Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-05 21:50:17    
Cin rani ya zama wata sabuwar hanya ga manoma musulmai na jihar Ningxia wajen kau da talauci da kuma samun wadata

cri

Jihar Ningxia wata jiha ce da aka fi samun dimbin musulmai a yammacin kasar Sin, tattalin arzikinta yana baya baya a gwargwado. Yawan manoman jihar ya kai fiye da miliyan hudu, amma rubu'i daga cikinsu ba su iya gudanar da ayyukan gona yadda ya kamata ba sakamakon rashin isassun gonaki da kuma mummunan yanayi. Sabo da haka matsalar samun guraban aikin yi ga wadannan dimbin manoma tana ta tsanata. Ganin irin wannan halin da jihar Ningxia ke ciki, gwamnatin jihar ta nemi wata sabuwar hanya don yakar talauci da kuma samun wadata, wato sa kaimi ga manoma da su dinga zuwa waje don yin aikin cin rani. To, a cikin shirinmu na yau, za mu gabatar muku da wannan batu.

"Yanzu zaman rayuwata ya samu kyautatuwa sosai, kin ga wannan sabon daki, na gina shi ne bisa kudaden da na samu ta hanyar zuwa cin rani. Haka kuma an gudanar da wata masana'antar sarrafa duwatsu da na kafa da kyau sosai a shekarar da ta gabata, a ko wace shekara ina iya samun kudaden Sin fiye da Yuan dubu 70."

Daga shigata gidan Ji Peigang, wani manomi musulmi na kauyen Shuangtang na gundumar Pengyang da ke kudancin jihar Ningxia, ya nuna mini sauye-sauyen zaman rayuwarsa sakamakon zuwa cin rani cikin matukar murna.

A cikin wannan sabon dakin da ya gina, ana iya ganin kayayyakin gida na zamani iri daban daban, ta haka ana iya gane cewa, lalle Ji Peigang yana jin dadin zamansa sosai.

Amma ya gaya mini cewa, kafin ya tafi waje don cin rani, zamansa ba kyau sam. Sabo da mummunan yanayi na wurin, kullum ba ya samu isashen abinci, balle ma jin dadin zaman rayuwa. Amma bayan da ya yi aikin ci rani, ya kau da talauci kuma ya kama wata hanyar samun wadata. Kuma ya kara da cewa, "A shekara ta 2002, na je masana'antar samar da bulo ta gundumar Yongning ta jihar Ningxia don cin rani, a ko wace shekara ina iya samun kudin Sin wato Yuan dubu 30. Bayan shekaru 5, na ajiye Yuan dubu dari. Na gina sabon daki da kuma kafa wata masana'antar sarrafa duwatsu, sabo da haka na kau da kangin talauci kwata-kwata."

Ana iya samun dimbin manoma masu cin rani kamar Ji Peigang a gundumar Pengyang. Chen Boxun, mataimakin shugaban hukumar kula da ayyukan samun guraban aikin yi ta gundumar Pengyang ya bayyana cewa, dalilin da ya sa haka shi ne sabo da a 'yan shekarun nan da suka gabata, gwamnatin gundumar Pengyang tana tsayawa kan raya sana'ar cin rani bisa matsayinta na daya daga cikin muhimman sana'o'i na gundumar wajen kara yawan kudaden shiga da manoma ke samu da kuma sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arzikin gundumar. Haka kuma bayan da manoma suka je ci rani, ba kawai yawan kudaden shiga da manoma suke samu yana karuwa ba, har ma ra'ayoyinsu suna sauyawa sosai. yanzu sun fara mai da hankali a kan raya ayyukansu a fannoni daban daban bisa kudaden da suke samu a maimakon gudanar da ayyukan gona kawai. Mr. Chen ya kara da cewa, yanzu manoma masu aikin cin rani na gundumarmu fiye da 100 sun riga sun komo gida don raya ayyukansu bayan da suka samu kudade a waje. Alal misali, wani manomi mai cin rani ya kafa wani kanti a cikin gundumarmu, ta haka 'yan gundumar fiye da 30 sun samu damar samun guraban aikin yi. Shi ya sa suka sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arzikin gundumar bisa wani matsayi."

Ban da samar da karfi, manoma musulmai na jihar Ningxia su ma suna bunkasa basirarsu ta iya harshen Larabci wajen cin rani a waje.

