Yanzu lokacin hunturu ya yi a yawancin yankunan kasar Sin, amma shin akwai hanyar yawon shakatawa da za ta iya dumama jikin mutane da kuma ba su mamaki? A halin yanzu, shiga cikin tabkin ruwan dumi ya fi samun matukar karbuwa ko-ina a kasar Sin a matsayin hanyar nishadi. Musamman ma a arewacin kasar Sin, tare da abokai da dama, shiga cikin tabkin ruwan dumi ya iya kwantar da hankalinka da kuma kyautata tunaninka sosai amma ba tare da biyan kudi da yawa ba. Yau ma bari mu dumama jikunanmu tare!
Tabkin ruwan dumi na Huaqing da ke birnin Lintong na lardin Shaanxi a arewa maso yammacin kasar Sin shi ne daya daga cikin tabkunan ruwan dumi mafiya shahara ga mutanen da ke sha'awar shiga cikin ruwan dumi a lokacin hunturu. Tsawon kasancewar wannan tabkin ruwan dumi ya wuce shekaru dubu 6. Ruwan dumi mai tsabta da zafinsa ya kan kai misalin digiri 43 bisa ma'aunin senttigrade a duk shekara yana ta gudana a cikin wannan tabkin ruwan dumi na Huangqing da ke kasan babban dutsen Lishan cikin shekara da shekaru. Xiao Yin ya kai wa birnin Xi'an ziyara ne daga garinsa na lardin Henan, ko da yake ba shi da lokaci da yawa, amma ya yi tsimin lokaci da zummar jin dadin shiga cikin tabkin ruwan dumi na Huaqing. Wannan saurayi ya gaya mana cewa,
"Bayan da na shiga cikin tabkin ruwan dumi, na ji dadi sosai. A zamanin da, sai sarakuna ne kawai suka iya yin amfani da wannan tabkin ruwan dumi, amma yanzu sauran jama'a suna iya shiga cikin tabkin, a ganina, wannan yana da kyau."
Kamar yadda Xiao Yin ya yi, matafiya na gida da na waje kimanin miliyan 1 su kan shiga cikin tabkin ruwan dumi na Huaqing a ko wace shekara. A zahiri kuma, a shekarun baya ne kawai irin wannan sabuwar hanyar kashe kudi wato shiga cikin tabkin ruwan dumi ta fara samun amincewa daga mutane.
Baya ga wadanda suka zo daga sauran wuraren kasar Sin, mazauna Lintong ma suna sha'awar shiga cikin tabkin ruwan dumi na Huaqing.
Gu Lijun, wata mazauniyar Lintong, wacce wata malama ce da ta riga ta yi ritaya. A ko wane lokacin hunturu, ta kan shiga cikin tabkin ruwan dumi na Huaqing. Ta yaba wa ruwan dumi a nan sosai. Ta ce, "Yana kasancewa a samu abubuwan ma'adinai da yawa a cikin wannan ruwan dumi, wanda ke amfanawa fata da kuma kara saurin zirga-zirgar jini, shi ya sa na kan shiga cikin tabkin ruwan dumin sau daya a ko wane mako. Bayan da kasar Sin ta yi gyare-gyare a gida da kuma bude kofarta ga waje, tattalin arzikin kasarmu ya sami bunkasuwa, haka kuma zaman rayuwar jama'a na samun kyautatuwa, ina son in kece raini a cikin ruwan dumi."
Bisa binciken kimiyya da aka yi, an ce, ruwan dumi da ke cikin tabkin ruwan dumi na Huaqing ba ya da wani lahani, yana cike da abubuwan ma'adinai da kananan abubuwa har nau'o'i 47, shi ya sa yake amfanawa wajen kiwon lafiya, musamman ma wanka.
Zhao Wuquan, mataimakin babban darektan kamfanin yawon shakatawa na tabkin ruwan dumi na Huaqing ya yi mana karin bayanin cewa, "Kamfaninmu mun gabatar da sabbin harkokin yawon shakatawa kan al'adun shiga cikin tabkin ruwan dumi, alal misali, mun shirya bukukuwan nune-nune kan al'adun shiga cikin tabkin ruwan dumi da tarihinsa. Nan gaba mun yi shirin fadada tabkin zuwa arewa, za mu yi kokarin maido da yadda tabkin ya kasance a zamanin daular Tang, wato yau da shekaru 1200 ko fiye. Baya ga al'adu kan shiga cikin tabkin ruwan dumi, mun kuma shirya wasu harkokin nishadi da aka taba yi yau da shekaru 1200 ko fiye. Muna daukar matakai domin kyautata al'adun shiga cikin tabkin ruwan dumi a tabkin ruwan dumi na Huaqing, ta haka tabkinmu zai iya biyan bukatun mutane na da'irori daban daban."
