin jagorancin jam'iyyar kwaminis ta Sin, kuma muhimmiyar hanya ce ta bunkasa dimokuradiyyar gurguzu a cikin harkokin siyasa na kasar Sin. Taron dai na kunshe da wakilai daga bangarori daban daban, ciki har da jam'iyyar kwaminis ta Sin da jam'iyyu daban daban na dimokuradiyya da wadanda ba su cikin kowace jam'iyya da kungiyoyin jama'a da kananan kabilu daban daban da dai makamantansu, kuma wa'adin aikinsu ya kai shekaru 5. Hakkokin da ke kan taron sun hada da yin shawarwari kan manyan manufofin kasa da muhimman al'amuran da ke shafar fannonin siyasa da tattalin arziki da al'adu da zaman al'umma, da sa ido a kan yadda aka gudanar da tsarin mulki da dokokin kasa da manyan manufofi tare kuma da yadda hukumomin kasa da akawunansu ke aiki, da kuma ba da shawarwari da ra'ayoyi ga jam'iyyar kwaminis ta Sin da hukumomin kasa kan muhimman al'amuran da ke daukar hankulan jama'a.
To, bayaninmu ke nan kan tarurruka biyu na kasar Sin, da fatan ya taimaka wajen fadakar da masu sauraronmu a kan tsarin siyasa na kasar Sin.
Kada dai a shagala, amsoshin wasikunku ne kuke saurara daga nan sashen Hausa na CRI. Ba shakka, masu sauraronmu na mai da hankulansu kan tarurruka biyu da ake yi a kasar Sin, ga shi kuma sun aiko mana ra'ayoyinsu game da tarurrukan.
Salisu Muhammed Dawanau a Abuja, tarayyar Nijeriya, ya ce, "Na san za ku yarda da ni idan na ce halin da Duniya ke ciki yanzu yana cikin rudani musamman game da tabarbarewar tattalin arziki. Koda yake wasu kasashen sun dauki matakai wadanda watakila suna iya samun sa'ida game da wannan hali da suke cki. Alal hakika, zai yi kyau idan, a wadannan tarurruka biyu da za a gudanar, an tattauna batun harkar neman mafita game da wannan hali na rashin tabbas na gurbatar tattalin arziki.
Bayan haka, sai kuma batun samar wa matasa, wadanda suka kammala karatu, aikin yi. Da kuma dada zuba jari a gida da kuma wasu kasashen duniya musamman kasashe masu tasowa da kuma dada taimaka wa manoman kasar Sin da kuma dada inganta huldar diplomasiyya da wasu kasashen Duniya.
A gaskiya, wannan taro na iya duba abubuwa masu dimbin yawa da ya kamata mahalarta taron su yi la'akari da su wajen kara karfin kasar Sin a fannoni masu yawa, da ci gaban kasa da dai sauransu.
A karshe, ina fata wannan taro zai yi nasara wajen samun mafita ga kasar Sin da al'ummarta baki daya. "
Sai kuma Muhammad Sani Jume a Saminaka Lere Iga Kaduna, tarayyar Nijeriya, ya ce, "Ina fata shugabannin kasar Sin za su tattauna kan abin da ya shafi rayuwar talakawan kasar Sin da kuma kasashen duniya gaba daya."
To, muna godiya ga Salisu Muhammed Dawanau da Muhammed Sani Jume bisa turo mana ra'ayoyinku, kuma kamar yadda kuke fata, tinkarar matsalar kudi da duniya ke fama da ita da farfado da masana'antu da samar da guraban aikin yi da ba da tabbaci ga zaman al'umma duk suna cikin muhimman abubuwan da ake tattaunawa a gun tarurrukan biyu, kuma sashen Hausa na CRI zai ci gaba da kokarin kawo muku muhimman labarai da dumi duminsu daga wajen tarurrukan biyu, da fatan za ku kasance tare da mu a ko da yaushe. Bayan haka, muna kuma maraba da masu sauraronmu ku aiko mana sakonninku, ku fadi albarkacin bakunanku a kan wadannan tarurruka biyu. (Lubabatu)
|