Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-02-27 15:46:30    
Kasar Sin ta kawo manyan sauye-sauye ga Afirka ta hanyar giggina kayan more rayuwa, in ji Meles Zenawi, firayin ministan kasar Habasha

cri

Kafin a yi taron koli na kungiyar tarayyar kasashen Afirka ta AU a watan Faburairu na shekarar bana, wakilinmu ya yi hira da Meles Zenawi, firayin ministan kasar Habasha, inda ya nuna yabo ga kasar sin kan matakanta na kokarin gina kayan more rayuwa a Afirka. Irin wannan kokarin da kasar Sin ta yi ta haifar da manyan sauye-sauye a kasashen Afirka, in ji shi.

Mista Zenawi ya ce, cikin shekaru 30 da suka wuce, yawancin kasashen Afirka ba su samu damar kula da kayan more rayuwa sosai ba,sakamakon rashin isashen kudi. Shi ya sa, tallafin da kasar sin ta baiwa kasashen Afirka a fannin raya kasa da na gina kayan more rayuwa na da kyakkyawan tasiri. Musamman ma a wajen aikin gina hanyoyin mota. Yanzu a Addis Ababa, hedikwatar kasar Habasha, kusan dukkan hanyoyi masu kyau da za a iya gani, kamfanonin kasar Sin ne suka gina su.

Mista Zenawi ya kara da cewa, dalilin da ya sa aka mai da "gina kayan more rayuwa a Afirka" babban taken taron koli na kungiyar AU, shi ne domin aikin gina kayan more rayuwa ya kasance batu mai muhimmanci sosai ga kasashen Afirka, bisa faftukarsu na neman raya tattalin arziki da kawar da talauci. Duk ko wane fannin tattalin arziki da ake neman bunkasuwa, ba za a samu cimma buri ba, sai dai tare da kayan more rayuwa mai inganci. Domin rashin kayan zai hana jigilar da danyun kayayyaki da kayan masana'antu yadda ya kamata.

Mista Zenawi ya ba da misali da kasar Habasha, inda ya ce, gwamnatin kasarsa ta fi mai da hankali kan horar da jami'an gwamnati da neman samun jari don raya kayan more rayuwa, wato a bangare daya, ana horar da jami'ai don kara kwarewarsu kan jagorancin aikin gina kayan more rayuwa. A dayan bangare kuma, gwamnatin kasar Habasha na kokarin janyo jari daga gida da waje, don neman cika gibin kudi da aka samu a wajen aikin gina kayan more rayuwa. Mista Zenawi ya fada cewa, kasar Sin ta riga ta zama daya daga cikin kasashen da suka fi bayar da kudi ga kasashen Afirka don inganta kayan more rayuwa. Kamar dai a kasar Habasha kadai, kasar Sin ta bayar da makudan kudade a matsayin rance don gina hanyyoyi, da kayayyakin sadarwa, da ma'aikatan fid da wutar lantarki, da dai makamantansu.

Sa'an nan Mista Zenawi ya kara yaba wa kasar Sin, bisa ganin kasar Sin ba ta rage tallafin da take baiwa kasashen Afirka ba, duk da cewa ita ma tana fuskantar barazanar rikicin hada-hadar kudi, wanda ke addabar kasashen duniya. Mista Zenawi ya ce, ko da yake rikicin hada-hadar kudi ya yi illa ga tattalin arzikin kasar Sin, amma bai hana ta yin alkawarin ci gaba da zuba jari a kasashen Afirka da ba da taimako ba, abun ya bayyana halin karko na huldar da ke tsakanin Sin da Afirka.

Haka kuma, Mista Zenawi ya amince da kwarewar kamfanonin kasar Sin kan gina ayyuka masu inganci. Ya ce, abubuwan da kamfanonin kasar Sin suka gina na da inganci, kuma ba a dakatar da wa'adin aiki, haka kuma an yi su ne bisa kudin araha. Rike wadannan manufofi ya zama dalilin da ya sa kamfanonin Sin suka samu karbuwa a nahiyar Afirka.(Bello Wang)