Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-02 17:14:28    
Kasar Sin ta kaddamar da rahotonta kan "jihar Tibet a cikin shekaru 50 da aka yi mata gyare-gyare ta fuskar dimokuradiyya"

cri
Ran 2 ga wata, ofishin yada labaru na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya kaddamar da rahoto kan "jihar Tibet a cikin shekaru 50 da aka yi mata gyare-gyare ta fuskar dimokuradiyya", wanda ya zama karo na 8 da gwamnatin Sin ta kaddamar da irin wannan rahoto dangane da jihar Tibet mai cin gashin kanta. Rahoton ya nuna cewa, gyare-gyaren da aka yi a jihar Tibet ta fuskar dimokuradiyya wani muhimmin batu ne a cikin tarihin bunkasuwar zaman al'ummar kasa da ci gaban hakkin dan Adam a Tibet, haka kuma, wani babban ci gaba ne da aka samu a fannin bunkasuwar al'adun mutane da kuma tarihin kiyaye hakkin dan Adam na duniya.

A cikin sassa 5 ne rahoton ya yi cikakken bayani kan dalilan da suka sa aka yi gyare-gyare ta fuskar dimokuradiyya a Tibet yau da shekaru 50 da suka wuce da yadda aka yi gyare-gyaren da sauye-sauyen da Tibet ta samu a sakamakon gyare-gyaren da kuma nasarorin da aka samu wajen yin gyare-gyaren.

Bisa abubuwan da ke cikin rahoton, an ce, kafin shekarar 1959, Tibet wani wuri ne da ya taba kasancewa mai koma baya da kuma duhu sosai, kuma an hade zaman addini da siyasa tare. Bayi manoma da bayin da yawansu ya kai kashi 95 cikin dari bisa jimillar mazauna Tibet ba su da abubuwan kawo albarka da 'yancin kai ko kadan. Suna fama da tsananin talauci a sakamakon ci da guminsu sosai.

Rahoton ya sha tsamo abubuwan da ke cikin littattafan da mutanen waje suka rubuta kan Tibet domin tono ainihin zaman rayuwar fararen hula mazauna Tibet kafin yin gyare-gyare ta fuskar dimokuradiyya. Tom Grumfeld, wani kwararre ne mai nazari kan Tibet daga jami'ar jihar New York ya rubuta cewar, a gabashin Tibet kafin shekarar 1940, iyalan da yawansu ya kai kashi 38 cikin dari ba su taba shan ti ba, kuma kashi 51 cikin dari ba su iya cin man girki irin na Su You ba. Kana kashi 75 cikin dari kuwa babu abincin da za su iya ci, sai dai ciyayin da suka dafa tare da kashin shanu da garin Oat.

Ban da wannan kuma, rahoton ya nuna cewa, babu abubuwan shaida da suka nuna cewa, Tibet ta kasance aljanna ce mai zaman lafiya kafin shekarar 1959.

Sa'an nan kuma, rahoton ya tsamo dimbin bayanan tarihi wajen yin cikakken bayani kan dalilan da suka sa aka yi gyare-gyare ta fuskar dimokuradiyya a Tibet da kuma yadda aka yi gyare-gyaren a shekarar 1959.

Bayan da aka yi gyare-gyare ta fuskar dimokuradiyya a Tibet, gwamnatin tsakiya ta kasar Sin ta yi jerin gyare-gyare a wannan jiha. Ta yi watsi da tsarin bauta na gargajiya tare da yin gyare-gyare kan gonaki, ta haka bayin manoma da bayi sun sami gonakinsu na kansu. Kazalika kuma, gwamnatin tsakiya ta Sin ta raba zaman addini daga harkokin siyasa da kuma aiwatar da manufar bin addini cikin 'yancin kai, ta haka, ta maido da ainihin addini da kuma tabbatar da hakkin mazauna Tibet na bin addini. Haka kuma, gwamnatin tsakiya ta Sin ta bai wa jama'ar Tibet ikon gudanar da harkokinsu da kansu.

A cikin shekaru 50 da suka wuce, Tibet ta sami manyan sauye-sauye a fannonin siyasa da tattalin arziki da al'adu da ba da ilmi da ci gaban zaman al'ummar kasa.

Bugu da kari kuma, bisa goyon baya da kulawar da gwamantin tsakiya ke nunawa, zaman rayuwar jama'ar Tibet ya samu kyautatuwa sosai tare da kyautatuwar gidaje da kiwon lafiya da samun ilmi da harkokin al'adu kwarai. Ta haka an tsawaita matsakaicin tsawon rayuwarsu da kusan sau 1 bisa na yau da shekaru 50 ko fiye da suka wuce. Ban da wannan kuma, ana kiyaye da yayata al'adun gargajiya na Tibet tare da bin addini cikin 'yancin kai.

A karshen rahoton, an nuna cewa, yanzu Tibet na kasancewa cikin hali mafi kyau a tarihinta. Amma a cikin wadannan shekaru 50 da suka wuce, rukunin Dalai bai daina yunkurin maido da tsarin bauta na gargajiya da ya hade zaman addini da siyasa ba. Ana yin gwagwarmaya da shi ne domin yaki da koma baya da kawo wa kasar Sin baraka. Rahoton ya nanata cewa, har kullum gwamnatin tsakiya ta kasar Sin na bude wa Dalai na 14 kofar maido da kishin kasar Sin, kuma ba za ta rufe ba a nan gaba.(Tasallah)