Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-03 17:30:00    
An bude taron shekara-shekara na CPPCC a Beijing

cri

A ran 3 ga wata da yamma, an yi gagarumin bikin bude taron shekara-shekara na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin, wato CPPCC. A gun bikin, a madadin zaunannen kwamitin majalisar, Mr. Jia Qinglin, shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin ya bayar da wani rahoto game da ayyukan da majalisar CPPCC ta yi a cikin shekara daya da ta gabata, da kuma ayyukan da majalisar za ta yi a shekarar da muke ciki.

"Kowane mamban majalisar, a madadin zaunannen kwamitin majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin, na gabatar muku da wannan rahoto domin nazartarsu."

Ya kasance tamkar wata muhimmiyar hukumar ba da shawara kan harkokin siyasa da ke hada kan jam'iyyun siyasa da dama kuma ke karkashin jagorancin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, taron ba da shawara kan harkokin siyasa na jama'ar kasar Sin wata muhimmiyar hanya ce da ke shimfida dimokuradiyya irin ta gurguzu lokacin da ake daidaita harkokin siyasa a nan kasar Sin. Jam'iyyun siyasa daban daban da wasu nagartattun mutane na kabilu da na bangarori daban daban suna shiga harkokin siyasa da sa ido kan ayyukan da gwamnatin ke yi ta hanyar dimokuradiyya da kuma ba da shawararsu kan harkokin siyasa a gun taron domin bayar da muhimmiyar gudummawarsu. Hakikanin abubuwa sun shaida cewa, wannan tsarin siyasa da aka yi shekaru 60 ana amfani da shi yana dacewa da halin da ake ciki a nan kasar Sin.

A cikin shekarar da ta gabata, kasar Sin ta hadu da bala'u daga indallahi masu tsanani, kamar su bala'in dusar da kankara da ya auku a yankunan kudancin kasar Sin da bala'in girgizar kasa da ya auku a lardin Sichuan. Amma a waje daya, kasar Sin ta samu nasarar shirya gasar wasannin motsa jiki ta Olympic a nan birnin Beijing da gasar wasannin motsa jiki ta nakasassu ta Olympic ta Beijing, kuma ta ci nasarar harba wani tauraron dan Adam mai dauke da 'yan sama jannati 3 zuwa sararin samaniya. Bugu da kari kuma, har yanzu ana tinkara matsalar kudi ta duniya kamar yadda sauran kasashen duniya suke fama. Lokacin da yake ambata abubuwan da suka faru a cikin shekarar da ta gabata, Mr. Jia ya almanta cewa, membobin majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin sun bayar da gudummawarsu wajen neman samun wadannan sakamako. Mr. Jia ya ce, "Mun ba da shawara da shiga harkokin siyasa cikin hali mai yakini kan muhimman batutuwan da suke da nasaba da ci gaban tattalin arziki da zaman al'umma da sauran fannoni. Kuma mun gabatar da dimbin shawara kan ayyukan musamman. Wadannan shawara sun zama muhimman bayanai ga gwamnatin tsakiya lokacin da take tsai da kuduran karshe a fannoni daban daban. A waje daya kuma, muna mai da hankali kan abubuwan da suke da nasaba da zaman rayuwar fararen hula a kullum domin sa kaimi ga kokarin daidaita wasu matsaloli masu tsanani."

Game da batun yin gyare-gyare da ci gaban sha'anin kudi a kauyuka da ke jawo hankalin mutane, mambobin majalisar sun yi rabin shekara suna rangadin aiki a kauyuka da yawa, kuma sun gabatar da "wasu shawara kan yadda za a yi gyare-gyare da ci gaban sha'anin kudi a kauyuka". Mr. Zhang Zuoji, shugaban kwamitin tattalin arziki na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin ya ce, "Bayan da suka yi bincike, mambobin majalisar suna ganin cewa, yin gyare-gyare kan hanyar aikin gona da tsarin kauyuka muhimmin juyin juya hali ne da aka yi a karo na biyu a kauyuka. Sun ba da shawara cewa, ya kamata a kara karfin raya kungiyoyin aikin gona na hadin gwiwa na zamani ta hanyoyi daban daban, kuma a nemi samun ci gaban aikin gona da masana'antu da kasuwanni tare a kauyuka."

Jama'a masu sauraro, kasar Sin kasa ce da ke kunshe da kabilu daban daban wadanda suke bin addinai iri daban daban. Mambobin majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin suna kuma kokarin neman ra'ayoyinsu. Mr. Tian Congming, shugaban kwamitin kula da harkokin kabilu da addinai na majalisar ya ce, "Lokacin da muke yin aikinmu, mu kan mai da hankali kan muhimman abubuwan da kabilu daban daban da masu bin addinai daban daban suke kulawa da su da kuma neman ra'ayoyinsu domin kare moriyarsu irin ta halal." (Sanusi Chen)