Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-02-25 15:38:59    
Mawakiyar yankin Taiwan Cai Qin

cri
yanzu ga shirinmu na al'adun kasar Sin, yau za mu kawo muku wani bayanin da ke da lakabi haka: "Mawakiyar yankin Taiwan na kasar Sin Cai Qin ".

To, masu saurarommu, wakar da kuka saurara ita ce "Lokaci na da da muka manta da shi" da mawakiyar yankin Taiwan na kasar Sin Cai Qin ta rera. Lalle wannan waka na da dadin ji, yayin da muke sauraron wannan waka, yanayin ya yi kamar wani mai dumi da ya barbazu a ko ina a cikin iska har zuwa ga zukatan mutane. A cikin kusan dukkan zukatan masu sha'awar kide-kide a kasar Sin, Cai Qin ita ce wata mawakiya da babu wadda za ta maye gurbinta, kuma ana kiranta mawakiyar da ba za ta tsufa ba wajen rera waka, To, a cikin shirimmu na yau, za mu gabatar da muku da wasu wakokin da mawakiyar Cai Qin ta rera da zaman rayuwarta, to bismillah:

Muryar Cai Qin na da dadin ji, kuma a cikin muryarta, za ka iya samun wani yanayi na soyayya, kuma mutane da dama suna sha'awar kide-kidenta, wasu mutane sun siffanta wakokin da Cai Qin ta rera kamar wani kayan shayi, wanda idan aka sha kadan, to, lalle ba za a iya mantawa da shi ba.

Cai Qin, yar asalin lardin Hubei na kasar Sin, an haife ta a birnin Taibei a shekarar 1957, mahaifiyarta wata edita ce ta mujallar Taiwan, kuma mahaifinta wani matukin jirgin ruwa ne, kuma kullum ya kan yi tafiye-tafiye a jirgin ruwa. Sabo da haka, Cai Qin ta kan yi begen babbanta kwarai da gaske, yayin da take karama, ta kan tsaya a gabobin teku, ta na hangen nesa don kallon komawar babbanta. Cai Qin ta bayyana cewa, tun daga take yarinya, sai ta yi fama da bakin ciki na barin dangoginta da irin farin ciki da suke haduwa. Sabo da haka, wakokin da ta rera na cike da wani yanayi na bakin ciki, wannan ya dangane da wadannan labarun da suka auku yayin da take karama.

A sai'lin da take jami'a, Cai Qin ta fara koyon zane-zane da yin fasali, amma sabo da tana son rera waka, a shekarun 70 na karnin da ya wuce, Cai Qin ta fara rera wakokin gargajiya na kasar Sin, ko da yake Cai Qin ba ta da kyan sura, amma sabo da tana da kyakkyawar murya, ta shahara a kasar Sin.

A shekarar 1979, Cai Qin ta rera wata wakar "a daidai da halinka da ke da yawan hakuri" da mai tsara kida Liang Hongzhi ya tsara.

Bayan shekaru 20 kuma, Liang Hongzhi ya rasu, kana Cai Qin ta yi aure, ta rabu da mijin har da ta gano cewar, ta gamu da ciwon sankara da illarta ba ta da tsanani, lalle ta kara jin ma'anar zaman rayuwar mutane.

Bayan da Cai Qin ta haye dukkan wahalhalu, Cai Qin ta bayyana cewa, yanzu tana iya kara fahimtar wannan waka ta "A daidai da halinka da ke da yawan hakuri".

"Yanzu yayin da nike sauraron wannan waka, ba na jin bakin ciki sosai, sai dai gundura kawai."

A cikin shekaru 20 da suka wuce, Cai Qin ta fitar da fina-finai da yawansu ya kai 40 da wani abu, kuma sau da dama, ta sami lambobin yabo a gun gasar rera wakoki, ta rubuta littatafai kuma ta nuna wasanni kuma ta zama jagora kana kuma ta zayyana fasalin tufafi.

