Tsoffafin hanyoyi da sunan "HUTONG" wato lunguna da ake samu a nan birnin Beijing, hedkwatar kasar Sin na da dogon tarihi, suna kuma ba da kyan gani irin musamman. Yau ma za mu zagaya wani gidan abinci na musamman da ke boye a lungunan Hutong na Beijing, sunansa shi ne gidan abinci da aka samu asalinsa daga gidan ajiye kankara na sarakuna. A bakin Sinawa kuwa, sunansa shi ne Huang Jia Bing Jiao Can Ting.
Masu sauraro, in kun sami damar kawo ziyara ga lungunan Hutong da ke yankin Houhai na Beijing kan keke mai tayoyi 3, to, watakila masu hawan keke masu tayoyi 3 za su kai muku a lungun Hutong mai suna Gongjian, da ke arewa da fadar sarakuna ta kasar Sin wato Forbidden City, kuma ya dab da yankin Houhai, za ku tsaya a gaban wani babban gini mai launin ja mai duhu, inda za su yi m ku karin bayani kan gidan ajiye kankara na sarukuna da ke cikin wannan babban gini.
Yau da shekaru 100 ko fiye da suka wuce, wato a karshen zamanin daular Qing ta kasar Sin, an taba sa kankara domin sarakuna kawai a cikin wannan gidan ajiye kankara a lokacin hunturu, inda kuma aka ajiye 'ya'yan itatuwa a lokacin kaka.
Amma yanzu wannan babban gini ya zama gidan abinci na musamma da a kan shirya nune-nune kan al'adun gidajen ajiye kankara. Wang Lihui, mai gidan abincin da ke sanye da gajeriyar riga mai launin shudi irin na gargajiya na kasar Sin, ya kan nuna sha'awarsa kan yi wa masu yawon shakatawa bayani kan gidajen ajiye kankara na sarakuna. Ya ce, "An taba kiran wannan gidan ajiye kankara da sunan 'De Shun'. A lokacin da ake fama da sanyi mafi tsanani, watakila yawan zafi ya kai digiri 10 a kasa da sifiri bisa ma'aunin sentigrade a sarari, a cikin wannan gidan ajiye kankara, yawan zafi ya kai digiri 6 bisa ma'aunin sentigrade. A lokacin zafi kuwa, yawan zafi a sarari ya kai digiri 37 ko 38 bisa ma'aunin sentigrade, a cikin gidan ajiye kankarar kuwa, yawan zafi ba ya kai digiri 20 bisa ma'aunin sentigrade. Me ya sa haka? Ashe! Zurfin bangon wannan gidan ajiye kankara ya kai mita 1.4, ta haka ya iya rike zafi sosai tare da abubuwan rike zafi a ciki."
A zamanin da, babu fasahar sanyayya, shi ya sa sarakunan kasar Sin su kan ajiye kankara cikin gidan ajiye kankara ta irin wannan hanya. A sakamakon irin wannan tsarin gini na musamman da bin hanyar da ta dace, kankarar da ke cikin gidan ajiye kankara ba ta iya narke ba har zuwa lokacin zafi mai kamawa. A lokacin zafi, sarakuna su kan yi amfani da wannan kankara a gun bukukuwan nuna girmammawa ko kuma gudun zafi.
An ce, a wancan lokaci, kasar Sin ta kasance kan gaba a duk duniya fannonin samar da kankara da ajiye kankara. Har ma an sami asalin aiskirim ne a fadar saurakuna a kasar Sin. Mr. Wang ya gaya mana wani labari cewa:
"Marco Polo ya zo Beijing domin gaida sarkin zamanin daular Yuan na ksar Sin ne a daidai lokacin zafi, amma tilas ne ya sanye da tufafi ba na sakai-sakai ba, ta haka ya yi gumi da yawa. Bayan da ya gaisa, an ba shi abin sha na musamman, inda aka hada nonon doki da kankara tare. Marco Polo ya ji dadin sha sosai saboda wannan abin sha ya sanyayya jikinsa sosai. Ba tare da bata lokaci ba, ya tambayi sunan wannan abin sha, ya kuma rubuta hanyar samar da shi."
