Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-02-26 16:37:59    
Zaman jin dadi na iyalin manoma Wang Honglin da matarsa

cri
wakar da kuke saurara yanzu wata waka ce da madam Ma Xiuhua ta rera. Madam Ma wata manomiya ce da take zaune a jihar Ningxia ta kabilar Hui mai cin gashin kai da ke arewa maso yammacin kasar Sin. A cikin wakar, Madam Ma ta rera kamar haka:" Ana iya samun abubuwa masu albarka da kuma maka-makan gonaki a arewa maso yammacin kasar Sin, mazaunan wurin kuma su kan nuna himma da kwazo wajen aiki, kullum su kan fadi albarkacin bakunansu da kuma gudanar da ayyukan da suke nuna sha'awa a kai. Arewa maso yammacin kasar Sin, arewa maso yammacin kasar Sin, inda a kan nuna fatan alheri da kuma jin dadin zaman rayuwa a ciki." To, masu sauraro, a cikin shirinmu na yau za mu ja ku zuwa gidanta don jin yadda Madam Ma Xiuhua da mijinta Wang Honglin da sauran iyalinta suke gudanar da dakun cin abinci na manoma domin baki su ji zaman nishadi a gidansu.

Wakilanmu sun dauki mota daga birnin Yinchuan, hedkwatar jihar Ningxia sun doshi kudu, sun shafe kusan rabin awa suna tafiya sai suka isa wani wuri, inda suka ji haushin karnuka, nan ne kauyen da gidan Ma Xiuhua ya ke.

Da baki sun zo, sai mai gida Wang Honglin da iyalinsa su kama shan aiki, suna kama kifaye da yanka kaji da kuma debar kayan lambu domin nuna bakunci ga bakin, ba da dadewa ba sai a gama dafa abinci, kuma a ajiye shi bisa kan tebur, ciki har da shinkafa da miya da sauran cimaka, dukkansu abincin musulmi ne sosai, madam Ma Xiuhua ta ce,

"Dukkan abincin da gidanmu ya sayar suna da halayen musamman na musulmi, bakin da suka zo ba don kome ba ne illa cin abincinmu kawai, sun ce abincin gidanmu yana da araha, kuma yana da dadi, sabo da haka bayan da suka ci abinci a karo na farko a nan, kuma yawancinsu za su sake dawowa."

Ganin farin ciki da matarsa ta yi, Wang Honglin ya gaya mana cewa, yanzu dukkan iyalinsa suna mai da hankali sosai a kan raya wannan dakin cin abinci na musulmi, dalilin da ya sa haka shi ne sabo da ya kawo musu fatan alheri da kuma zaman rayuwa mai zaki.

Wang Honglin wani manomi ne da ke zaune a kauyen Taqiao na unguwar Xingqing ta birnin Yinchuan, a da ya dukufa kan aikin noma. Daga baya bisa karin himmar da ya samu daga wajen gwamnatin kasar wajen gudanar da sana'o'i da yawa, da samun arziki ta hanyar yin aiki tukuru, ya fara kiwon kifaye daga shekarar 1994. Amma domin karancin ilmin kiwon kifaye, burinsa na jin dadin zaman rayuwa ya zama wani mummunen mafarki. Ko da yake shekarun Wang Lijun, da na Wang Honglin suka kai 12 da haihuwa a wancan lokaci, amma har yanzu bai iya mantawa da wancan abu mai bakin ciki sosai. Wang Lijun ya ce,

"A wancan rana da tsakar rana, ina yin barci a cikin daki, kwaram na samu labarin cewa, wurin kiwon kifaye ya gamu da hadari. Ashe, kifaye ba su iya samun isashiyyar iskar Oxygen ba, in a gamu da wannan hali, to ba yadda za a yi sai a zauna a gefunan wurin, a ga mutuwar kifayen."

Sabo da haka, kudin Sin wato Yuan dubu 30 sun bace, wanda ya bata ran Wang Honglin sosai. Daga baya kuma ya kaddamar da zamansa na cin rani a wurare daban daban. Amma sabo da ba shi da fasaha ko kadan ba, shi ya sa ba yadda za a sai ya gudanar da ayyuka na ba da karfi kawai, kuma bai iya samun yawan kudaden shiga ba. Ko da haka, amma wadannan ayyukan cin rani da Wang Honglin ya yi har shekaru 10 sun bude idonsa sosai, kuma ya samu sabbin ra'ayoyi. A daidai wannan lokaci, kauyen da yake ciki yana cikin shirin kara kwarin gwiwar 'yan kauyen da su raya dakunan cin abinci domin baki su yi zaman ninshadi cikin gidan manoma, shi ya sa Wang Honglin ya yi rajista ba tare da bata lokaci ba domin shiga kungiyar bincike da kauyen Taiqiao ya shirya wajen koyon yadda aka raya aikin. Kuma Mr. Wang ya ce,

"Na samu labari ta talabijin cewa, yanzu aikin raya dakunan ci abinci domin baki su yi fatsa da yin zaman nishadi cikin gidan manoma wata hanya ce mai kyau da ake bi wajen samun aikin yi. Kauyenmu kuma ya aike da mu zuwa sauran wurare na kasar Sin ciki har da lardin Shandong domin koyon fasahar tafiyar da aikin, muna ganin cewa ma iya samun kudin shiga da yawa ta bin wannan hanya."

Wannan ra'ayi ya samu goyon baya sosai daga matarsa Ma Xiuhua, Madam Ma ta bayyana cewa,

"bayan da muka yi tafiya zuwa wurare daban daban, da kuma ganin yadda ake raya irin wannan dakin cin abinci cikin gidan manoma, muna ganin cewa, lalle ya kamata mu raya aikin a wurinmu domin mutane su zo su shaki iska mai danye su yi fatsa su ji dadin zaman rayuwarsu."

