Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-05 16:47:40    
Kasashen duniya sun nuna damuwa kan bayar da sammacin kame shugaban kasar Sudan da kotun kasa da kasa ta yi

cri
A ranar 4 ga wata, kotun hukunta manyan laifuffuka ta kasa da kasa ta bayar da sammaci domin tsare shugaban kasar Sudan Omar Al-Bashir, akan tuhumarsa da take yi da aikata laifuffukan yaki da take hakkin bil'adama. Wannan dai shi ne karo na farko da wannan kotu ta yanke irin wannan hukunci akan wani shugaba dake kan karagar mulki. Ko bayar da umurnin cafke Omar Al-Bashir da kotun kasa da kasa ta yi zai taimaka wajen wanzar da zaman lafiya a Sudan, yana jawo hankalin kasa da kasa da damuwarsu.

A wanann rana, kotun hukunta manyan laifuffuka ta kasa da kasa ta sanar da cewa, Al-Bashir yana da hannu a aikata laifuffukan keta hakkin bil'adama guda 5 da na yaki guda 2 a yankin Darfur, amma mashawarcin shugaba Al-Bashir na Sudan ya ki amincewa da wannan sammaci. A ranar 3 ga wata kuma, Al-Bashir ya nuna cewa, kamata ya yi kasar Sudan ta dukufa kan kiyaye zaman lafiya da neman bunkasuwa a kasar, amma ba za ta maida hankalinta kan kowane kuduri da kotun kasa da kasa ta tsayar a kanta ba.

Bayan da kotun hukunta manyan laifuffuka ta kasa da kasa ta bayyana sanarwar bada sammacin kame Omar Al-Bashir, darurruwan mutane sun yi dandazo a titunan Khartoum, babban birnin kasar Sudan, don nuna adawa da hukuncin da kotun ta yanke. Masu zanga-zanga sun yi gangami a gaban kofar majalisar ministoci ta kasar, inda suka nuna tsayayyen goyon-baya ga Omar Al-Bashir, da zargi kotun kasa da kasa da ta yi shiga-sharo-ba-shanu cikin harkokin cikin gida na kasar Sudan.

A watan Yuli na shekara ta 2008, kotun laifuffuka ta kasa da kasa ta zargi Al-Bashir da aikata laifuffuka guda 10 masu alaka da laifuffukan kisan kare dangi a Darfur, da rokon kotun hukunta manyan laifuffuka ta kasa da kasa da ta bada sammaci don tsare Al-Bashir. Game da wannan batu, kasashen duniya suna fatan hukuncin da wannan kotu ta yanke zai amfana wajen kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a Sudan. Sakamakon shiga-tsakanin da Majalisar Dinkin Duniya, da kungiyar tarayyar Afirka, gami da kasashe makwabtan Sudan suka yi, gwamnatin Sudan ta bayyana fatanta na yin shawarwari tare da kungiyoyin 'yan adawa, don cimma kulla yarjejeniyar shimfida zaman lafiya mai dorewa a yankin Darfur. Amma akwai wasu kungiyoyin 'yan adawa wadanda suka ki sanya hannu kan wannan yarjejeniya, inda suka bukaci da a kara samun moriya, da raba iko da dukiyoyi a wannan yanki na Darfur.

Bayan da kotun hukunta manyan laifuffuka ta kasa da kasa ta bayar da sammacin cafke Omar Al-Bashir, kasashen duniya sun bayyana damuwarsu sosai. Kwanan baya, sakatare-janar na MDD Mista Ban Ki-Moon ya nuna cewa, tuhumar da kotun kasa da kasa ta yiwa Omar Al-Bashir, ba za ta taimaka ba wajen gudanar da yarjejeniyar shimfida zaman lafiya daga dukkan fannoni a kasar Sudan. A waje guda kuma, shugaba kwamitin kungiyar tarayyar Afirka Mista Jean Ping ya bayar da wata sanarwa a ranar 4 ga wata, inda ya jaddada cewa, bai kamata ba yanke hukunci ta hanyar shari'a ya jawo tsaiko ga yunkurin kiyaye zaman lafiya a Sudan. Akwai wasu kasashen Afirka kuma wadanda suka yi barazanar yin watsi da kujerun membobin kotun hukunta manyan laifuffuka ta kasa da kasa, don nuna matukar bacin-rai game da umurnin kama Omar Al-Bashir. Ministan harkokin wajen kasar Masar Ahmed Abul Gheit ya nuna cewa, abun da kotun kasa da kasa ta yi, zai lahanta yanayin tsaro da kwanciyar hankali a kasar Sudan, ya kuma yi kira ga kwamitin sulhun MDD da ya kira taron gaggawa, don tattaunawa kan jingine batun kama shugaba Omar Al-Bashir na Sudan.(Murtala)