Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-02-26 16:33:55    
Yankin Tibet a jiya, yau da kuma gobe a idon Garba

cri

Garba

Kamar yadda ya taba faruwa a wasu sassan kasashen duniya, yankin na Tibet dake kudu maso yammacin kasar Sin ya sheda mulkin danniya kan wasu mutane da suka kasance marasa galihu duk kuwa da cewar adadinsu ya haura na masu abin hannu da shugabannin addini yawa. Marasa abin hannu a da can a yankin Tibet sun kasance bayi ga shugabannin addini da masu mulki gami da masu hannu da shuni na wancan lokaci. Cikin shekaru da yawa wadannan bayi na dole sun kasance cikin halin ukuba da gallazawa, suna yin aiki ga masu gidajensu a filayen noma da kuma cikin gida a matsayinsu na bayi kuma barori. A cibiyar baje kolin kayayyakin tarihi na al'ummun kasar Sin, sakamakon zagayowar ranar cika shekaru hamsin da 'yantuwar bayi manoma, an baje kolin kayan tarihi na yankin Tibet, wata mai yin bayani kan kayan tarihin ta sheda farin cikinta na kasancewa da samun 'yanci ga bayin na da kamar haka:

"Muna nan muna aikin bayani kan bajekolin, kuma mun yi hira da masu kallo.Gaskiya sun nuna sha'awa kan hutuna da abubuwan da ake nunawa, musamman ma kan abun da ya dangane da yadda bayi manoman Tibet suka samu 'yancin kansu.Mun san cewa, daga tsohuwar tibet ta shekaru gomai da suka wuce, zuwa sabuwar tibet ta yanzu, an samu gagarumin sauye-sauyen zaman rayuwar jama'ar Tibet. Ganin abubuwan da ake nunawa ya sa mu farin ciki, kuma ya sa mu nuna yabo da kauna ga kasarmu. Kamar dai ni ina haka, wato ina jin alfahari bisa matsayina na 'yar kasar Sin."

A karkashin jagorancin gwamnatin gurguzu ta kasar Sin, wadannan bayin Allah manoma ko bayi ga Lamas da Dalai da Panchen wadanda suka kasance shugabannin addini kuma masu fada aji a tsakanin al'umar Tibet, sun kubuta daga irin wannan kangi na mulkin danniya da tursasawa. Don a karshen shekarun 1940 zuwa farkon shekarun 1950 ne, wannan gwamnati ta fara aiwatar da yunkurin 'yantar da bayin dole manoma. A yayin bikin baje kolin kayan tarihin al'umar Tibet din mutane da dama sun hallara, ga abinda wani tsoho ke fada, kan tasirin da 'yantar da bayin yankin Tibet din da kuma irin ci gaban da hakan ya kawo:

"Abubuwan da nake ji a rai sun cika yawa.A takaice dai, idan ba a 'yantar da Tibet daga tsarin bayi manoma ba, to ba za a samu wani tibet mai cigaba kamar na yanzu ba. Abun da ake nuni na shaida cewa, sai dai a karkashin jagorancin da jamiyyar kwaminis ta kasar Sin ta yi ne, aka samu damar raya tibet lami lafiya. Su 'yan tsirarun mutanen da ke yunkurin balle tibet daga kasar Sin sam ba za su samu cimma burinsu ba. Domin jama'ar Tibet ba za su yarda da aikace-aikacen neman kawo baraka ga kasar Sin da Dala laima ke yi a kasashen waje ba, kuma duk jama'ar kasar Sin ba za su yarda da wannan ba. Tabban ne, yankin tibet zai samu gobe mai haske."

Dalilai da dama ko shakka babu sun yi tasiri kan batun bukatar samun sauye-sauye a Tibet, kuma ba shakka, wasu zarata a kasar Sin sun yi hobbasa wajen ganin sauyin ya samu. A shekarar 1951 ne aka kafa yarjejeniya mai gafaka goma sha bakwai a tsakanin gwamnatin tsakiyar kasar Sin da kuma karamar hukumar Tibet dan 'yantar da yankin da kuma jama'arsa. Amma daga bisani an samu masu tada kayar baya da suka so ganin ci gaban dorewar yanayi tamkar na mulkin mulaka'u. Wannan ya haddasa kafsawa a tsakanin sojojin gwamnatin Sin da na yankin Tibet masu ra'ayin ci gaba da mallakar bayi. A karshe dai, sojojin gwamnati sun yi galaba kuma sun 'yantar da yankin da jama'arsa. Kuma wadannan sojoji sun taimakawa jama'ar yankin Tibet ta fannoni da dama, kamar aikin kula da lafiya, giggina hanyoyi da magudanan ruwa. Sannan basu tsaya nan ba, hatta abincin da zasu ci sune da kansu suka noma tare da tarairayarsa har zuwa lokacin girbi da yin amfani da shi. Game da irin wannan bunkasa da yankin ya samu, wata tsohuwa da ta halarci wajen nunin kayan tarihin ta bayyana cewar:

"Kallon abubuwan da aka nuna ya sa na fahimci kyaun yankin tibet. Da na samu dama zan kai ziyara a can. An kwatanta zaman manoman tibet na da da na yanzu, mun gano cewa, da ma ana shan wahala sosai yayin da suke zaune a tibet, amma yanzu an samu jin dadi.Dazu nan na dan dandana ganyen shayi na musamman na tibet, akwai dadin sha sosai. yanzu an raya tibet da kyau a dukkan fannoni.

ina jin takaici kan mugun aiki na neman jawo baraka ga kasar Sin. duk da cewa mun kasance cikin hali ne mai kyau, amma su 'yan tsirarun mutane sun aikata danyen aikinsu.ina jin tausayi kan mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon tarzomar da aka yi a shekarar bara.Da ma ana shan wahala a tibet, amma yanzu ana samun cigaba da jin dadi a can, me ya sa ka yi wani abu na ta da hankulan mutane?wannan bai yi daidai ba.

Koda bayan wannan ci gaba da aka samu a yankin na Tibet, har yanzu tsugune ana iya cewa bata gama karewa ba. Dalili a nan shi ne, har yanzu akwai masu neman kawo baraka ga yanayin zaman lafiyar jama'ar yankin sakamakon ingizawar wasu. Sannan akwai masu ra'ayin cewar irin wadannan mutane ba komai suke so ba face kawowa kasar Sin baraka da samun rarrabuwar al'umarta. Ga misali a cikin watan Maris na shekara ta 2008 ma an tafka hargitsi a yankin Tibet, wanda kuma wasu tsiraru dake bololon ganin yankin ya zama mai mai 'yancin kai suka haddasa. Lamarin ko tantama babu bai yi dadi ba dan kuwa ya haddasa rasa rayukan mutane da yawa."

Koma dai mene ne nufin irin wadannan mutane, jama'ar yankin Tibet a yau ana iya cewa sun gamsu da kasancewarsu cikin jamhuriyar jama'ar kasar Sin daya tilo. Sun kuma sheda irin ci gaban da sannu a hankali yake ta zuwa musu, ta hanyoyi da dama na rayuwa kuma tattare da sauye-sauyen dake ci gaba da wakana.