Sabo da Wang Honglin ya taba cin tura wajen raya aikinsa sakamakon karancin ilmi, shi ya sa ya tsai da kudurin mayar da aikin koyon fasahohi a gaban kome. Ko da yake shekarunsa suka zarce 40 da haihuwa, amma ya tsaya tsayin daka kan shiga kwas din horar da fasahohi da kauyen ya shirya don manoma, da kuma fara koyon fasahohin dafa abinci. Mr. Wang ya ce,

"A lokacin da, na iya dafa abinci iri da dama kawai, amma bayan da na shiga kwas din horaswa, an koyar mana yadda a dafa abinci iri daban daban. Bayan da na gama karatu daga kwas din horaswa, na hada sakamako mai kyau da na samu daga kwas din da kuma abincin da manoma su kan ci kullum tare, sai na gano cewa, lalle na samu babban ci gaba. Kamar yadda mutanen jihar Ningxia su kan ce, in a zaune a gida, to ba zai san kome ba, amma in a tafi waje, to zai ji mamaki sosai. Kwas din horaswa na da muhimmanci kwarai, wanda kuma ya kara kwarin gwiwata sosai."

Madam Ma Xiuhua ita ma ba ta huta a gida ba, tana koyon fasahar kiwon kifaye daga wajen masanan kimiyya da fasaha. Bayan da Wang Honglin da matarsa suka shirya kome da kome, sun kaddamar da aikinsa na bude dakin cin abinci da ya hada da yin fatsa da abincin manoma musulmi tare a watan Afril na shekara ta 2007. Bayan da ma'aikatan hukuma da manoman kauyen Taqiao suka ji labarin, dukkansu sun je gidansu don taya su murna, kuma sun nuna musu goyon baya wajen tunani sosai. Madam Ma Xiuhua ta gaya wa wakilanmu cewa,

"Da aka ji labarin budewar dakin yin nishadi na manoma musulmai a gidanmu da kuma kebe wurin yin fatsa, sai shugabannin gundumarmu da na kauyenmu dukkansu suka zo nan don taya mana murna, kuma sun nuna mana goyon baya, sabo da haka muka kara nuna amincewa ga gudanar da wannan aiki namu."

Domin wannan dakin yin nishadi na manoma musulmai na da halinsa na musamman, ban da samar da kifaye masu rai da kuma abinci mai dadi, Wang Honglin ya sa kujeru masu rawa da na'urar oda wakoki wato karaoke da kuma teburin wasan kwallon billiards a farfajiya domin biyan bukatun baki daban daban. Wu Shenglin, wani bako ne da ya kan zo wurin kullum. Kuma ya nuna yabo sosai ga ayyukan ba da hidima na wurin. Ya ce,

"Na riga na zo wurin sau da yawa, a karshen mako, na kan zo wurin tare da abokaina, mun yi fatsa, mun gasa kifaye, mun ci abinci mai dadi, kuma mun ji dadin zaman rayuwarmu sosai. Da zarar mun iso wurin, sai mun ji kamar mun shiga gandun daji."

Kamar yadda Wu Shenglin ya ce, yin fatsa da rera wakoki da cin abincin manoma da kuma shakar iska mai danye a karshen mako sun riga sun zama wata sabuwar hanyar zaman rayuwa da 'yan birane suka fi son zaba. Sabo da haka a ko wane karshen mako, iyalan Wang Honglin su kan sha aiki sosai har ma zuwa karfi 1 ko 2 da sassafe, amma duk da haka suna farin ciki sabo da kyakkyawan yabo da suka samu daga wajen bakin, ban da wannan kuma abin da ya fi faranta ran Wang Honglin shi ne, yanzu yawan kudin shiga da iyalinsu ke samu ya iya kaiwa kusan Yuan 1000 a kowace rana, ya ce,

"Yanzu lalle muna cikin zaman jin dadi sosai, wallahi! kamar aljanna muke ciki. Yanzu kuma dakunan kwana da aka gina a kauyenmu suna da kyau sosai, yayin da dana ya yi aure, an gina masa dakuna daidai kamar na mutanen birni. Sharudan zaman rayuwa na iyalinmu suna da kyau, kusan a ce muna cin naman kifaye da na shanu da na awaki a kowace rana, yanzu ma har ba mu son cin namun dabbobin gida sosai, akasin haka kuma mun fi son cin dankalin turawa."

Lokacin da wakilanmu suke yin hira tare da Wang Honglin, dansa Wang Lijun da ya je kasuwa don sayen kayayyaki ya dawo. Wang Honglin ya gaya mana cewa, bayan shekaru biyu, dansa zai maye gurbinsa wajen tafiyar da wannan dakin cin abinci, shi kuma zai kere raini.

Burin mahaifinsa ya kara nauyin da ke bisa wuyan Wang Lijun, a ganinsa, yana bukatar koyon abubuwa da yawa. Lokacin da yake tabo bunkasuwar dakin cin abinci na manoma musulmai a nan gaba, Wang Lijun yana ganin cewa, kiyaye halin musamman na daya tak wani muhimmin abu ne, yin fatsar crayfish wani aiki ne da yake cikin shirin gudanarwa. Kuma ya kara da cewa,

"Halin musamman na abinci na arewa maso yammacin kasarmu shi ne yaji, shi ya sa tabbas ne dafa crayfish tare da yaji zai samu amincewa sosai daga baki. In ana iya yin fatsa, to tabbas ne ana iya yin fatsar crayfish. Dafa crayfish ya fi sauki in an kwatanta da kifaye, shi ya sa ina ganin cewa, idan mun iya samun nasara wajen gudanar da aikin, to za mu zama dakin cin abinci daya tak a arewa maso yammacin kasar Sin."