Gundumar Tongxin da ke tsakiyar jihar Ningxia wata gunduma ce da ake iya samun dimbin musulmai. Har kullum musulmai fararen hula suna da al'adar koyon karatun Alkur'ani mai girma da kuma harshen Larabci. Tare da ingantuwar cudanyar da ke tsakanin kasar Sin da kasashen Larabawa, ana ta bukatar mutane da suka iya harshen Larabci, sabo da haka aikin fassara da Larabci ya zama wata sabuwar hanya ce ga dimbin 'yan ci rani musulmai. Yang Hong, shugaban hukumar kula da ayyukan samun guraban aikin yi ta gundumar Tongxin ya bayyana cewa, "a 'yan shekarun nan da suka gabata, tare da bunkasuwar cinikayya tsakanin kasa da kasa yadda ya kamata, kasuwannin lardunan Zhejiang da Guangdong da Fujian da dai sauransu na kasar Sin suna jawo hankulan 'yan kasuwa Larabawa kusan dubu 300 a ko wace shekara. Sabo da haka manoma masu aikin fassara da Larabci na gundumarmu sun samu wata hanya wajen samun wadata."

Tian Shuhai, wani manomi musulmi ne na gundumar Haiyuan da ke kudancin jihar Ningxia, inda ake fama da talauci sosai. Ya gama karatunsa daga makarantar koyar da harshen Larabci ta gundumar Tongxin na jihar Ningxia a shekara ta 2003, yanzu yana gudanar da aikin fassara da Larabci a birnin Guangdong. Kuma ya gaya mana cewa, yana iya samun kudaden Sin yuan 5000 a ko wane wata. Ya kara da cewa, "Ni ne mutumin farko daga kauyenmu a koyon harshen Larabci. Ganin wadatar da na samu, yanzu mutane 8 na kauyenmu sun riga sun fara koyon harshen. Idan na samu isasshen kudi, zan bude wani kamfanin ciniki, ta yadda zan iya ba da taimako ga iyalaina da abokaina masu aikin fassara da Larabci."

Ya zuwa yanzu, yawan masu aikin fassara da Larabci 'yan asalin gundumar Tongxin da ke birnin Yiwu na lardin Zhejiang da birnin Guangzhou na lardin Guangdong ya riga ya kai 875, kuma mutane 26 suna gudanar da aikin fassara a kasashen Larabawa na shiyyar gabas ta tsakiya. Ta haka aikin fassara da Larabci ya riga ya zama wata muhimmiyar hanya ce wajen tura manoma musulmai zuwa waje don aikin ci rani.

Domin ci gaba da raya aikin tura masu fassara da Larabci zuwa waje, gundumar Tongxi ta sa kaimi ga bunkasa hukumomin horar da masu aikin fassara da Larabci. Kuma ya zuwa yanzu an riga an kafa makarantun koyar da harshen Larabci 7, inda yawan malamai masu koyar da harshen ya zarce dari, kuma yawan daliban da ke shiga kwas din horaswa ya kan kai fiye da 1000 a ko wace shekara. Shugaban makarantar koyar da harshen Larabci ta gundumar Tongxi a jihar Ningxxia Bai Shengyun ya bayyana cewa, "Aikin horar da masu aikin fassara da Larabci yana da ma'ana sosai, a fannin siyasa, ya kara inganta dangantakar da ke tsakanin Sin da kasashen Larabawa, kuma a fannin tattalin arziki, ba kawai masu aikin fassara da Larabci suna samun dimbin kudade ba, har ma sauran mutane sun samu wannan hanyar samun kudi ta hanyar tallafawar da suka bayar."

Chen Xiaojun, shugaban ofishin kula da harkokin 'yan kwadago na hukumar tabbatar da samun guraban aikin yi ta jihar Ningxia ya bayyana cewa, a 'yan shekarun nan da suka gabata, aikin sa kaimi ga manoma wajen ci rani ya samu babban ci gaba. Ya zuwa yanzu, kudaden da manoma suke samu ta hanyar cin rani ya riga ya kai kusan rabi daga cikin dukkan kudaden da suke samu. Kuma ya kara da cewa, "yanzu aikin cin rani na jihar Ningxia ya riga ya zama wata sabuwar hanya ga manoma wajen sauya hanyoyin samun guraban aikin yi bisa kwarewarsu da kuma ilminsu. Sabo da haka ya samar da wani dandalin wajen kafa kasuwar bai daya a fannin samar da guraban aikin yi ga masu aikin yi na birane da na kauyuka."(Kande Gao)