Birnin Xianyang mai dogon tarihi da ke da nisan kilomita sama da 60 daga tabkin ruwan dumi na Huaqing, wuri ne na daban a fannin shiga cikin tabkin ruwan dumi. Wang Faxiang, wani tsoho ne da ya samu sassaucin zafin kafarsa a sakamakon shiga cikin ruwan dumi har na tsawon watanni da dama. Ya bayyana cewa,
"Shiga cikin tabkin ruwan dumi na iya kiwon lafiyar mutane da kara saurin zirga-zirgar jini da warka da amosanin kashi da amosanin gabbai da ciwon fata. Ina jin dadi sosai saboda ban samu shanyewar kafata ba a sakamakon shiga cikin ruwan dumi a nan kullum."
Mr. Wen, wani mazauni birnin Shenyang, yana son yin musayar lafiyar jiki ta hanyar shiga cikin ruwan dumi. Ya ce,
"Na ji saukin jiki kwarai bayan da na shiga cikin ruwan dumi. Ko da yake na kashe kudin Sin yuan 30 ko fiye domin shiga cikin ruwan dumi, amma a ganina, yana da amfani, kuma na iya biya. Yanzu a sakamakon karuwar kudin shiga, muna son yin musayar lafiyar jiki da kudade."
To, masu sauraro, yanzu bari mu dawo birnin Beijing, za mu ga yadda mazauna Beijing suke kasancewa a fannin shiga cikin tabkin ruwan dumi!
A nan Beijing, akwai tabkunan ruwan dumi manya da kanana da dama, a ciki kuma kila tabkin ruwan dumi da ke garin Xiao Tang Shan a gundumar Changping a arewacin Beijing ya fi nuna fifiko wajen kiwon lafiya. Tabkin ruwan dumi na Xiao Tang Shan ya sha bamban da na saura sosai saboda launin ruwan duminsa ya zama tamkar na zinariya mai haske kuma yana da tsabta sosai.
Ana iya shiga cikin ruwan dumi a cikin daki ko kuma a sarari a tabkin ruwan dumi na Xiao Tang Shan, inda a duk shekara iska mai zafi ke cika wurin, haka kuma a kan samu cunkuson mutane a nan.
Sun Zhiwei ya kan yi fama da ayyuka sosai a wani kamfanin talla. Amma in ya sami lokaci, ya kan shiga cikin tabkin ruwan dumi tare da matarsa. Ya bayyana cewa, yana jin dadin shiga cikin tabkin ruwan dumi sosai da sosai. Ya ce,
"Ruwan dumi da kuma kaunar da ke tsakanina da matata suna sa ni jin dadi sosai, har ma na kan manta da ayyuka da matsaloli, ba na lura da ni'imtattun wuraren da ke kewayena. In wani ya tambaye ni yadda ni'imtattun wuraren dake kewayen tabkin ruwan dumin ke kasancewa, to, ban iya cewa kome."
A lokacin hunturu, shiga cikin tabkin ruwan dumi wata hanya ce da ta sha bamban da wadda mutane suka saba bi domin kece raini. Zhang Ruoqi yana aiki a cikin wani kamfani mai jarin waje, yana son shiga cikin ruwan dumi, musammam ma a wajen daki tare da kankara mai laushi. Mr. Zhang ya ce,
"A yayin da aka yi babbar kankara mai laushi tare da iska mai karfi, mutane suna cikin tabkin ruwan dumi a sarari, su kan bugu saboda iskar ruwa da kankara mai laushi. Yanzu ina Alla-Alla wajen ganin an yi kankara mai lasushi, kuma a daidai wannan lokaci ne nake cikin tabkin ruwan dumi."
E, wannan gaskiya ne. Shiga cikin ruwan dumi tare da kallon kankara mai laushi, ba za a iya kwatanta shi da sauran hanyoyin kece raini ba. Mutane na iya sakin jiki a lokacin da suke kasancewa a cikin ruwan dumi. Yin hira a tsakanin abokai tare da shaye-shaye da kuma more ido da kankara mai laushi a cikin tabkin ruwan dumi a sarari ya kan sanya mutane jin dadi kwarai da gaske, mutane su kan ji sauye-sauye masu ban mamaki, wato a tsakanin sanyi da zafi.
|