Yayin da aka tabo maganar shiga dandalin wasanni, Caiqin ta bayyana cewa,

Na yi farin ciki sosai, sabo da ina da saukin kai kuma na da karfin jurewa, da ma a hakika dai, a bakin wasu mutane, ka kan ji, wadannan wakoki ba su da dadin ji, amma, yanzu idan wasu tsoffin mawaka suka bude baki kuma suka rera wakokin da suka taba rerawa, lalle za su iya kara jin dadin wadannan wakoki.

Wakokin da Caiqin ta rera na da dadin ji kuma suna cike da wani yanayi na bakin ciki, kuma yayin da mutane da na zamani suka hadu da yanayin bakin ciki, bayan da suka ji wadannan wakoki, lalle, za su ji sauki a zukatansu, wasu mutane sun yi sharhi da cewa, Cai Qin ta yi amfani da muryarta don bayyana zaman rayuwar jama'a, watau ba kullum ake kwana a kan gado ba, watakila ma wata rana a kasa ne ake kwantawa, sabo da haka ya kamata mu nuna saukin kai.

Lalle, har zuwa yanzu, mutanen babban yankin kasar Sin da dama na iya tunawa da Wakoki "babban iyali mai katafaren gida" da "jiragen ruwa" da "Wakar tafiya zuwa iyakar kasar Sin" da dai sauran wakokin da suke bayyana al'adun gargajiya na kasar Sin. Cai Qin ta tuna da cewa, da ma, wani tsohon mutum na babban yankin kasar Sin da ya yi zaman rayuwarsa a yankin Taiwan ya yi musafaha da ita kuma ya tambayi Caiqin, ina dalilin da ya sa ba ta manyanta ba, amma ta iya rera wakokin gargajiya da dama.

Cai Qin wata mace da ta fi son rubutattun wakoki na kasar Sin, kuma tana ganin cewa wadannan rubutattun wakoki na cike da wani yanayi na nuna zurfin tunani.

Da ma, Cai Qin tana da wani buri, tana so ta shirya wani taron wake-wake a babban yankin kasar Sin. A lokacin bikin gargajiya na kasar Sin watau bikin bazara na shekarar 2001, gidan telebiji na tsakiya na kasar Sin watau CCTV na kasar Sin ta gayyace ta da ta nuna wasanni a shagalin dare domin murnar bikin gargajiya na kasar Sin watau bikin bazara. A lokacin kaka na shekarar da 2002, sai burinta ya cika, ta shirya wani taron wake-wake a babban yankin kasar Sin. Daga bisani kuma, Cai Qin ta fara shirya taron wake-wake a birane da dama, kuma ko da yaushe mutane na rige-rigen sayen tikiti. Amma Cai Qin ba ta gamsu da dukkan nasarorin da ta samu ba, yayin da aka bayyana makomarta, ta bayyana cewa,

"A ganina, ni mutum ce mai son rera waka, kuma kullum na kan rera wakoki a dandali da nuna wasanni, 'yan kallo su yi tubarkalla gare ni, amma abin kaito ne, sabo da na tsufa, watakila ma nan ba da dadewa ba, za a kawo karshen zaman rayuwata ta rera wakoki, lalle ina fata mutane ba za su manta da ni ba"

A shekarar 2008, Cai Qin ta nuna taron wake-wake na "Kaunar da ba za a iya mantawa da ita ba" a biranen Shanghai da Nanjing da Shenzhen. Bisa labarin da muka samu, a ranar 31 na watan Disamba, Cai Qin ta nuna wasannin "Kaunar da ba za a iya mantawa da ita ba" a dakunan wasannin motsa jiki na lardin Sichuan na kasar Sin, har zuwa lokacin sanyin safiya na ranar 1 ga watan Janairu na shekarar 2009. A gun taron wake-wake, Cai Qin ta rera dukkan wakokinta da ta taba yi a cikin shekaru 20 da suka wuce, kuma wannan taron wake-wake ya zama wani taro ne da aka fi rera wakoki a cikin tsawon lokaci.