Abin sha na nonon doki da kankara shi ne asalin asikirim. Wajibi ne Marco Polo ya nuna godiya ga gidajen ajiye kankara saboda ya iya dandana abin sha mai dadi haka a wancan lokaci. Yanzu Mr. Wang da matarsa sun yi kwaskwarima kan gidan ajiye kankara da ya dade bai yi aiki ba zuwa gidan abinci na musamman da muke gani a yau. Suna fatan karin mutane za su iya kara saninsu kan al'adu game da gidajen ajiye kankara na sarakuna da kuma abincin gargajiya na Beijing. Mr. Wang ya ce:
"Yanzu a nan Beijing, a wannan wuri ne kawai aka iya ganin tsantsar gidan ajiye kankara, inda ka iya kara saninka kan tarihin gidan ajiye kankara da kuma labarunsu da al'adunsu a lokacin cin abinci. A ganina, kara fahimta kan wadannan abubuwa yana gaba da cin abinci a wajen."
A cikin wannan gidan abinci na Huang Jia Bing Jiao, a kan dafa wasu kayayyakin abinci bayan da aka nazarci kalaman da mutane suka fada bayan da suka ci su a zamanin da, shi ya sa wadannan kayayyakin abinci suka sha bamban sosai da saura, kuma a wannan gidan abinci ne kawai aka iya dandana su. Matar Mr. Wang ta gaya mana cewa, sun sami sabbin abokai da yawa ta hanyar tafiyar da wannan gidan abinci. Ta ce:
"Mutane su kan kawo mana sirrinsu na dafa abinci. Su kan gabatar mana da kayan abinci mai dadi. Muna da kuku-kuku, wadanda suke da kwarewa, shi ya sa su kan samar da kayan abinci mai kyan gani kuma mai dadi."
Kayan abinci mafi shahara da ke kasancewa tamkar alamar gidan abinci na Huang Jia Bing Jiao shi ne gasasshiyar kafar tunkiya. An sa kafar tunkiya a cikin ruwan abubuwan kamshi tukuna, daga baya, a gasa ta a kan wuta, a rika mirgine kafar tunkiya, ta haka, launin gasasshiyar kafar tunkiya zai zama na ja, kuma naman na da garas-garas, kuma yana da dadi sosai ba tare da warin naman tunkiya ba. Cin irin wannan nama mai dadi tare da shan ruwan lemon tsami ko kuma jar giya ya kan sanya mutane su kasance kamar yadda sarakuna suka taba kasancewa a lokacin kece raini.
Sun Li, wata mazauniyar Beijing ce ta dade tana zaune a lungunan Hutong a wannan birnin, ta kan ci abinci a gidan abinci na Huang Jia Bing Jiao. Ta bayyana cewa, cin abincin da mazauna Beijing suka saba ci a cikin wannan gidan abinci mai nuna al'adun gargajiya na kasar Sin kuma mai kyan gani ya kan tuna mata yarantakarta. Kasancewa cikin wannan gidan abinci daya tilo ya sha bamban sosai a ganinta. Madam Sun tana mai cewar:
"Da zarar na shiga wannan gidan abinci, sai na ji mamaki kwarai da gaske bisa ganin wannan gidan ajiye kankara. Ina tsammani cewa, Sinawa suna da basira sosai. A can da mun iya samar da karya-karyar firiji kamar haka. Na ji alfahari sosai ga al'ummarmu."
Madam Wang ta kuma yi bayanin cewa, masu yawon shakatawa da yawa kamar yadda madam Sun ta yi, sun zo gidan abincinsu ne saboda gidan abincinsu ya shahara sosai, inda suka nemi kara fahimtarsu kan al'adun gargajiya na Beijing. Ta ce:
"Mutanen da suka nuna sha'awa kan al'adun gargajiya na Beijing su kan zo gidan abincinmu kullum, inda su kan gabatar da wasu lacca a wasu lokuta domin yin karin bayani kan halin da Beijing ke ciki. Sa'an nan kuma, su kan shirya tarurrukan kallon hutunan da suka dauka a gidan abincimu. A wani gefe, sun nemi more idanunsu da wadannan hotunan da suka dauka da kansu bisa fasaha, a wani daban kuma, sun yi hira kan yadda za a kiyaye wuraren gargajiya a nan Beijing bisa hakikanan halin da muke ciki a yanzu. Kazalika kuma, su kan gabatar da wasu lacca kan mutane da abubuwa da kuma labaru game da Beijing, inda duk wanda yake son ba da lacca da kuma wanda yake son sauraran lacca suka iya zuwa. Ba a bi ka'idoji ba, amma wannan yana da ban sha'awa sosai."
Masu sauraro, baya ga gidan ajiye kankara mai dogon tarihi da kayan abinci mai dadi daya tilo da aka dafa bisa sirri, a gidan abinci na Huang Jia Bing Jiao akwai sauran karin labaru game da Beijing mai dogon tarihi, inda sarakuna suka kafa fadarsu a wajen.
|