Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-02-26 16:16:11    
Labaru masu ban sha'awa na kasar Sin

cri
Bisa labarin da aka buga a cikin jaridar Changsha evening News ta lardin Hunan dake kudancin kasar Sin kwanan baya, an ce wani matashi ya yi suna sabo da nauyin jikin da ya rage cikin shekaru biyu. Har ma ya zama abun koyi ga mutanen da suke son su rage nauyin jikinsu. Sunan matashin shi ne Du Jie yana da shekaru talatin da haihuwa . ta hanyar yanar gizo ta internet ya yi hira da mutane da suka rage wa kansu yawan abincin da suka ci ya gaya musu yadda ya yi a da wajen rage nauyin jiki. Kafin shekaru biyu nauyinsa ya kai kilo 147, ga shi yanzu ya rage har ya kai kilo 80 kawai.A cikin shafinsa na yanar internet ya rubuta haka,abun mafi muhimmanci wajen rage nauyin jiki, shi ne nacewa. Idan kana so ka rage nauyi, sai ka nace ga bin hanyar da ake bukata,ta haka burinka zai tabbata. Kafin ya rage nauyin jikinsa ya ci jarrabawar shiga manyan jami'o'i.amma nauyin jikinsa ya wuce matakin da aka dauka na shiga jami'ar soja wanda ya ke so,ya rasa damar. Wata jami'ar koyon likitanci ta shiga da shi.

Wani yaro ya samu taimako daga masu kashe gobara. Bisa wani labarin da aka buga a cikin jaridar Dahe news, an ce an samu wata mahaifiya da take neman taimako daga ma'aikatan kashe gobara yayin da danta mai shekaru biyu da haihuwa ke kamuwa da teburin wasa mai aiki da wutar lantarki. Duk da masu kashe gobara sun isa wurin cikin lokaci, Yaron bai samu rauni mai tsananni ba, wannan lamari ya faru a makon jiya a gundumar Yiyang ta lardin Henan dake kudancin kasar Sin.

Wani mutum da ya yi suma na tsawon shekaru shida ya farka. Bisa labarin da aka buga a cikin jaridar Dongfang Jinbao News ta lardin Henan dake tsakiyar kasar Sin kwanan baya, an ce wani mutum ya yi magana kwanan baya bayan da yana cikin yanayin suma na tsawon shekaru shida duk da kulawar da matarsa ta yi masa. An kiran wannan mutum da suna Chang Xueyun,yana da shekaru 57 da haihuwa,ya suma ne saboda wani hadarin mota da aka yi a gundumar Huixian ta lardin Henan a shekara ta 2002. Daga wannan lokaci matarsa ta yi iyakacin kokarinta wajen kula da shi.Kusan a ce kowace rana ta yi mijinta tausa kuma ta fitar da shi domin shan hantsi. Matar ta ce," shi ne mijina ne kome gajiya da na yi ba zan yi watsi da shi ba." Bisa kokarin da ta yi na nuna kulawa sosai,mijinta ya warke ya koma yadda ya kamata.

An daukaka matsayin yan sanda bisa yawan ayyukan da suka yi.Bisa labarin da aka buga a cikin jaridar Beijing News kwannan baya, an ce wata hukumar kula da 'yan sandan dake wani bangare na birnin Beijing, babban birni na kasar Sin tana so ta daukaka matsayin 'yan sanda 66 dake karkashinta kan ayyukan da suka yi, kamar su kama barayi da warware gardama tsakanin mazauna. Amma duk wanda ya kasa cimma matsayin da aka tsaida,wato kama barawo a kalla dai daya ko warware gardama daya tsakanin mazauna birni,ba a daukaka matsayinsa ba. Wani jami'in hukuma ya ce " mun dauki wannan mataki ne tare da nufin karfafa guiwar 'yan sanda ta yadda za su kara mayar da hankalinsu kan tsaron lafiyar jama'a da kare mazaunan birni." Duk da haka wannan matakin da aka dauka ya haifar da cece kuce tsakanin mazauna birnin.

'Yan sanda sun kama mabiyan addinin Buddha na jabu. Bisa labarin da aka buga a cikin jaridar Beijing Morning Post kwanan baya, an ce kwanan baya wata hukumar 'yan sanda ta kama barayi mata sama da ashirin da suka shiga burtun sista mabiyan addinin Budhha wadanda suka yi mazauna birnin zamba da satar kayayyakinsu masu daraja, a ganin daidaikun jama'a su mabiyan addini ne ba ruwansu da zamba da kuma sata,a ainihin gaskiya su barayi ne. har sun yi satar kayayyaki daga gidaje da yawa, ban da wannan kuma sun yi wa mazauna birni zamba ta hanyar addini ta wai, kudin da suka zamba daga wani iyali ya kai kudin Sin Yuan dubu sha hudu da dari biyar da hamsin. Da kowace rana da safe madugar barayi ta tattara mabiyanta ta ba su aikin da dare ta sake tattara su domin duban yawan kayayyakin da suka samu ta sata. Duk da haka,'yan sanda sun kama su gaba daya, kuma an yanke musu hukunci yadda ya kamata.

An kama wani dan fashin dake cikin barci. Bisa labarin da aka buga a cikin jaridar Shanxi Evening news kwanan baya. Kwanan baya wata kotu ta wuri ta yanke hukuncin dauri na shekara daya a gidan wakafi da cin masa tarar kudin Sin Yuan dubu biyu domin ya yi shirin yin fashin matukin motar taxi,an kama shi kafin ya tabbatar da burinsa. Wata rana da dan fashi ya shiga motar taxi, baci ya kwashe shi sabo da wani maganin da ya ha, da motar ta yi nisa dan fashi ya ci gaba da barci.matukin motar bai san inda ya kwana ba,sai ya ta da shi,ashe ya ga wata wuka mai kaifi ta sauko daga babbar rigarsa.da ganin haka ya kirawo 'yan sanda, 'yan sanda sun yi awon gaba da shi.

Masu tafiyar da harkokin dakin sayar da abinci suna so su taimaki dalibai. Bisa labarin da aka buga a cikin jaridar Chongging News kwanan baya, an ce mutane hudu masu tafiyar da harkokin dakin sayar da abinci suna so su ba da taimako ga dalibai biyar da ke karatu a jami'a. Mr Liang Huan,na daya daga cikin mutanen hudu ya ce lokacin da ya ke karatu a wata jami'a a birnin Chongqing ba shi da kudin cin abinci hade da nama,duk da suka ci abinci hade nada,abokansa na karatu ne suka biya.amma yanzu yana da kudi isashe,yana so ya bayar da taimako.wani abokin aikinsa ya ce muna so mu taimaki dalibai biyar wadanda ba su da karfin biyan kudin sayen abinci hade da nama." Da haka sun yi mu'amala da kafofin yada labarai da su ba su taimako wajen samo daliban da suke so su ba su taimako.